← Book details Binteee Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 136 OF 218

Sashe 136

Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da komawar ta bata ma zauna ba ta wuce sashen Ammi wajen Marwa, anan ta shashance har lokaci yaja sosai suna ta hira da Marwa anan suka sallaci azahar ma.

Ko da Mufeeda ta dawo daga skul anan ta same su, Marwa ce tai mata wanka ta shirya ta tace fita yawo zasu yi, Zaitoon dai bata ce komai ba.

Sai da Marwa taga bata da alamun tashi ta shirya sannan tace.." Banga kina niyya ba..."

" Niyyan me ne, ni fa babu inda zani.."

Turus Marwa ta ja ta tsaya tana duban ta..." Kamar Yaya, Allah baki isa ba, kin.san inda zamu je ne..?"

" Ni dai dan Allah Marwa kuje abinku ni babu inda zani..."
Marwa har zata yi magana sai kuma ta tuna wani abu.

Murmushi tayi tana jinjina kai..." Na mance ai, kice izinin yaya kike bukata kafin ki fita...".

Sosai Zaitoon ta zaro idanu tana toshe bakin ta cike da mamaki tace..." Marwa!"
...." Yes ai na fahimta...".
" Ni yaushe nace mk haka Marwa?...wace ni ma da zan ce sai da izinin sa zan fita...".

" Kin fini sanin koma mecece ke awajen sa ai yarinya..."
Cewar Marwa tana dariya..." Yanzu dai fa'di gaskia, in tambaya mk shi ko abar shi...?"
" a a ni dai bance ba dan Allah, kawai kuje abinku..."
" Sai fa kinje, dan ya yini.a office nema da har 'daki zan raka ki ki tambaye shi...."

Zaitoon kasa fa'din komai tayi kawai ta tsaya saroro tana duban Marwa..bata ankara ba kawai taji sautin muryar sa cikin wayar dake hannun Marwa.

Ga mamakin su duk Rayyan cewa yayi suje amma banda Zaitoon.
Duk basu yi zaton zai hana ba tunda ba wani daraja ya bawa auren nasu ba...

" Toh fa sabon salo...".
Cewar Marwa bayan ta kashe 'kiran.

Bata bar Zaitoon ba ta ringa tsokanar ta har suka fita bayan sun 'dauki hotuna.

Ba 'karamin kyau Mufeeda tayi cikin shigar da Marwa tai mata ba.

Suna cikin mota ta turawa Sultan hotunan ganin yadda suka yi kyau suka fito rass da su...yayin da wasu kuma ta tura su status.

Amrah ce ta uku cikin wa'danda suka fara bude status din take wani kullutun bakin ciki ya turnuke ta.

Haka ta ringa mita tana fa'dan magana gami da kushesu wa Sultan.

So take kawau ya raba matar sa da su ta ko wani fanni amma Sultan be ce komai ba, sai dai tuno maganar da suka yi da ita kwana ki da kuma ganin hotunan su Marwan da yayi ayau ya sake haddasa masa wani mugun abu cikin ransa.

Sultan baya jira ba kuma ya tsaya 6atawa kansa lokaci kan duk wani abu da ya sa gaba.
Idan yayi niyya baya ja.da baya ba kuma ya sararawa har sai ya zartass, dan haka tun daren ranar ya 'kira waya ya fara shirya abinda yake ganin shine mafi 6illewa agare shi ya kuma fara shirin komawa gida shi da Amrah, sun huta sosai, sun kuma yi yawon dunia, kowa ya gansu tare dauka yake mata ne da mijin ta hadda 'dansu, musamman da kamar yaron yake 'kara fitowa sosai da shi.

Tun daren ya shirya tafuyar su Amrah dan ba jirgi guda yake so su koma Nja aciki ba.

So yake kowa yayi tafiyar kansa da kansa.
Washe gari sassafe jirgin su Amra ya tashi ko da suka isa kuwa Kaduna ta yada zango.

