Sashe 64
Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sosai abin yake bawa Rayyan haushi, ya mai magana amma kuma 'karshe Sultan daina 'daukan wayar sa ma yayi kwata kwata, shine ya yanke shawarar samun Ammi suyi maganar.
Yana so ne su dakatar da Sultan daga wannan yawon banzan da yake 'daukan Marwa suke tafia da ba wata amfani gareta ba, ya dawo gida su ha'da 'karfi su kula da ma'aikatar su.
Dan shi abin yawa yake masa, yana zuwa hospital lokaci zuwa lokaci as a consultant duk da ma tuni ya ajiye wannan aikin amma sun 'ki sakin sa, dole suka ro'ki yake aiki da su as in contract abin yawa yake yi masa.
Yana ganin matukar babar sallah ta wuce Sultan bai tattaro ya dawo gida gaba 'daya ba sosai zai 6ata masa rai dole zai nuna masa asali waye waye Rayyan Sa'ad Auta dan sakarcin yayi yawa.
*****
" Zaitoon!...Zaitoon!!"
Muryar Ammi ke 'kwala 'kiran sunan Zaitun tana nufar 'dakin da suke.
Amma kasantuwar tana bathroom sai bata amsa ba.
Ammi na tura 'kofan 'dakin ita kuma tana bu'de na bathroom sai suka yi hudu ido.
Ido Zaitun ta kwalalo tana fa'di " Ahh Ammi da kanki, yanzu ma fa nake niyyan zuwa can 'din".
Tayi maganar tana 'karasowa tsakiyar 'dakin.
'Yar daria Ammi tayi tana kallon Moopy dake wasan ta da kayan wasa na yara da aka wadata ta da shi tace.." Haba bakomai, duk 'daya ai..".
" Wannan kishiyar tawa bata amsa sallama ne..?".
Ta 'karasa maganar tana mikawa Moopy hannun ta gami da zama bakin gadon Zaitun 'din at same time tana ajiye wata babbar ba'kar ledar da ta shigo da shi hannun ta.
Atampopi ne masu kyau aciki guda hudu da ku'di 20k na 'dinki kasantuwar latti da akayi saboda karatowar kwanakin sallar yasa gudun kar ta basu wahala ya sa ta ha'da da kudin wala'Allah ko zasu samu inda za'ai musu 'dinkin express, amma babu wanda yasan hakan fa sai ita ka'dai.
Moopy bata ki zuwa wajen Ammin ba dan zuwa yanzu sun saba sosai, sai dai duk sabon su ba kasafai ta ke sake jiki da Ammin ba matukar babu Zaitun a wajen.
'Dan wasa Ammi tai mata, ta fara daria wanda hakan yasa Zaitun murmusawa cike da jin da'di har 'kasan zuciyar ta take duban su.
Sai da Ammi ta gama da Moopy kafin ta dawo da kallon ta ga Zaitun tace.." Wai dai sa'ko ne wallahi shap na mance ne gashi lokaci ya kure duk da hakan dai ba wani abu tunda mantuwa ce...".
Duk da Zaitun bata san inda maganar Ammi ta dosa ba dan ta kara mata kwarin gwiwa yasa ta fa'din" Allah ma yakan yi uzuri ga ma'abocin mantuwa Ammi ba laifin ki bane ai..".
" Hakane Zaitun, nagode..".
Murmushi kawai tayi yayin da Ammi ta cigaba da magana tana kuma nuni da hannun ta" Nan ma'kwabta yamma da mu haka ina jin gida na uku ko hu'du zaki ga gidan dai da brown gate dan Allah ki mika musu, suyi hakuri dan Allah mantuwa ta same ni wlh...".
" Toh Ammi ba wani abu, kamar ma fa na gane, ba gidan da Raleeya tace min na marayun nan da suke zaune da kakar su ba..?"
Da sauri Ammi ta jinjina kai tana fa'din" Allah yai mk albarka nan 'din ne dai 'yata
".
