← Book details Binteee Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 194 OF 218

Sashe 194

Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun daga farko Anty Madeena ta basu labari tun barowar ta gida, mahaifiyar Zaitoon motsin kirki bata iya tayi ba da yake ta riga taji komai a halin yanzu tamkar maimaici ne ake yi mata dan ko Adam ya 'dan labarta mata wani yanki daga ciki.

Yah Bukar kuwa rashin motsin sa ya samo asali ne daga tsuma da tafarfasar da zuciyar sa ke yi masa, jin dalili da kuma kalar irin rayuwan da 'kanwar sa ta faro.

Ammi ce ta bawa Zaitoona daman cigaba da yi musu bayani da kanta domin aganin ta zasu fi tabbatar wa, bata so hakan ba amma bb yadda zatayi, haka take basu labarin tana yi tana kuka, lkc zuwa lkc take kai hannu ta share hawaye.

Gurin yy tsit bb mai motsin kirki kowa na saurarenta ne, mamaki da ban al'ajab ya cika zuciyar ahalin ta kaf, na yadda tayi tunanin tafia ta barsu akan 'diyar da ita kanta bata san tushe da asalin ta ba.

Ta jure irin wannan wahalwahalun rayuwar a 'dan shekarun tan nan alahali tana da mahaifa both side ga yan uwa masu son ta.

Duk dauriyar Yah Bukar sai da ya share hawaye, haka ma mahaifin ta da dama dannewa kawai yake yi, Innani kam ai ba a cewa komai.

Abu guda da take gode Allah akai shine da bai sa 'diyar ta ta fa'da harkar banza ba kamar yadda mafiya yawan 'yan garin nasu ke hasashe cewa abinda ya fitar da ita kenan.
Ta kuma gode Allah har kamar zatayi sujudur shukur ma na yadda Allah ya tseratar da ita daga hannun 'yan iska titi..Bbn Abdul, Sultan da sauran su...ta gode Allah da ba'a samu nasarar kashe mata yarinya ba.

Tun kafin Zaitoon ta kai 'karshen labarin nata Mufee ta farka a bacci sai dai luf tayi jikin Rayyan tana rarrabe idanu, jin yadda sautin muryar Mammin ta ke fita kuma cikin kuka ya sanya Mufee 'dagowa da sauri tana lalu6en inda zata ganta da idanu.

Da ganin ta kuwa ta mi'ke tsaye ta nufi wajen ta cikin hanzari tana fa'din" Mammi..!" ta fa'da jikin ta..
Zaitoon sai ta rungume ta sosai wani sabon kuka na zuwa mata...tamkar zata maida ta cikin ta, wani sabon kaunar yarinyar ne ya shige ta a halin yanzu.

Duk kan idanu sai ya dawo kansu ita da Mufee, ga wa'danda basu sani ba tunani suke mecece alakar Zaitoona da yarinyar nan...yayin da su Ammi.da suka riga suka sani murmushi kawai tayi..tasani indai Zaitoon da Mufeeda ne fiye da hakan ma za'a gani.

Babu wanda yakai Yah Bukar, Khausar da Iyami waro idanu akansu...kar dai ace ace...kalma yake ta so ya ha'da amma ya gaza ha'dawa.

Iyami kuwa tararradi take dama, anya kuwa wannan labarin gaskia ne?...sam ma bata gama yadda da cewa wannan ita ce Zaitoonan su ba..sbd kusan komai nasu ya bambanta da tasu Zaitoonan illa kamanni...amma ita wannan kyakkyawar yarinyar fa?
Kar dai ace itace 'diyar Zaitoon wacce ta bar gida domin ta?

Lokacin da takai 'karshe a labarin kusan za'a iya cewa daga Azeema dake can tsaye dan tsakiyar labarin ta samo bayan shigowan ta sai Iyami su ka'dai ne basu share hawaye ba..hatta khausar sai da ta zubda hawayen tausayin ta.

