Sashe 195
Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Bata yi jayayya da su ba tace" bakomai..tana mai 'kara neman afuwar su kan shishshigin da suka yi na 'daurawa Zaitoon aure da ba tare da amincewar su ba..."!
Wannan karan Abban Zaitoon ne ya amsa da " ai bakomai...sune ya kamata ma suyi godia..domin yadda ce ta kawo hakan, da basu yadda da ita da tarbiyar ta ba ai bazasu fara ha'da ta aure da 'dan su na cikin su ba..dan haka su ya kamata su gode acewar sa, ai shi aure garkuwa ne, aure 'karin martaba ne da kariya ga duk wata 'diya mace...shi dai a 6angaren sa bai 'kalubalanci hakan ba..sbd tun farko ai laifin su ne, da basu 'ki 'diyar su suka kasa zama da ita ba ai da hakan bai faru ba...toh ina laifin wanda ya tallafi naka, ina laifin wanda ya 'kaunaci naka a lokacin da yafi bu'katan taimako....?"
Ammi tace " hakane...duk da hakan kuwa ya zam dole su gode su nemi afuwar su, dama kuma ba wai sun zo dan su tailasta bane, sun zo ne kawai dan nuna godiya gare su baki 'daya...tace tana fatan ha'duwar su ta kasance musu alkhairi a tsakanin su, alkhairi kuma mai 'dorewa har abada, idan kuma rabuwar kenan tana fatan zumunci ya 'karfafa tsakanin su kar a yada shi, tunda Allah ya riga ya ha'da.
Ta 'kara nuna yabawa da sosai ga Zaitoon acewar ta har abada bazata gaji da gode mata ba domin kuwa tattausan zuciyar ta yasa komai ya faru..taimakon da tayi musu kuma ire- iren taimako ne da bakowa ke jure yin irin sa ba shiyasa ta bawa Zaitoon lamban yabo, dole ta jinjina mata, tayi matukar nuna jajircewa da jarumtaka a matsayin ta na yarinya mai 'karancin shekaru...tace har abada bazasu iya mancewa da ko guda cikin abubuwan da tayi musu ba, shiyasa suke fatan su 'karasa rayuwar su tare da ita amma tunda su mahaifan nata basu amince ba shikenan...su zasu koma..Allah yasa hakan shine mafi alkhairi gare su baki 'daya.
Yadda Rayyan ya 'kurawa Ammi idanu bisa wannan karkatacciyar maganar ta ta har sai ya baka daria..duba da yadda yy kicin kicin da fuska..amma ba kowa zai iya fahimtar yanayin da yake ba sai wanda ya san shi sosai, lkc guda kuma yaji yy nadamar biyo sun da yayi ma duba da yadda ko kadan Ammi bata damu da shi damuwar da zai iya shiga ba take wani magana, meyasa tun farko da ya ajiye su bai koma ba ne? yace da yasan wannan shirmen za'a yi wlh da bai biyo su ba...kawai ya barsu da Fawwaz.
'Kirr ya tsaida idanun sa akanta so ma yake su ha'de idanu amma Ammi ta'ki bashi wannan damar sam.
Cikin su babu wanda yace komai, Anty Madeena ma na son tace wani abu amma ta dake ta hana kanta tankawa.
Gefe guda wata uwar harara take bankawa Rayyan da zaka rasa gane ko ta mecece.
Zaitoon dai na nan zaune har a lkcn bata bar share hawaye ba...bata san takamammen yanayin da take ciki ba a halin yanzu illa bugun da take ji zuciyar ta nayi mata, bugu kuma da 'karfin gaske, bata kuma san dalilin hakan ba, ta dai san tana farin ciki, yau ga ta ga ahalin ta, ga ta ga mahaifi da mahaifiyar ta ga kuma 'yan uwan ta nan duk kewaye da ita amma ta rasa dalilin wannan damuwar da take ji ke sake taso mata sabuwa...da kyar ta samu ta lalu6o dalilin bai wuce na fargaban tafia da Mufeeda da take tunanin za'ayi ba ne ya sanya ta jin hakan.
Sai dai lkcn da aka tsaida magana akan su zasu wuce amma zasu bar mata Mufee na kwana biyu in yaso zuwa lokacin da za'a zo 'daukan ta idan sun yanke shawara to sai a san wani mataki ya dace a 'dauka in ma takardar sakin ne ko kuma cigaba da zaman su, za6in naga iyayen Zaitoona ne.
Baffa Liman yy karaf yace" Ba wani shawara Hajia..kawai a sakar mana 'diyar mu abinda mukafi bukata kenan a halin yanzu..."
" Toh bakomai ranka ya dade Insha Allahu za'a kawo mata takardar ta...a hakan ma mun gode bisa karamcin da aka nuna mana..Allah ya 'kara girma..."
Fawwaz abokin Rayyan shine yayi wannan maganar da alamun tabbatarwa.
Wata uwar harara Rayyan ya banka masa Fawwaz duk na lure da shi amma yayi tankar bai gansa ba.
Daria kawai yk kunshewa a cikin sa.
