Sashe 204
Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ha'ki'ka akwai wani yanayin da sam baki bazai iya bayyana su ba.
Ko da wasa bazai iya zayyano yanayin da yake jin zuciyar sa ba, ya dai san yana jin natsuwa sosai fiye da mafiya yawan lokutan sa na baya..domin ko baccin da yayi aranar bacci ne mai cike da kwanciyar hankali da natsuwa irin wacce ya jima bai yi irin ta ba, wanda ya tabbatar hakan baya rasa nasaba da samun damar mallakan abinda yake mai matukar daraja ne a wajen sa da yayi, shi ka'dai yasan halin da yake ciki.
A yanzu ji yake kamar babu wanda ya kai sa zama cikakkken mutum kuma mai kwanciyar hankali, domin wannan karan yanayin na daban ne.
Shi Kansa daban yake Jin Kansa, kamar cikin mafarki, ji yake tamkar za'a tada shi a baccin da yake, yau wai gashi ga Zaitoon, Kuma cikin gidan sa, matsayin Mata agare sa, karkashin inuwar sa, zata rayu 'kar'kashin ikon sa ba na kowa ba, zata rayu ne bisa bin umarnin sa ba na kowa ba.
'Karfe uku ya tashi a baccin...bayaso ya tsawaita tunanin hakan yasa shi tashi ya 'dauro alwala, nafilfili yayi sannan ya zuba kirari wa mahalicci ya Kuma gode Masa bisa cika Masa wannan buri nasa..ya Kara rokon sa neman zaman lafia, kwanciyar hankali, zuri'ah masu albarka, ya roki Ubangiji ya wanzar musu da zaman lafia tsakanin su ya Kuma Sanya albarka cikin rayuwar gidan sa ya kawar da shai'dan ya basu ikon sau'ke hakkokkin junan su akan su.
Rayyan ya dade yana addu'o'i kafin ya kammala, bashi ya sake komawa bacci ba kuma har sai bayan da ya dawo daga masallaci.
Hatta iskar da ke ka'dawa yake sha'kan ta ma jin ta yake daban, ji yake tamkar wani gagarumin nawi aka sau'ke masa, shi da kansa yasan ko sakin fuska da walwalar sa ma ya bambanta da na baya, amma duk wannan yanayin baka isa tashin farko ka fahimci halin da yake ciki ba indai ba shi ne ya sanar da kai bisa radin Kansa ba.
Tun jiya bayan shigowar sa bai sake amsa wayar kowa ba duk ma wayoyin sa akashe shi da kansa ya za6i ya bawa kansa hutu yadda ya kamata.
Fawwaz yaso tsokanar sa ma a safiyar washegarin amma ga mamakin sa ya kasa samun sa Sam sam.
'Yar daria kawai yy a fili ya furta shegen kaya, zaka zo ka same ni ne.
Bashi ya tashi a baccin ba sai goma na safia...wanka yy cikin tsanaki ya shirya, wanda hakan ya 'dauke sa cikakken mintina talatin domin bai wani zafafa ba...ji yy ga66an jikin sa kansu basu zafafa masa ba dan hka sai yy komai cikin natsuwa.
Waya guda ya bu'de wacce yake tunanin ma'aikatan sa zasu iya neman sa ciki, duk da ko yanzu ma can ya nufa amma bai san ko da wani uzurin da zai iya ji kafin wanzuwar sa wajen ba.
Key ya 'dauka cikin sassanyan yanayi da kwalliyar sa ta 'kwalisa gwanin birgewa, yayi kyau cikin shigar tasa ta milk colour 'din shadda 'dinkin zamani sai tashin 'kamshi yake ya nufi hanyar fita...da isar sa babban parlon da ya linking dukkan 6angarorin gidan sai yaja ya tsaya ya kasa yin gaba.
Shin anya akwai adalci anan kuwa? Anya ya kyauta kuwa, amanar yarinya ya 'dauko gaban mahaifan ta cikin mutunci da mutuntaka aka bashi ya dace ya banzatar da al'amarin ta kamar hakan kuwa?