Tace " Abban mu ".
Ya 'dago kansa ya dube ta.
Hannun ta tasa cikin nasa..ta kuma sanya na Mufeeda a tsakani tace..." Abban mu ga Aishatu na nan Allah ya raya ta, ta girma...Abba halin yanzu kana da ikon yanke hukunci tsakanin ni da ita, sbd a halin yanzu tafe take da garkuwan ta, tana da bangon da nasan zata dafa a rayuwa, tana da tsani ma'ana tana da ahalin ta kewaye da ita.. Abba ko abaya ban tafi sbd son zucia ta kawai ba Abba na tafi ne sbd tausayin ta, na amsa cewa nice na haifeta ne sbd tausayin ta kawai Abbah, nasan kona rabu da ita hannun wasu daban zata fa'da, bani da tabbacin zata samu isa ga mahaifin ta ta rayu tare ta da shi, bani da tabbacin zata samu ingantaccen rayuwa fiye da wanda zan iya bata, shiyasa na 'kwammaci ni in ri'ke ta awaje na...domin ni mahaifiyar ta ta bawa amanar ta Abba...na kwammaci insha kowacce iriyar wahala a rayuwa sbd ita domin ganin ban yi wasa da amanar da Allah ya dam'ka min ba...Abba ka yafe min...nasan abaya na 6ata maka sanadiyan Mufeeda...na kuma gode Allah daya bani damar zuwa da 'kafafuna gareku ya kuma bani ikon neman yafiyar ku da halshe na...Innani ku yafe min dan Allah..."
Ga Yayan ta koma tace" Hamma ni nasan mai laifi ce awajen ka, bani da baki ko kalmar da zan baka hakuri, bani da wata gamsashshiyar kalmar da zan furta agare ka, amma Hamma kasani tsawon rayuwa ta inajin sam ban kyauta maka ba, tsawon rayuwar da nayi bana gaban ka kowscce rana ina jin ban kyautawa halaccin ka ba Hamma...ka yafe min....nasan ka riga ka sani Hamma bani na haifi Aishatu ba...amanar ta aka bani, ga mahaifin ta nan zaune, mahaifiyar ta anan garin namu aka akashe ta, ga dangin ta nan kewaye da ita kuma suna matu'kar 'kaunar ta...ko daga yau na rabu da Aishatu bani da wani sauran buri Hamma, sbd nasan zata rayu cikin farin ciki, zata rayu cikin mahaifa da 'yan uwan ta, wa'danda na tabbatar sun ninka ni 'kaunar ta..Hamma ko daga yanzu kace kar in sake ta6a jikin Aishatu har abada bazan sake ba......"

Kai yayi saurin girgiza mata...yana mai janye hannun sa..amma ya kasa fa'din komai.

Taya ma zai ce hakan, taya take tunanin zai furta hakan? Bayan da idanun sa ya gani, yarinyar daga jikin wanda akace shine mahaifin ta ta tashi...duk yawan su awajen bata ga kowa ba sai Zaitoon, ga Zaitoon ka'dai ta tafi ta fa'da jikin ta sbd 'kauna da soyayya, ta 'dauke ta ne tamkar mahaifiyar ta, 'kauna ce ta asali a tsakanin su, 'ka'kkarfar ala'ka ce tsakanin su a fili zaka fahimci haka, shi wane da ya isa ya raba wannan ala'kar? Sam bazai iya ba...bazai ma fara ba.

Tunda Iyami taji cewa wa'dannan da suke tare sune mahaifan yarinyar Zaitoona ba 'karamin mamaki ne ya kama ta ba har ma da su sauran jama'ar.

Allah cikin ikon sa ashe 'diyar manya ke tare da Zaitoonan basu sani ba...suka wulakanta baiwar Allah.