Da rufe bakin sa Ammi ta cigaba...amma ita dai suyi mata duk hukuncin da zasu yi mata bisa duk abubuwan da yafaru indai sunga dacewan hakan burin ta guda ne a wajen su, tace su taimaka su bar mata 'diyar ta kar su ce a a, tace kar su yi tunanin cutarwa ko kuma wani abin daban tace koda ace Zaitoona ba matsayin matar Rayyan take ba a halin yanzu ya zam mata dole ne ta kula da ita da rayuwar ta, balle ace ta cigaba da kasancewa 'karkashin inuwar gudan jinin ta tace tamkar sauran 'diyoyi na nake ji da ganin ta...bazan ta6a bari wani abin ya same ta ba nayi muku alkawari... dan Allah kuyi hakuri ku sake bani wannan damar akan Zaitoon, kar ku raba auren nan, bamu san alkhairin da Allah ya 6oye acikin sasa ba... kuma fatan itama Zaitoonan kar tace a a..domin rashin amincewar ta kan batun daidai yake da rushe duk wani ginin da suke kokarin 'dagawa a halin yanzu.
Ta fadi hakane dan tasan cewa ita kanta Zaitoon ma rigimammiyar kanta ce...ba abin mamami bane tace bata son zama da Rayyan musamman yadda ta ganta tsundum cikin ahalin ta.
Komai Ammi bata basu ba dan ma kar suce sbd Zaitoona ne ko kuma dan wani abu, duk tarin alkhairan da suka zo da shi haka suka koma da abin su.
Ita dai fatan ta su amince ne kawai sbd Allah ba dan wani abu ba....sun yi rabuwar alkhairi bb yabo bb fallasa...Rayyan ne farkon tashi ya fita ya shige mota na biyun sa Anty Madeena ce sai sauran suka fito daga baya.
Yadda yake wani ha'de rai ya sanya Fawwaz 'kyalkyacewa da daria sosai.
Yace..." Wai me yafaru ne kk wani ciccin magani..?"
Wata hararar ya 'kara banka masa amma bai ce komai ba.
" Tambayar ka fa nake...?"
Yace
" Ban sani ba.."!
Fawwaz ya cigaba
" Banga laifin ka ba dai...babu mamaki ciwon baki ne ya kamaka batare da mun sani ba...haba ni dai nace ko...tunda ba hana mutum magana akayi ba ai duk hukuncin da muka yanke dole a kar6e sa hannu bibbiyu..hadda wani ban sani ba...ina tabbatar maka da cewa zaka sani ne watarana..ba yanzu ba..sai lokacin da ka budi idanu kaga an daurawa baiwar Allahn aure da wani kafin zaka sani".
" Only if kai ne zaka sakar min da ita kenan"!
'Yar Daria Fawwaz yy yana 'daga hannuwa sama yace" Ni a suwa kuma? Kaine da kanka zaka yi bani ba"
Idanu Rayyan ya lumshe yana shafa go shin sa a hankali 'dan 'karamin nazari ya tafi, dagaske fa bai tankan ba ashe a can...toh amma har aka yi zaman aka gama ma ai bai ga hurumin magana awajen ba, mai ma zai ce toh.
Sai bayan tafiyar su Ammi..Zaitoona ta fahimci ba wai farabagan rabuwa da Mufee bane ka'dai ke damun ta tunda gata ga Mufee a halin yanzu amma kuma bata daina jin fargaba da rashin sukunin ba, ta kuma rasa inda matsalar take...wata 'kila tunanin Marwa ne...ko kuma rabuwa da su Ammi...'karshe akan abinda ta bari kenan.
Rayyan ma ko cikin motar bai ce da kowa uffan ba, duk irin tsokana da Fawwaz ke masa bai tanka shi ba...har suka isa cikin garin Maiduguri.
Ammi duk na lura da shi.
Can gidan su Ammi duk suka sau'ka, Washegari kuma suka yiwa gidan su Nadia diran mikiya.
Sun sha hirar yaushe gamo...an jajantawa juna kan abubuwa da dama sannan aka hau hirar rayuwa.
Nan suke basu labarin duk abinda ya faru.
Sun yi matu'kar mamaki suma sun kuma nuna tsantsan farin cikin su a fili...sun kuma ce ko bakomai ya zam dole su ma su bada gudunmawa.
Rayyan kam aranar ma 'kin kwana yy yabi hanya ya koma Kano abin sa ransa a matu'kar jagule.
Duk yadda Abban Zaitoon yaso janyo hankalin Bukar da Baffa Liman sam sun 'ki fahimtar sa...kuma yasan ba shi da ikon tilasta su musamman ma shi Bukar 'din sbd yafi shi iko da Zaitoona.
Dole sai dai yy amfani da kalaman kwantar da hankali dan janyo hankalin sa.
Ya nuna masa mutuntaka da karamci da ya fahimci mutanen na da shi, sannan da ace masu cutarwa ne da bazasu yadda su biyo Zaitoonan har nan 'kauyen ta ba, tunda sun riga sun samu 'diyar su a hannun su amma basu yi hakan ba.