Sashe 171
Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Haka sauran yaran sa duk ya nemi layukan su akaro na barkatai domin kuwa tun kafin ma diran sa 'kasar yake neman su amma bai yi nasaran samun ko guda cikin su ba, so haka yanzun ma dai bai samu 'din ba...sai dai bai tsaurara bincike ko tsawaita tunani kan hakan ba, sau tari ma sai yaji tamkar 'kwakwalwar sa a cushe take ya kuma rasa dalilin hakan sam.
Kwanan da Amrah tayi cikin ba'kin ciki yasa babu kalan tunanin dabai zo mata kanta ba kafin wayewar gari.
Abubuwa da yawa ta sa'ka ta kuma kwancewa, kwata kwata bama ta iya tausan zuciyar ta sbd zafin rai, sosai take jin ranta nayi mata suya sbd bakin cikin Anty.
Washegari kuwa sallah kawai tayi ta kama hanyar 'dakin Rayyan cike da masifa da tayi niyyan sau'ke masa akan maganganun Anty Madeena da suka fi tsaye mata fiye da komai.
Ko da ta isa 'dakin na sa ko sallama bata iya tayi ba kawai ta banka 'kofa ta shiga.
Yana tsaye jikin window hannun sa 'daya cikin aljihun wandon sa jikin sa farin singileti ne ka'dai da dogon wando na bacci.
Shi kansa tun jiyan tunani yake da al'ajabin yadda abubuwan suka zo masa.
Yana jin farin ciki sosai, yana kuma jin kishi mai zafi, walwalar sa duk tayi nesa da shi, a can wani 6ari cikin ransa yake jin tasirantuwar da wutar dake cin zuciyar sa ke da shi da fansar sa, atimes idan ya tuna da Mufeeda sai yaji komai ya kwance masa shi ka'dai sai kaga ya saki murmushi, yayin da wasu lokutan tunanin butulci da cin amanar da akayi masa sai yaji 'kaguwa da son ganin ya kama shi ya hana sa sukuni.
Ko jiyan bai dawo da wuri ba sai da dare ya raba sosai kafin ya dawo gida.
Tsaye yake idanun sa 'kir a haraban gidan motsin kirki baya yi illa idanun sa dake motsawa lkc zuwa lkc.
Jin bugun 'kofa ya sa shi lumshe idanu ya bude nan take sannan ya waigo cikin hankali, sai dai tozali da idanuwan sa suka yi da Amrah yasa shi 'kan'kance shanyayyun idanun sa yana mai duban ta cike da mamakin ganin ta a wannan lkcn.
Sau da dama idan ya dubi Amra sai yaga gaba 'daya kamar ba Amran sa ba, idan ya dube ta ya kuma tuna cin amana da tayi masa sai yaga ta juye masa izuwa wata halitta can ta daban ba Amra ba, ya fara ganin hakan game da ita ne kuma tun bayan fahimtar cewa Arfan ba jinin sa bane Sultan ta haifawa shi.
Yana cikin 'dan nazarin ya tsinkayi sautin muryar ta cike da kaushi da izza mai tafe da 'kwarin gwiwar da shi kansa bai san inda ta samo shi ba.
Ko da yake da kansa ya bata dama, ya bata dama a rayuwa fiye da yadda ya dace ya bata a ganin sa, shiyasa bazai yi mamaki ba dan abin ya biyo ta kansa.
" Ka ja kunnen Antyn ka Baby ka sanar da ita, ta fita harkata, ta fita sha'anin rayuwa ta domin nafi 'karfin ta, ta daina interfering akan rayuwa ta tunda ba da uban kowa nake tsara yadda zan gudanar da rayuwa ta ba, na gaji da sa ido da bi diddigin da ake min agidan nan, for God sake me na tsare mata, me ya sa zata bi ta sakawa rayuwa ta idanu...? Ina ce kai nake aure ba ita ba da zata bi ta takurawa rayuwa ta, abin kuma har ya tashi akaina ya koma kan 'danka dana haifa....bandamu ba koma me zata ce 'amma ni dai adaina sakawa rayuwa ta idanu...na lura tun da aka yi ruwa akayi tsaki aka aura maka 'yar aikin nan kowa ma yake ganin dama na cikin gidan nan, dan hatta Ammi tsabar shishshigi da kuma son a nuna min ni ba kowa bace a wurin ta balle abinda na haifa..a gaba na take nuna ta ma mance da Arfan sai wancan 'yar mayu me kama da dodanniyar...."
Bata kai ga rufe baki ba taji sau'kan mari lafiyayye saman bakin ta, wanda ya kai mata shi da bayan hannun sa na hagu...." Kasa magana tayi sbd ra'da'di daya shige ta batare kuma da 6ata lkc ba ta kai hannu ta dafe wajen.
Idanun ta na tara ruwa tace" Baby...?"
" Don't Baby me...!"
Shima ya dakatar da ita a mugun tsawace da kuma sauri idanun sa na canza launi.
..." How dare u talk to my mother this way...?..is she ur mate..? Ohh 'dan iska kk 'dauke ni? Ko kuwa kece kk so ki nuna min cewa naki iskancin ne ya sake upgrading to another level...?"
" Baby ni fa...?"
Ta fara fa'di cikin kuka, da sauri ya dakatar da ita da fa'din" Shut up da Allah!"
Idanun sa jajazir ya cigaba da fadin" Ke har kina da wani sauran kalma, daraja ko wani abin yi cikin gidan nan ne da har zaki zo gaba na..in front of me fa Amra? kina zagar min mahaifiya, da 'yan uwa na..?"
