← Book details Binteee Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 142 OF 218

Sashe 142

Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

........" Sai yau aka ga daman zuwa duba ni...?"
Yace yana duban fuskar ta bayan ya amsa sallamar da tayi.
Zaitoon baki ta 'dan tura gaba tana mai kawar da kanta gefe.
" even once Zaitoon..? ko mafarkin ki bai raya miki cewar kizo ki duba ya nake ba? kika mance da ni baki tunanin cewa akwai wani bawan Allah da ya dace ki san halin da yake ciki ba? ya nk ya na kwana? lpy ta ko babu duk ba shine gaban ki ba yarinyar kice kawai damuwar ki ko?
Ni yadda nake ganin kk 'kaunar Mufeeda ma yana sa inji na rasa hope kwata kwata, sai inga kamar bb wani wanda zai iya sake samun gurbi cikin zuciyar ki makamanciyar ta Mufeedah...tunda gashi ina shirin mutuwa ma amma ba'a damu da ko zuwa gani na ba.."
" Ba kaine kace baka son Mufee na akashe min ita ba.."
Ta bashi amsa da dukkan gaskiyar ta da sanyin sauti.
Rayyan yace
"..akan hakan kk ta fushi dani dama..?"
Ya tambaya yana 'dan waro idanu akan ta.
Kanta ta 'dauke..cikin sanyin murya me cike da jin haushi tace" cewa fa kayi su kashe min ita, me yasa ba kace ni ba a lkcn? kasan yanda naji cikin zuciya ta ne a daka furta hakan? ji nayi tamkar kaina zai tsage gida biyu Allah kamar raina baya jiki na, da ace sun kashe min ita a wancan ranar da ban san halin da zan iya tsintan kaina ba..."
Ta 'karashe maganar hawaye na gangaro mata sosai.

Jikin sa sanyi 'kalau yayi, gaba 'daya yaji mutuwar jiki ta ziyarce shi da jin kalaman nata, domin ya fahimci da iya gaskiyar ta take maganar.

Tasowa yayi ya zago ta bayan ta ya tsaya yana duban ta sosai.
So yake ya janyo ta ya rungume amma baya so ta fassara manufar sa zuwa ga wani abu daban.

Hannun sa ya 'dago ya janyo nata da shi zuwa bakin gadon da ya taso sai da ya koma ya zauna sannan a hankali ya shigar da ita cikin jikin sa ya zagaye ta da hannuwan sa.

Jin ta cikin jikin sa ya sa ta fara 'ko'karin fita 'kwantan kanta amma ta kasa, a kunne ya ra'da mata " Shiiii...calm down please, u ar still my wife remember..?"

Bata fahimci abinda yace 'din ba sam amma haka kawai sai ta ji ranta na raya mata tamkar garga'di yai mata, a fili ta saki ajiyar zuciya tana mai cigaba da 'kara sautin kukan ta.

Tsawon mintina biyu suna a hakan tana a jikin sa yana ayyana irin wannan 'kaunar, ganin kamar bazata sarara bane ya sa da sigar rarrashi yace"...i'm sorry..ba nufi na kenan ba kinji...but nasan bazaki ta6a fahimta ta ba? amma in zaki min adalci ki kwatanta da kanki if akace ki za6a tsakanin ni da Mufeedah wa kk ganin zaki za6a..?"