Shi kuma Sultan ya shigo da yammacin ranar sai dai babu wanda ya san da sau'kar sa kaf cikin 'yan uwan sa, har ma da matar sa.

Bayan kwana biyu...Zaitoon ta shirya Mufeeda zuwa skul ta kamo hannun ta suka fito harabar gidan sai dai babu kowa illah gate man.
Ta kuma tambaye shi yace duk drivers din an aike su ne...bata yi mamaki ba domin ba yau aka fara irin hakan ba sai dai duk yadda za'a yi tasan Ammi bata ta6a bari drivers su watse gaba 'daya in dai ba taga an mika Mufee makaranta ba, gashi yau din gab take da makara ma, ji take tamkar ta bari sai washegari taje kawai amma sai taji kuma zuciyar ta bai nutsu da hakan ba.

Cikin ranta ta yanke shawarar gara ko keke napep ne ta hau ya kaita ta sau'ke ta tunda tasan makarantar, ba komai ke bata kwarin gwiwar hakan ba face yadda take jin yarinyar ta na rairo karatu sosai yafi ya fara birge ta kadan kadan har ya shie ranta take jin dadi, ada bata so aka akai Mufeeda amma yanzu dai- dai da rana guda bata kaunar taga Mufee tayi fashin zuwa, dan haka zata kaita in yaso idan an tashi sai a 'dauko mata ita babu mamaki kafin lkcn sun dawo.

Hakan kuwa akayi, lkcn har takwas kusan da rabi na shirin yi, ai da tasan drivers din zasu fita dukkan su ma da ta ro'ki Rayyan su wuce mata yarinyar su ajiye ta lkcn fitar sa.

Sai da ta koma ciki ta 'dauko ku'di kafin ta sake fitowa,
tana isa bakin titi ta samu adaidaita sahu tamkar dama jiran isowar ta yake yace" hajia sai ina...?".

Tace" Concord dan Allah zaka ajiye mu, ka hanzarta, mun riga mun makara ma sosai..."
Tayi maganar tana shiga cikin adaidaita sahun.
yace" ai a babu wani abu, bani mintina sha biyar zaki gan mu bakin gate din makarantar.

Yana fara tafia bai yi nisa ba taga ya tsaya wani matashi ya hau gefen sa.

Mufeeda ce ta yi tari sai ta kalle ta gami da janyo ta zuwa jikin ta sosai tana mai yi mata sannu.

Bata 'dago kai daga kallon yarinyar ba ta nemi hankalin ta ta ta rasa, bata kuma san dalili ba sai bu'de idanu tayi ta ganta a wani 'daki mai duhu baki 'kirin.

Kuka ta sanya da 'karfi tana mai lalu6o Mufeeda nan ta tsinto ta yashe gefen ta tana baccin wahala itama dan Mufee har a lkcn bata san ma ina suke ba balle tasan me ke faruwa.

Duk ihun da Zaitoon take da kuka babu wanda ya kawo mata agaji, babu kuma motsin wanda taji illa 'karan wani 'ka'k'karfan sauti da ke tashi na wa'ko'kin turanci.

Sai yamma lis kafin wani mai rufaffen fuska yazo gare ta ya dur'kusa hannun sa da 'yar torchlight.

Jajayen idanun sa ya zuba mata Zaitoon kam ko ganin sa da kyau ma bata yi har a lkcn kuma Mufeeda bata farka ba.

" Kina jin yunwa...?" ya tambaye ta da wani bau'da'd'den muryar sa dake nan tamkar 'karan drum.

Kallon sa kawai ta tsaya yi tama kasa bashi amsar komai..mamakin yadda akayi ta ganta anan 'din take, me take yi anan, wa kuma ya kawo ta.

Sosai tsoro da fargaba suka cika mata zuciya amma taki bawa hakan damar bayyana a zahiri.
Bata kuma san meyasa taji tsoro da fargaban ta ya iya dannuwa mata a rai ba.