Waige- waige ya fara cikin kamilalliyar yanayi kamar ance masa zai ganta cikin parlon ne.
Tashin farko zuciyar sa ta bashi shawara kai tsaye...u have to go and check on that girl...kar wani abu ya samu yarinyar mutane.
Bai yi jayayya ba ya biyewa zuciyar sa kai tsaye ya nufi 6angaren da ya san take hannun sa ri'ke da makullin mota da wayar sa.
This is Mr Rayyan heading to Zaitoon's apartment as his wife...amazing!...sai yy 'dan murmushi.
Ko da iya jikin 'kofan kasa bugawa yy kawai ya tsurawa 'kofan idanu.
hannayen sa duk biyu ya zuba cikin aljihu fuskar sa bb yabo bb fallasa.
Ya kai kimanin mintina uku tsaye wajen sannan ya iya sa hannu guda ya bu'de 'kofan..while 'dayan hannun still na cikin aljihu.
Bakin sa kansa nawi yayi masa dan ko sallama kasa furtawa yayi, a hankali yake takawa cikin tsakiyar parlorn tare da 'kare masa kallo.
Ba 'karamin kyau kala da tsarin palorn nata yayi masa ba..navy blue 'din kujerun sun tafi da imanin sa.
Sai dai ba wannan ne yafi damun sa ba kamar yadda ya lura ko alamun motsin mutum babu a 6angaren, tamkar babu wani halitta mai arai cikin sa.
Ciki ya 'karasa zuwa bedroom nan ma ya tura a hankali, babu wani wadataccen haske, hakan ya sa ya 'karasa saka kafafuwan sa ciki sannan ya mayar da 'kofan a hankali ya rufe shi.
Makunnin wuta ya lalu6a ya kunna Nan haske ya gauraye 'dakin Nan take.
Sai da ya 'karewa 'dakin kallo tsab yaga kamar babu dai alamun mutum cikin sa, ga dai dadduman sallah Nan shimfida da kuma mayafi akan sa wanda dukkan alamu sun nuna anyi amfani da shine bada jimawa ba..sai da ya gama yawo da idanun sa cikin dakin sannan ya kai duban sa izuwa saman gado.
Nan ya lura da ita du'kun'kune cikin bargo har kanta.
Tsayawa yy daga wajen yake da yake tsaye batare da ya motsa ba yake hangota da kuma tunanin meyasa take bacci har wannan lokacin tunda yasan ba halin ta bane hakan sam..dole cikin biyu akwai 'daya.
A hankali ya taka izuwa bakin gadon ya sake ja ya tsaya a har lkcn bai cire hannun sa cikin aljihu ba.
Ido kawai ya tsurawa mayafin da ta rufa da shi shi kansa bai san tunanin me ya tsaya yi ba kuma.
Gani kawai yayi kamar mayafin na 'dan motsawa alamun rawan sanyi take sai ya 'dan 'kankance idanu.
Me kenan? ya tambayi kansa.
Bai san lkcn da ya zare hannun sa cikin aljihu ba, wanda da zaman sa da zarewan duk bai fi cikin en 'kalilan 'din sakanni ba.
Hannu yakai jikin mayafin bisa umarnin zuciyar sa Dan haka Nan kawai wani Abu ke fizgan sa ga son ganin fuskar ta.
Da niyyan janye duvet din ya Kai hannun sa, amma ga mamakin sa 'dumi sosai yaji mayafin yayi.
Subhanallah yace gami da hanzarin zarewa.
Wani yarr yaji tsikar jikin sa ta amsa sakamakon ganin yanayin ta da yayi.
Alama kawai ya gani cewa a galabaice take.
Bai ma san lkcn da bakin sa ya ambaci sunan ta ba.
Amma Zaitoon bata amsa ba.
akaro na biyu ya sake fa'din " Zaitoon!"
Gami da kaiwa hannu saman goshin ta.
A lkcn ne ya tabbatar da cewa tana jin jiki...domin yadda yaji zafin jikin da Kuma yadda jijiyoyin kanta ke harbawa abin har ya bashi tsoro
" Mamin Mufee...!!"