Sosai Zaitun ta jinjina karamci irin na wannan matar dan tasan Ammi ba baya ba wajen kyautatawa, ko su da suke aiki a karkashinta sai dai suce masha Allah, sutturun da aka 'dinka musu a sallah abin ba acewa komai kuma ko sallar azumi hakan akayi musu.
Kayan Zaitun ta 'dauka" Barin je in dawo Ammi..."
Sam batayi niyyan zuwa da Moopy ba a tunanin ta zata barta da Ammi ta mi'ka sa'kon ta dawo tunda ba da'dewa zatayi ba.
Amma Moopy na ganin ta da hijab kuma tana kokarin barin 'dakin kawai ta fara kuka tana mika mata hannu.
" Ja'ira bazamu zauna ta dawo yanzun ba..?"
Kamar jira take sai ta 'kara sautin kukan ta.
" Dawo ki kar6i abarki wannn ba zama zata yi ba Zaitoon..".
Cewar Ammi tan mikewa tsaye ta bata yarinyar duk suna 'yar daria.
A hannu ta rike ta suka tafi a haka....
Sosai jikin Zaitun yayi sanyi da ganin yadda tsohuwar nan ke share 'kwalla da jin cewa Ammi ce ta aiko ta..." Allah sarki Aseeya.."
Ta ringa jero mata addu'i'o tana share 'kwalla sosai.
Nan.ta bawa Zaitun labarin cewa 'dan ta 'daya ne kuma Allah bai bata shi da wuri ba har sai da ta cire rai da samun rabo kafin ta same shi, tun kuma kafin ta haife shi mahaifin sa ya rasu ita kadai ta rain shi har girma yayi aure ya dauko ta suna zama tare dukkan su da matar sa mai kirki yaran sa uku duk mata kuma ba wasu manya bane dan babbar ce ma ke da shekaru shida, rana guda ciwon ajali ya kama shi yini guda a asbiti Allah ya kar6i ransa....
Sun shiga tashin.hankali sosai gami alhini da rashin sa, sunyi zaman shekaru biyu da matar sa kafin 'yan uwan ta suka nemi ta koma gida tayi wani auren.
Yanzu haka tana aure a Zamfara ita kuma tsohuwa ta cigaba da zama da yaran.
Kusan Ammi tafi kowa 'dauke musu bu'katun su batare da kowa ya sani ba, abincin su suttutarar su hidimar makarantar su duk Ammi ke musu.
Akwai kuma wasu 'yan.unguea da abokan.arziki da ke tallafa musu dan ko lokacin da yake raye ba wani mai karfi sosai ba ne rufin asiri ne kawai na ubangiji har ya jefo shi cikin unguwar da suke da suke.
Sosai Zaitun ta jinjinawa Ammi ta kuma 'kara bata wani babban matsayi cikin zuciyar ta saboda halin kwarai da take da shi.
Ita kanta sai da ta taya tsohuwar nan share 'kwalla, hakika rayuwa iri iri ce, duk yadda kake zaton tsananin dake cikin rayuwar ka ya kai wani matsayi idan kaji na wasu sai ka raina naka, Zaitun da batayi tunanin 6ata ko mintina biyu a gidan ba sai gashi ta sahfe sama da awa guda suna tattaunawa da tsohuwar, tace jikokin nata duk basa nan suna makaranta shiyasa gidan ya kasance shiru babu kowa.
Suna tsaka da hirar sai ga wata brown magen ta 'yar kyakykyawa da ita ta taho sa'daf- sa'daf cikin irin tafiyar su da babu tashin hankali a ciki, bata zame ko'ina ba sai jikin tsohuwar nan ta lafe ta fara goga mata kanta.
Zaitun sam bata lura da tahowar magen ba sbd yanda duk hankalin ta ya 'dauku ga labaran da tsohuwar nan ke bata.
