← Book details Binteee Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 218

Sashe 17

Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

_" Salamu Alaikum"_ !!
Saukar tashin Sallamar Hajiyan akaro na biyu sai dai wannan karon tayi sallaman ne gami da tura kofan dakin Zaitun dake a kare ta shigo ciki wanda yayi daidai da dawowan Zaitun cikin hayyacin ta.
Hijab din ta tayi saurin lalu6owa tana sakawa take amsa sallamar Hajiyan.
"..Hajiya sannu da isowa... ke da kanki kuma Hajiya haka..?"
" Dole ce ta sani zuwan nima ba'a son raina ba".
Hajiya tayi maganar tana mai samawa kanta wajen zama bisa karamar daddumar da ta gani shinfide a dakin.
Zama Zaitun tayi itama tana gaida Hajiyan a 'darare tamkar wacce tayi wa sarki karya.
" Zauna me kyau Zaitun magana nazo muyi da ke".
Cewar Hajiya Talatu bayan ta amsa gaisuwar Zaitunan.
Gyara zama Zaitun tayi jin cewa magana zasu yi.
" Zaituna kinsan Shahid Adam ko...?"
Kallon Hajiya tayi tana me girgiza mata kai..." Shaa..hid Adam Hajiya kina nufin...Adam din ki..?"
" Shi 'din dai, shi nake nufi..dama yana zuwa gidan nan ne..?"
" erh...Hajiya yana..zuwa amma ba...sosai ba..."
Tayi maganar ne a rarrabe sbd bugun da zuciyarta da ya kara tsanan ta.
" Yana dai zuwan kuma wajen ki yake zuwan ko...?"
Shiru Zaitun tayi bata bawa Hajiyan amsa ba...sbd ta fara hasaso dalilin zuwan Hajiyan.
Bata damu da rashin amsawar ba sai ma wata tambayar da ta sake jefa wa Zaituna.
" wace iriyar ala'ka ce tsakanin ke da shi..?"
'Kasa Zaitun tayi da kanta tana mai jin wani nauyi da kunyar Hajiyan na taso mata wanda sai yau din kadai ne taji haka game da Hajiyan.
" Zaitun ki fada min gaskiya..."
Haka kawai sai ta tsinci kanta da furta" Hajiya babu komai".
Shiru ne ya ratsa dakin na 'dan wani lokaci, kowa abinda yake sa'kawa cikin zuciyar sa daban, ita Zaitun rudani ta shiga yayin da Hajiyar ke kissima abubuwa da dama sam bata ga wata dacewa tsakanin Zaitun da Adam ba, bata san me ya jashi har ya birge shi game da yarinyar ba, baza'a kira Zaitun mummuna ba kam dan kyau tana da kyanta daidai gwargwado amma ita ai a ganin ta kyan dan maciji tayi.
Sai da Hajiya ta saki huci abinka da masu dan qiba sannan ta cigaba..." kikace babu komai?"
Kai Zaitun ta daga cikin taraddadin abinda ya dace tace da Hajiyan.
" Amma me yasa ya same ni da batun yana san auren ki..? Nasan kinsan komai gaula kawai kike son maishe dani"
" Toh kiji in fada miki wani abinda baki sani ba Zaituna".
Kadan ta dago ta dubi Hajiyan ta kuma 'dauke kanta da sauri" nasan a iya matsayin shekarun ki bazaki rasa sanin waye tsohon Sanata Jibrin Adam 'Dan maliki ba ko..?"
Shiru Zaitun tayi tana tunano inda tasan sunan, 'dagowa tayi ta kalli Hajiya lokacin da ta tuno wani dan siyasa ne me irin wannan sunan..."
Kamar tasan abinda ke ran Zaitun sai cewa tayi" 'Dan Maliki da kika sani wannan 'dan siyasan shine asalin mahaifin Adam Shaheed"
Hajiya ta fadi cike da tabbatarwa.
Idanu Zaitun ta zaro cike da mamaki...yayin da Hajiya ta cigaba da fadin.
" Adam da kike gani ba sa'an auren ki bane, bar ganin sa haka nan Adam mutun ne shi mai matukar kima da daraja uwa uba kamilallan yaro ne da kowa zai yi alfaharin kasancewar sa 'da agareshi, bar ma natun wannan, ta ya ma ke da shi din 'karamar kwakwalwar ku take muku tunanin ni Talatu zan amince 'da na, yaro irin Adam ya auri mace wulakantacciya irin ki? Mace mai zaman kanta? Mace marar ilimi?
Macen da bata san kanta ba? Macen dana tabbatar ba kamilalliya bace, macen da ta bar gaban iyayen ta ta za6i tai zaman kanta..? haba baiwar Allah ki yiwa kanki adalci mana...bana raba 'dayan biyu ma korar ki iyayen ki suka yi saboda abin kunyar dakika jajibowa kanki..? kuma ni sai in zuba idanu ina ji ina gani in bar 'dana ya kwashe ki?..me ne suna na kenan?"
Shiru babu amsa tuni hawaye ya 6allewa Zaitun hakika in dai hakane ta zurma da yawa, amma me yasa sai Hajiya ta sata a gaba da wannan irin zagin cin da cin mutuncin dan kawai tana so ta rabu mata da 'dan ta...'daya bayan 'daya zagin da Hajiyan tai mata suke shiga kwakwalwar ta suke samun wuri..ji take ba'a ta6a ci mata mutunci irin hakan ba kaf din rayuwar ta.
Mufee dake zaune gefe ma tuni ta taso izuwa jikin Zaitun din ta jingina daga gefen ta tamkar tasan cin mutunci akewa uwar ta haka ta tsura idanu wa Hajiyan tana kallon ta.
" Dubi kanki fa? dube ki? dubi inda kike rayuwa?
inda ta fadi hakan tana me rarraba idanu a dakin Zaitunan...ita kam bata bukatar sai ta kalla ko Hajiyan bata fada ba tasan cewa ita din kaskantacciya ce batun yau ba..."Ko kusa Zaitun ko alama kai ko a wasan yara sam baki dace da auren 'daa na ba, kuma matukar ina raye matukar ina numfashi bazan ta6a kuskuren barin hakan ya faru ba har abada..."
" Dan haka daga yau daga yanzu..mintina ashirin ban amince ki sake karawa cikin gidan nan ba ki bar min kaya na..ki tafi duk inda zaki je, duk inda ya miki, akwai gidajen bariki da dama wadanda suka dace da zaman mace irin ki amma ba gidan Shaheed 'dina ba, gidan auren tsarkakke ne bai kuma dace da zaman mace watsatstsiya irin ki ba, ki tafi dan Allah kiyi ne sa da rayuwar yaro na.."
Numfashi Hajiya ta sauke sbd dogon maganar da tayi kuma ya kasance a zuciye take yin sa dole sai da ta sauke numfashi kafin ta cigaba.
" Na hada ki da Allah ne saboda in tabbatar miki cewa da gaske nake, in kuwa kika qi, kika bijirewa magana ta bisa son zuciyar ki da kwadayin da ke ranki wallahi Zaitun duk abinda na aikata agareki ki zargi kanki da kanki...".

