← Book details Binteee Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 218

Sashe 26

Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Parlour ya koma yy kira wanda Zaitun sam ba fahimtar abinda yake fada take yi ba sai dai ko kadan hakan bai sa taji shakka ko tsoron kasancewar ta anan din ba.

Mahaifiyar sa ya 'kira yayi mata bayani bayani a takaice ta kuma fahimce shi dan macece mai saukin kai sam bata da matsala.
"…Ba komai Abbah..indai kaga hakan ba zai zama wata matsala ba kayi yanda ya dace kawai, Ni dama tunani na Hameeda ce kar taki amincewa.."
" erh dama zanyi magana da ita Hameedan tukunna.."
Ya fadi hakanne kuma saboda ya kwantarwa da mahifiyar tasa hankali amma ba wai dan ya damu da amincewar ita Hameedan ba.
"..Toh shikenan Ubangiji Allah ya 'kara rufa asiri..."
Da Ameen Ya amsa gami da ajiye wayar.
Tunani yayi na 'yan mintina sannan ya tashi kawai yayi waje.

Fitar sa da kusan mintina talatin kenan yanzu...Zaitun na zaune tana ta zuba ido, jira take taga ta inda shi kuma zai 6ullo da nasa lamarin amma shiru...tana so ta shiga bayi ma amma sam ta kasa tashi daga inda take zaunen.
Allah ya sota ma tana hutun sallah ne amma sosai take da bukatan rsaftace jikin ta.
Haka ta cigaba da zama ba wai dan bata san ta inda zata fara ba ko kuma bata fahimci inda bathroom din yake bane kawai dai fargabar abinda ke jiran ta agaba ne ya hanata tashin.

Shahada kawai tayi ta yunkura ta sauko cikin sa'a kuwa tana saukowa sai taga ledan kayan ta a kasan gadon wanda ta sako musu 'yan kayan su a ciki.
Hamdala ta saki cikin zuciyar ta gami da daukan ledan tana me gyara rikon Mufeeda da kyau.
Bathroom ta shiga da be wani yi mata wahalar ganewa ba, dan ta koyi wannan tun a asbiti da kuma gidan Hajjaju, duk da yake na nan din haduwar sa daban ne amma bai bata matsala ba.

Da yake taga Mufeeda Fes da ita so bata yi tunanin sake yi mata wanka ba tunda taga har sabuwar riga aka sanya mata da bata san takamamme wanda yayi hakan ba..sai dai tasan koma menene an yishi ne bisa umarnin Dr Rasheed.

Sai da ta tsaftace jikin ta ta canza Pad din da Na'eema ta koya mata amfani da shi, canza shiga tayi zuwa doguwar rigar abaya sannan suka fito..sai ma da idanun ta suka yi arba da yagaggiyar rigar ta kafin ta kare godewa mahalicci daya tseratar da ita ya kawo mata wannan mutumin, ko bakomai iya taimakon da yayi matan ba karamin tallafawa bace kuma yaci ace ta girmama shi..domin badan zuwan sa ba bata san iya abinda ze afku gareta ba, da kila ba wannan zancen ake yi ba yanzu.

Ba'a jima ba aka kawo musu abinci har 'daki wanda ta fahimci siyo shi aka yi daga wurin masu sayar da abinci, nan suka ci suka yi 'kat ba tare da fargabar komai ba.

Suna nan zaune har zuwa dare babu wanda ya sake leko su..sai dai ta kan jiyo tashin muryoyin mutane cikin gidan kuma har zuwa lokacin kunnuwan ta basu jiyo mata muryar mace ko guda ba haka kuma itama bata damu ta leka ko fita daga dakin ba.
Bata sake ganin Dr Rashed ba amma duk lkcn da ya kama na cin abinci ne kawai sai taga an kawo mata.
Tana nan har akayi, Asr, Maghrib ga Isha'i da yake jerowa a daidai wannan lokacin.
Zaitun ban da tunani babu abinda take, sosai yau din Adam ya dawo ranta, tana tuna kyautatawar da yayi mata, Adam ya nuna musu kauna irin kaunar da har ta mutu bazata iya mancewa ba, ga kuma Mmn Abdul mace me kyakykyawan zuciya, wa'dannan bayin Allahn bazata ta6a mancewa da su cikin tarihin rayuwar ta ba, sun zauna da ita sun rayu da ita ba tare da sun san wace ita ba, ba kuma.su damu da sanin hakan ba suka aminta da ita, ba tare da ta gutsira musu ko kwayar zarra cikin tarihin rayuwar ta ba.
Kwalla ta share bayan tunawa da 'dan uwan ta abin alfaharin ta wato Yah Bukar, tana da tabbaci da zai san inda take tabbas sai yazo gare ta, uwa uba mahaifiyar ta, yau kam tana jin dole ne ta bawa kanta lkcn tunawa da su, tana matukar kewar su, tana kewar ahalin ta amma akwai wani shamaki, akwai babban dalilin da bazai ta6a bari taje gare su ba a yanzun.