Abu guda da Zaitoon bata fa'da musu ba shine batun auren dake kanta ahalin yanzu.
Dan dama gudun ta kenan tun farko, bata so har lokacin zuwan su nan batare da an warware mata shi, ba bata so 'yan uwan ta su san da batun barin ma Yayan ta shiyasa ta kasa fa'da ko cikin labarin.

Ammi kuwa bu'dan bakin ta bayan wani 'dan jawabi da tayi abinda ta fara furtawa kenan ta kuma nuna Rayyan matsayin mijin Zaituna ahalin yanzu...

'Kasa sosai ta 'karayi da kanta dan ko ba a fa'da mata ba tasan dole akwai wani canjin yanayi tattare da mahaifi har ma da Yayan ta Bukar, ilai kuwa hakan ne, sai dai sa6anin yadda Zaitoon tayi tunanin ita zai wa banzan kallo Ammi kawai ya kurawa idanu yana jin in bai yi hakan ba tamkar ba fahimtar ta zai yi yadda ya kamata ba.

Afuwa ba 'dan ka'dan ba ammi ta nema bayan nuna tsantsan godiyar da tayi akan ri'kon da Zaitoona da yiwa 'diyar su, ta kuma yaba mata sosai kan wahalhalun rayuwa 'kunci, 'kalubale da kuma bautar da duk tayi domin ta.. harma da mahaifan nata baki 'daya ta yaba ta kuma gode musu.

Ta kuma ce ba wai sun tilasta bane ko kuma zasu tilasta ba, amma suna masu ro'kon alfarma akan dan Allah su dubi girman Allah da manzo su dubi alkhairin da yarinyar nan ta yi musu su bar musu ita matsayin matar Rayyan, ta hakan ne ka'dai suke ganin zasu fi saka mata alkhairin da tai musu..amma sai in sun amince itama ta amince...tukunna.

Anan Yah Bukar yy caraf yace wannan ne kuma bazai ta6a faruwa ba Hajia...Yace duk cikin su bb wanda zai sake amincewa Zaituna ta yi musu nisa kwatankwacin wanda ta yi musu abaya, bayan da kunnuwan su suka ji irin tarin wahalhalun da ta sha abaya acan 'din...yace sam dole sai dai a raba wannan aure.

" Abubakar..."!
Abban su ya 'kirayi sunan sa yana mai 'ko'karin sanya idanun sa cikin nasa.
Yace " Sam ba haka na sanka da zafin rai ba...!"
" Abbah babu inda Zaitoona zata sake komawa..ka barni in fada musu gaskia Abbah...agaba na nake so tayi aure ta kuma rayu kusa dani ba can wata uwa dunia inda kowa nata ba lalle yasan inda take ba...".

Murmushi kawai Abban yayi..Baffa Liman ma cewa yyi zancen Habu gaskiya ne tunda ta dawo bb kuma inda zata sake koma wa a koya mata yahudanci...tunda 'diya dai kun gano cewa taku ce sai ku 'dauki abarku kuyi gaba, Allah ya ji'kan mahaifiyar ta ya kuma kiyaye na gaba, itama Zaitoona Allah ya bata ladan ri'kewa da wahalwahalun da tayi.

Salmerh😍
[23/01, 6:51 am] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕
*( 'Yata ce)*

*Wattpad@*
_Serlmerh-md_

🅿️ *...102*

.......Wannan maganar ya matu'kar sosa zuciyar Anty Madeena da ma Rayyan kan sa, a wannan ga6ar Ammi ce ka'dai ta iya tankawa da" Ameen Ameen"..tana murmushin da iyakar sa kan fuskar ta ne kawai...domin a fili ta fahimci wani abu guda dangane da shi wanda aka 'kira da sunan wan mahaifin Zaitoonan.

Bayan tattaunawar su tayi nisa ya iso da niyyan duba jikin 'kanin nasa sai kuma ya tarar da su suna kan maganar.
Chapter 194 · 0% Book details