Ya 'karashe da waro rinannun idanuwan sa akan ta yana mai nuna kansa da yatsan sa.
" Baby please...."
Ta fara magana cikin kuka amma Rayyan yaki bata cikakkiyar daman da zata tanka...tuni la66an ta sun kumbura sunyi suntum har kamannin ta ya canza...
Hannu Rayyan ya 'daga mata hakan kuwa shi ya dakatar da ita ga abinda tayi niyyan fa'di.
" Get out from my side...".
Ya buga mata tsawan da ya sa ta tunowa da old Rayyan.
Da gudu ta fice a 'dakin zuciyar ta cike da bakin ciki da tunanin wai duk menene wannan? Ta ko ina bb sauki?
Ko da ta koma 'dakin ta ma bata zauna ba, mayafi kawai ta figa tayi waje ko ta kan Arfan ma bata bi ba haka tayi waje tana risgar kuka.
Tsaki Rayyan yayi ya koma kan sofa ya zauna dabas yana me dafe kansa da yake jin na sara masa sosai, ga wani gudu da hannun daman sa ke yi masa yana jansa sakamakon 'dagawan da yy a fisge ya nuna Amrah da shi.
Bai san me yasa hannun yaki warkewa gaba ' daya har yanzun ba, ya gaji da riritawan da yake masa, gaba 'daya ya maidashi tamkar wani mara kuzari duk da 'ko'karin yawan motsa shi da yake.
Ta ko'ina abubuwa na neman cunkushe masa, ba Amra ba ba Sultan ba ba kuma lafiyar sa ba.
*****
'Bangaren Zaitoon kuwa tun tana kuka da farin cikin irin dangi da gatan da taga Mufeedan ta ke dashi har abin yazo ya fara bata tsoro, mamaki ya cika kwanyar ta, da ido kawai take bin kowa da komai, ashe ba 'karamin tauye yarinyar tayi ba, ashe ba 'karamin shiga hakkin ta tayi ba, ashe shiyasa a mafi yawan lokuta take ji can 'kasan zuciyar ta tamkar ta gaza, tamkar ta gaza bawa yarinyar kula da gata yadda ya kamata, sa6anin sauran mutane dake ganin cewa ta za'ke da yawa ne, ashe dagaske ta gaza 'din, ashe duk iya yadda zata so yarinyar da nuna mata gata bata kama 'kafan dangin ta ba balle mahaifiyar ta, har gara Rayyan ma dan shi tun wannan fitar da yayi basu sake saka shi cikin idanun su ba, amma idan ta dube su a yau ta ga yadda Mufeedan ta ke cikin 'yan uwa da dangin ta sai taji ta raina kanta gaba 'daya.
Dangi da abokan arzi'ki na kusa duk sun zo dan tuni labari ya iske su..Anty Madeena da Marwa cike da farin ciki suke 'kiran waya suna bayyanawa 'yan uwa na kusa da nesa.
Hatta can 'yan uwan Nadia an sanar da su sun kuwa yi mamaki suka kuma bayyana farin cikin su sannan su kara da bada tabbacin suna nan tafe suma dan su ganewa idanun su sam ba za'a bar su abaya ba...
'Yan uwan su 6angaren mahaifin su ma an sanar da su, haka ma su Anty Raihana da tace gobe gobe ma zata kamo hanya da Bassam har ma da maigidan ta gaba 'daya dan baza a bar kowa abaya ba.
Hatta kishiyar Anty Madeena sai da tazo ganin Mufeeda abin tamkar a shirin film ko kuma labaran tatsuniyoyi.
Albarka, addu'o'i da fatan alkhairi kuwa Zaitoon tasha shi har ta 'koshi.
Sai da Ammi ta dakatar da su kafin suka daina sanar da mutane...Mufeeda kuwa tamkar yau suka fara sanin ta, Marwa koka'dan bata san yarinyar ta bar jikin ta gani take tamkar zata sake yin nesa da ita ne ko kuma idan ta matsa 'din ta rasa ta kenan har abada.
Abubuwa da dama idan ta tuna na baya sai kawai taji daria ya kamata, ba komai tafi tunawa ba illa yayan ta Rayyan...
Duk yadda Marwa taso yiwa mijinta albishir din wannan lamari abu ya faskara domin ta kasa samun sa a awaya sam..ta kuwa san shima zai yi farin ciki sosai tunda shima ahalin gidan ne, wannan tunanin Marwa kenan.
Dole kuwa ta ha'kura amma can 'kasan zuciyar ta take jin babu da'di, ya kamata ace shi ta fara yiwa wannan albishir 'din kafin wasu daban amma bata san dalilin da yasa cikin kwanakin take yawan rasa wayar tasa ba..sannan shima baya 'kiran ta yadda ya kamata.
Yadda kowa ke ta 'ko'karin jan Mufeeda ajiki ita kuma sai suka fara bata tsoro ma, dan har gara Marwa tana zama ajikin ta dayake dama mutuniyar ta ce amma sauran kam ha'de rai take sosai tayi tamkar zata saki kuka, dayake dama can Mufeeda ba baya ba wajen 'kiyuya kuma koda ta kara girman ma ba laifi takan 'dan ta6a, abin sai ya motsa mata yanzu.
Idan ta gaji da kowa sai ta koma wajen Zaitoon ta shige jikin ta lafe tana fa'din Mammi.
Hakan na matukar karya zuciyar Zaitoon sai taji tausayin junan su ya kamata...dan tasan sun sha'ku, irin sha'kuwar da rabuwar su sai ya doki kowanne daga cikin su, kuma da alamu rabuwar ta riga ta tunkaro su ne gadan gadan a yadda ta lura.