Wani kallo ta 'dago tayi masa da ita kanta bata san ma'anar ta ba...
Bai damu ba ya 'dan yi guntun murmushi yana duban idanun ta da frawning nd crying face 'din ta yace" I know...na riga na sani...ni bani da wannan darajar in dai a wurin ki ne but yadda zaki ji a zuciyar ki idan za'a rabaki da Mufeedah nima hakan naji koma fiye da naki a lokacin, kuma akan kowanne daga cikin ku ba wai mutum 'daya ba, kawai nabi dacewa ne, na kuma cire son zuciya...i can't afford loosing u both sbd mabambantan matsayi da kuke da shi a wuri na, but a rayuwa akwai cancanta da halacci, sharri kansa ba'a mancewa da shi cikin sauki balle khairin da ka tabbatar domin Allah aka yisa, manufa ta rama khairan ne Zaitoon ba wai dan bana so ko kaunaf Mufeeda ba, nasan ko da na rasa ta Insha Allah watarana zaki haifa min wasu kamar ta...amma ke 'din idan na rasaki shikenan na rasa ki kenan har abada, na rasa wani 6angare ne na rayuwa ta, na kuma yiwa 'ya'ya na hasarar uwar da ta dace...ki fahimce ni ki fahimce ni...."

Kawar da kai tayi tana mai share hawayen da ke sau'ko mata, sosai ya 'daure mata kai da kalaman nasa, yayin da ta wani 6angaren ta fahimce shi ta kuma fahimci girma da darajar da take da shi a wurin sa, wanda take kyautata zaton bakomai yasa hakan ba face bautar da tayi masa har yake ikirarin khairan ya kuma so maida mata da takuicin sa ta hanyar bata damar cigaba da rayuwa a dunia, ha'kika ta ji dadin hakan domin ta fahimci shi kansa yasan ta bautu akan sa, duk da domin Allah tayi, amma kayi a yaba maka ma wata sabuwar nasarar ce.

Duk da hakan da ta tuno wacce ya za6i akashe hkn bai hana ta turo baki gaba ba, cikin shagwa6ar da bata san ta ina ta fito ba tace" ...ni dai ban ji da'di ba da kace su kashe min 'yata.."
" I also felt very bad dana bada wannan za6in amma nasan ban yi kuskure ba.."
" Ni dai bana son rasa ta..kar ka sake dan Allah..idan bakwa son ta ai ni ina 'kaunar abu na..."
" nd i also luv u..".
Yayi maganar yana 'dage gira da wani zazzafan sauti mai shiga zuciya.

Da sauri ta sunkuyar da kai tana mai kokarin barin jikin sa amma Rayyan yaki bata dama.
'Karshe zamewa tayi ta kwantar da kanta saman 'kafar sa bata sake magana ba sai ma 6oye fuska da tayi da tafukan hannun ta domin bazata iya cigaba da duban fuskar sa ba.

Murmushin mugunta Rayyan yayi, Yana duban fuskar ta a hankali yace" in tambaye ki wani abu....?"
Shiru tayi babu amsa.
Sai da ya sake maimaitawa kafin ta ce.
" Allah yasa nasan amsar...."

" Insha Allah ma kin sani idan kuma ke baki sani ba ai bb mai amsani kaf duniyan nan...."
" uhumm ina jinka..."
Sai da yaja numfashi kafin ya furta.
" Ina mahaifin Mufeeda ne...?"
" Ya rasu..."
" Waye shi toh...?"
Da sauri ta cire hannun ta dake kan fuskar ta cike da tsoro, fargaba gami da mamakin tambayar tasa...sau nawa suke so tayi ta amsa musu wannan tambayar ne?
Ta tambayi zuciyar ta.

Ganin tayi shiru ne yasa shi fadin" Ina jin ki..."
" Ai baka san shi ba..."!
Ta bashi amsa zuciyar ta na luguden gudu mai tsanani.
" Mahaifiyar ta fa...?"
Ya sake jefa mata wata tambayar.
Shiru Zaitoon tayi tana wawware idanu, daga 'dayan 6angaren, bata san duk yana kallon idanun nata ba.

Zaune tayi 'kokarin mi'kewa sai fuskar su ta kusan cin karo da juna...

Ido suka tsurawa junan su kowa na kissima abu a aran sa.
Rayyan ne ya sake magana inda a hankali ta yadda ita ka'dai dake kusa da shi zata jisa yace..." Baki bani amsar tambaya ta ba..."
" Me ma kace...?"
Ta sake tambaya tana kawar da idanun ta gami da mikewa zaune ta juya masa baya.
" Mahaifiyar Mufeeda..."