Duk 'din su babu wanda ya lura, suna tsaka da magana Zaitun ta 'dan kalli fuskar Moopy jin yanda jikin ta ke daukan 'dumi.
Ido ta 'kwalalo waje tana furta kalmar Innalillahi...ganin yadda skin 'din yarinyar ya wani koma jajajir da wasu kananun kuraje kamar na zafi da duk bata san lokacin da hakan ya faru ba, zabura tayi tana sake duban jikin yarinyar, sai lokacin tsohuwar nan ta lura da abinda ya razana Zaitun 'din.
" 'yar nan me yasa kika 'dauko musu 'diya zuwa gidan nan? ai dama saboda sun san bana rabuwa da mage yaran Aseeyah da jikokin ta basa shigowa nan gidan...wannan 'din ma inajin mancewa akai aka barki tahowa da ita, maza kai musu 'diyar su gida akwai abinda suke shafawa zai washe...".
Cewar tsohuwar tana mi'kewa tsaye da kokarin mi'kar da Zaitun ganin ta kasa ta6uka komai.
Zaitun da duk bata fahimci kan maganar tsohuwar ba tuni ta fara ziraro 'kwalla tana jijjiga Mufeeda da jikin ta duk ya saki..." Innalillahi wa inna wa inna ilaohi raji'un...dan Allah Mamana karki mutu ki barni, Moopy, Moopy na..."
Ina yarinya kam idanun ta duk sunyi luhu luhu tamkar mai jin bacci yayin da jikin ta ke ra daukan 'dumi yana kuma 'kara yin jaa.
Lami lafia suka zo ta sani toh me ke faruwa kuma? Me ya samu Mufeedan haka?
Me ya samu yarinyar ta?
Tuni kuka ya riga yaci 'karfin ta da 'kyar tsohuwar nan ta tashe ta ta kama hanyar gida rungune da Moopy gudu- gudu sauri sauri ko kulawa da inda take takwa bata yi.
_Salmerh_ 😘
[26/9/2022, 10:19 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕
*( 'Yata ce)*
Wattpad@
Serlmerh-md
🅿️ *...40*
.......A rikice ta shigo gidan tana nufan babban part 'din dake gaban ta...bata zame ko'ina ba sai saman Ammi dan ba ai mata shamaki da ko'ina na gidan ba musamman 6angaren Ammin da ya kasance nan ne wajen aikin ta.
"...Ammi, Ammi...kalli jikin Mufeeda."
Ammi da ke zaune a parlourn saman nesa kadan da ita Rayyan me suna kan tattauna batun dadoear Sultan gida kawai suka tsinkayi muryar Zaitun da yau ko sallama bata tuna yi ba.
Ba'karamin tashi hankali Ammi yayi ba ganin tahowar Zaitun a hakan da ko ba'a fa'da ba tasan ba lafiya ba, tun kan ta 'karasu tasan cike da tashin hankali ta tunkaro ta.
Tsam Ammi tayi ta zubawa inda tasan Zaitun 'din zata 6ullo idanu tama kasa ta6uka komai jira kawai take taji meke faruwa da fatan Allah yasa ba wani abun bane babba, amma 'kasan ranta take jin kamar ba 'karamin abu ne fa zai tayar da hankalin Zaitun har haka ba.
" Ammi, dan Allah ki taimake ni Ammi dubi jikin Moopy abinda yayi, Ammi dan Allah kice kar ta mutu ta barni wallahi ina son ta..."
Abinda take cewa kenan tana zubda 'kwalla ta zube gaban Ammi.
Sai lokacin ta saki asalin kuka tana kifa kanta saman cinyoyin ta gaba 'daya nutauwar ta tafi.
Da mamaki ya 'dago ya kalle ta, take kuma ya sake kawar da kansa yana tsakin tsaki kasa kasa, haushin tsayar musu tattaunar da suke nema yafi cika shi..'karshe wayar sa ya ciro ya fara danne dannen da shi ka'dai ya san meke yake yi cikin wayar.