Daga haka Hajiya ta mike tsaye ta kama hanyar barin dakin jakar ta rataye a dantsen hannun ta...sai kuma ta tsaya tace.." Karki manta mintina ashirin kacal na baki ki bar min gidana kashedi na na karshe da ke kenan...".

Daga haka Hajiyan bata sake waigowa ba sai jin karar kofan gida Zaitun tayi da alamu ta fice kenan.
Idanun ta ta sauke kan abincin da take shirin hada musu kafin shigowan Hajiyan sai kuma ta juyo ga Mufee data kwantar da kanta bisa kafadar Zaitun din.

Hannu takai ta shafi fuskar yarinyar cike da karfin hali tace" Mamana zaki ci abincin..? bari in sa miki.."
Tayi maganar ne tana jan jiki zuwa ga abincin duba daya idan kayi mata sai ka tausaya mata sbd yadda yanayin ta ya nuna tsantsan tashin hankalin da take ciki..da ace tana da dama da hannu zata sa aka tayi ta zabga ihu har sai numfashin ta ya kare gana daya...amma sbd Mufeeda..ita kai saboda ita kadai dole zata so cigaba da rayuwa, zata rayu domin ta ne kadai.
Duk abin da take yi kwalla bai bar sauka mata ba...hawaye ne kawai ke sauqo mata dan shidin bazata iya dakatar da shi ba...maganganun Hajiyan sun sosa ranta fiye da zaton mai karatu amma da yake tasan ta cancanci hakan sai bata ga laifin Hajiyar ba.
Zaunar da Mufee tayi ta aje mata abincin a gabanta tunda ta iya dan ci dakanta kadan kadan...duk da dai tasan ba sosai take iya ci da kan nata ba amma dai tana kyautata zaton kafin ta kammala abinda ke gaban ta Mufeedan zata ci yadda ya kamata.
Da yake ta riga ta sallaci azahar dama sallayar kenan da Hajiya ta samo shimfide ta yada zango akai.

Shi Zaitun ta fara ninkewa har a lokacin kuma hawayen ta na zuba...cikin mintina kalilan ta gama hade musu kayan sawan su cikin wata karamar Ghana must go wanda daga iya kayan sawan bata yadda ta dauki komai ba ta dai juye guntun taliyar a bakar leda saboda Mufeeda sai kuma takalman su da bai fi kala bibbiyu ba..Mufee ce ma ke da kusan kala hudu saboda Adam na yawan siya mata.

Zama tayi ta karasa bawa Mufee abincin da kanta wanda bata ma jima da fara batan ta ta nuna ta koshi sai da ta bata ruwa tasha kafin ta goge mata baki tas ta goye ta abaya tare da zum6ula Hijabi akanta.

Haka ta fito daga ita sai jakan kayan su tana sake bawa kanta kwarin gwiwa, jan kofan kawai tayi ta juya ta yiwa gidan kallon 'karshe, bata so tafiya batare da ta yi magana da maman Abdul ba, ga shi ita ba waya ce gare ta ba balle ta kira ta, a irin zaman da suka yi da Mmn Abdul be kamata suyi irin rabuwar nan ba, sai gashi bazata sun rabu a lokacin da kowannen su bai yi tsammani ba, rabuwar da bata tunanin akwai ranar sake haduwar su.

Hajja ce tayi saurin fitowa jin motsin Zaitun din, da yake duk abinda suka tattauna a kunnen ta ne, Hajja bata yadda ta zauna adaki ba tun bayan shigowan Hajiyan...sai gashi kunnuwan ta sun yi mata kyakykyawan ji abin faranta zuciya, ba karamin farin ciki taji ba da Hajiya tace Zaitun ta bar mata gidan ta..itama zata huta da alakakai daga yau.
Chapter 17 · 0% Book details