" Bata da uwar da ta wuce ni ai...".
Bayan ta ya tsurawa idanu yana mamakin 'karfin hali irin nata.

" Baki ji ba...?"
Sai ta 'dan juyo ta kalle shi, tuni ya karanci wasu 6oyayyun abubuwa tun daga sautin muryar ta har zuwa kan fuskar ta.
" What I mean is...waye ya haifi Mufeeda...?"
'Kan'kance idanu tayi sosai a 'kokarin ta na ganin ta hana hawayen ta saukowa.
Sam yau bata san meke damun Rayyan ba...wannan wasu irin tambayoyi ne haka yake damun ta akan su.
Duk yadda taso dai-daita sautin muryar ta abun yaci tura..dole da rawar murya ta amsa shi da fadin.
" Gani...nice mana, Mufeeda bata da wata mahaifiyar ai baya ga ni...."

Gira ya 'dage sama ya 'dan ja jikin sa baya.." Ohh really ...?"
Ta jinjina kai alamun tabbatarwa.

" Ni nasani..na san ba kece kika haife ta kuma ke kanki kinsani right..?"
Tayi shiru.
" Zaitoon...kalle ni.."
Rintse idanu tayi da sauri.
Taya ma zai wani ce ta kalle shi salon duk ya 'kure mata 'karyar ta ko mene? Me ma ruwan sa da 'diyar ta balle mahaifiyar ta..?"

Fahimtar da yayi cewar bazata kalle shin ba ya sanya shi cigaba da magana.
" Zaitoon..ina so a yau, kuma ayanzu ki sake fahimtar da ni...ki fa'da min duk wata gaskiyar da kika jima kina 6oyewa, rayuwa bata ta6a tafiya bisa tsarin da ke kika 'dora taki rayuwar akai..akwai kuskure babba bayan 'kalubale akwai kasada...idan kuma baki shirya fa'din komai ba ni nan shirye nake da in tunasar da ke omai, baki na bazai min ciwo ba, zuciya ta bazata 'kuntata ba kamar yadda na tabbatar bazata ta6a raunata dan na fadi abinda ke raina ba, sai dai za ta rayu cikin farin ciki, farin cikin da nake fatan ya kasance na har abada daga yanzu da zan sanar dake cewa Aishatul Mufeeda jini nace, nine mahaifin Mufeeda kamar yadda Matata ta kasance mahaifiya ta hakika awajen ta har zuwa lokacin da zan tabbatar miki da hakan a zahiri....."!

A wani firgice Zaitoon ta mike hadda ja baya tana 'kare masa kallo gami da waro idanu tana nuna sa da yatsan ta...yadda tayin ga wanda bai sani ba zai 'dauka wani abin tsoro ta gani.
Bakin ta na rawa sosai tama.kasa furta komai, tana so tayi magana amma harshen ta sai yayi mata nauyi...da 'kyar ta harha'da kalmomi 'kalilan ta iya bayyana su saman la66an ta...tace
" Kai kuma...Mufeeda ta fa kace..?"
" Yes..ni 'din dai..."
Ya fadi yana mai sake jinjina mata kansa yana kum murmushi 'kasa 'kasa.

Sosai ya karamci firgici da tsoron ta saman fuskar ta.

Wani hawaye ne ya gangaro mata shar da gudun su.
Da sauri ta juya baya tana mai 'dauke hawayen da 'dan yatsanta amma a banza kamar ana tunku'do su ne.
Da muryar kuka batare da waigo ba ta fara fa'din.
" Bana son irin wasan nan dan Allah....".
" Ke kanki shaida ce Zaitoon wasa 'daya tak nake mk a kaf 'din zama na dake...wannan ba ya cikin jerin abubuwan da zan iya wasa akan su da gasken gaske nake miki magana, da kuma iya gaskia ta..."
Chapter 142 · 0% Book details