Abu 'daya kawai take tunawa a yanzu shine Dr Abdulrasheed...kamar hakan dai ne ya ta6a faruwa tsakanin ita da shi, sai dai shi ba sato ta yayi ba, ba kuma cutar da ita yayi ba, bambancin kawai shine wannan karan ba kowa take jin tana zargi ba illa Rayyan, shi ka'dai ne take jin kamar zai iya yi mata wannan abin, sai dai kuma ta kasa samo hujjar da zata rike da cewa shi dinne da dagaske, a kullum rasa gane kan Rayyan take, wani lkc he is nice wani lkcn kuma sai a hankali, amma idan ma.shi 'din nevfatan ta 'daya ne Allah yasa kar su cutar da ita ko diyar ta.

Shirun da tayi masa ne ya sashi sake maimaita tambayar sa...ya kuma 'kara da fa'din..." amsar ki zata taimaka sosai wajen ku6utar ke har ma da 'diyar ki gaba 'daya, amma hkn bazai faru ba har sai kin bamu ha'din kai 'dari bisa 'dari...."
Tambaya ta farko zan kuma maimaita mk" Shin kina jin yunwa...?"
Da kai tayi saurin amsashi alamar a a.
" Sallah fa kinaso kiyi.
'Daga kai tayi alamar "erh..."

"Gud of u..".
Ya fada gami da jinjina mata, ki bani amsoshin tambayoyin da zan mk cikin sauki cikin kuma lkc kankani indai dagaske kina so abarki kiyi ibadar ki...".

Tambaya 'daya ce zuwa biyu..." Ta farko shin menene ala'kar 'diyar ki da Sa'ad Auta's family? Me kuma yasa suke 'kaunar ta sosai fiye da jikan su Arfan da matar Rayyan ta haifa...?"

Salmerh😘
[7/12/2022, 12:14 am] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕
*( 'Yata ce)*

*Wattpad@*
_Serlmerh-md_

🅿️ *...78*

........Shiru Zaitoon tayi tama amsar da ta dace ta bashi, cikin ranta take ayyana" wannan wace iriyar tambaya ce? 'kauna kam ai Allah ke dasa ta cikin zu'kata, kuma shine ya sanya musu 'kaunar Mufeeda ba wai ita ta sa ba, me yasa hakan zai zam abinda har sai an nemi hujjar da za'a kare shi da shi, shin laifi ne dan sun so Mufeeda ko kuwa wani abin daban suke nufi da ita bata sani ba.

Shirun da tayi tana duban da tunani ba 'karamin 'kona ran sa yayi ba.

Ganin kamar bazata amsa shi ba ne dan bai ga alamun tana da niyya ba, hakan ya sa ya fisgo Mufeeda dake jikin ta, wata irin fuzga ne.da ko kadan babu 'digon imani ko tausayawa tattare da shi.

Mufeeda kuka ta sanya har tana kokarin shi'dewa, ai da sauri Zaitoon ta zabura ta koma kan gwiwoyin ta tana kuka ta fara ro'kon sa da ban baki.
" Dan Allah kayi min rai ka bar min 'diya ta, wallahi dana san amsar tambayar ka babu abinda zai hana ni sanar da kai amma ban sani ba, tamkar kana tambaya na ilimin gaibu ne fa.."
" In dai kina son cigaba da ganin ta araye toh amsamin tambayoyi na yanzun nan..."
Yayi mata magama da wata bu'da'd'diyar muryar da babu alamun wasa a ciki, sautin ta kadai ma na iya hargitsa lissafin matsoraci.

" Dan Allah kayi hkr, wallahi babu wata ala'ka tsakanin mu da su fa, kawai dai ha'duwar jini ya sa suke sonta amma na rantse maka babu komai...."
" Toh ina mahaifinta yake...?"
" Ya rasu! ya rasu tun ma kafin a haife ta...."
Ta sake bashi amsa jiki na mazari idanun ta akan Mufeeda dake hannun sa tana kuka.
Chapter 136 · 0% Book details