Ya sake fa'di da sanyin sauti sosai cikin tsananin tausayin ta.
A hankali ta bu'de idanu ta dube shi take ta sake mayar ta rufe su
" Me ke damun ki..ne Zaitoon..?"
Sai ta girgiza masa kai.
Yace " Na'am "
Da kyar ta bu'di baki ta furta.
" Nima ban sani ba ".
Wanda sam sautin maganar ba wani fitowa yayi sosai ba.
Bai sake ce komai ba kawai ya mi'ke ya nufi bathroom 'din da ke 'dakin.
Sai ma ya rasa toh me zai yi.
Babu komai ko towel babu a bathroom 'din kasantuwar jiya ne mamallakiyar dakin ta fara amfani da shi.
Hakan yasa ya sake dawowa cikin 'dakin.
Bazai ce yana wani cikin yanayi mai dadi ba, kamar yadda bai isa yace dai dai yake jin zuciyar sa ba...Amma duk da hakan ya na Jin kaguwar ya taimakawa Zaitoon.
Inda take ya koma bai yi wata wata ba kawai ya sa hannu ya 'dago ta zuwa jikin sa, can 6angaren sa ya wuce da ita.
Yanayin fitan numfashin ta kawai ya gama alamta masa wahalallan yanayin da take ciki.
Kan gadon sa ya kwantar da ita.
Rigar sa yayi saurin cirewa ya ajiye gefe inda ya rage Masa farar singileti kadai..ya nufi bathroom cikin hanzari...
( nace himma dai maza).
Bai da'de ba ya fito da ji'ka'k'ken towel 'karami a hannun sa.
Saman goshin ta ya 'daura shi take ta saki wani wahalallan ajiyan zucia takai hannu jikin hannun sa tana girgiza kai alamun yanayin Bai mata...ganin bashi da niyyan Bari a hankali ta bu'di Baki da dasashshiyar muryar ta tace" Yayah sanyi fa.."
" Sorry...soon zaki daina ji..kinji..."
Abinda kawai ya fadi kenan ya cigaba da saka towel 'din cike da kulawa har zuwa saman wuyan ta.
Gani yai ta koma wata kamar ba ita ba duk tayi laushi.
Ko da ya gama, Tea ya hado mata batare da ya sanya madara ba with less sugar gudun kar ta kasa sha nd yana da tabbaci Bata ci komai ba.
Da kansa ya zaunar da ita sannan ya mi'ka mata cup din yace" Sha..."!
Ba idanun ta ka'dai ba hatta fuskar ta kumbura sosai sannan ko bu'de idanun Bata iyawa da kyau....sosai ta bashi tausayi.
Kai ta girgiza da sauri.." Banjin yunwa.."!
" Meaning..?"
Ya fada Yana 'dage gira Yana kallon lips din ta data motsa.
" Sai tayi shiru, gefe ta Dan juya kanta Dan gujewa kallon sa da kallon da yake binta da shi.
Rai ya ha'de sosai yana Mai cigaba da duban ta..batare da ya janye cup din daga mika matan da yayi ba...tamkar ma bai ji me tace ba ya sake fa'din..." Ansa kisha ".
" Na 'koshi Yaya..".
Ta fa'da kamar zatayi kuka.
" Ansa kisha nace.."
Ya sake fadi da 'dan daga murya kadan alamun ransa ya fara 6aci.
Dawo da kallon ta tayi gare shi, ta lalle shi cikin idanun ganin da gaske fa Rai ya ha'de sai ta sa hannu ta ansa ta kai baki.
Sau daya ta sha ta kasa mayarwa bakin ta, hannu bibbiyu ta rike cup din kawai tana duban cikin sa tamkar mai karantar wani abin a ciki.
" Ki shanye sai kisha magani..".
Ya sake fadi yana mai daidaita zaman sa.
Hannun sa ta kalla dake rike da wasu maganin da bazata iya tantance su ba.
A hankali ta sake kaiwa bakin ta..take taji ya yun'kuro mata sai ta kasa ha'diyewa.