Ta dauki tsawon lkc tana wannan sakar zucin, hannu ta kai tana share kwallan da ke zubo mata dai dai kunnuwan da jiyo tsayuwar mota da kunnuwan ta suka yi, wanda ya kasance mintina kamar arba'in ne bayan sallar Isha taji harabar gidan, sosai taji faduwar gaba, bakomai ta tuna ba face ranar da 'yan fashi suka dira gidan Hajjaju.

Tsam ta tsaida tunanin ta gami da daidai ta zaman ta ta tsurawa kofar dakin manyan idanun ta, kallo daya zakai mata kasan cewa a tsorace take.
Sai yanzun ma tunanin ina matar gidan ya fado mata, dan tun farkawar ta bata ji motsi ko tashin muryar mace ba.

Mufeedah dake bacci kan cikin ta ta sake gyarawa kwanciya still idanun ta na ga kofan dakin.

Tsawon wasu mintina bata sake jiyo motsin komai ba, amma dai hnkln ta taji bai kwanta ba sam.

Tashi tayi rungume da yarinyar sa'daf sa'daf ta taji jikin kofan, kadan ta bude ta leka, wani karamin parpour taci karo da shi amma babu kowa a 'dakin.
Bata san dalili ba sai kawai taji tamkar ana ingiza ta ne, daf da zata wuce gaban wani 'daki dake kusa da wani corridor ta jiyo tashin muryan mace 'kasa'kasa tana kuka cike da sheshsheka.
Sake zaro idanu tayi tana kokarin tura kofar ganin a dan bude yake ta jiyo muryar Dr Rasheed kuma, hakan ne yasa ta daka ta da tunanin ba hurumin ta bane.
Duk da hakan bata ji zuciyar ta ta aminta da yanayin kukan yarinyar da tajiyo ba tana so ta tilasta wa kantan cewa iyalin ta sace dagaske amma ina, ta gaza.
Tasan kukan iri daban daban, tasan yanayin kuka kala kala sbd ta tsinci kanta cikin mabanbantan yanayi da ita kadai ta sansu ta kuma san zafin su.
Wannan kukan ya banbanta da kukan dackai tsaye zata ce normal kuka ne.
Kuka ne me tsayuwa a zuci kukan neman agaji abin a tausaya.
Bata gama tantance abinda ya kamata tayi ba ta fara jiyo maganar Dr Rasheed....
" Alhajin Allah bar rokona ka saurare ni, dokokina uku ne kacal, babu hukuma cikin aikina, idan kayi abinda aka kamamin yaro mintina biyu kacal bayan kamashin ka tabbatar sunan 'yar ka gawa, ciwon farce yaro na yy bayan karbo kudin ina tabbatar maka da cewa sunan 'yarka matacciya...idan kuma kabi dokokina kamar yadda suke zaka saurari zuwan 'yar ka kwana biyu bayan na tabbatar baka yi abinda ya sosa min zuciya wurin kar6ar kudin ba...fatan ka fahimta..?".
" Shawara mai kyau..".
" Baka da matsala da wannan".
Tattaunawar Dr kenan kan waya sai dai bata iya jiyo ko guda daga can 'daya 6angaren wayar ba.
Bata fahimci komai da maganganun ke nufi ba amma kalmar _gawa_ da kuma _matacciya_ da ji su suka matukar 'dimautata, take jikin ta ya fara kyarma, tsoro da fargaba suka cikata, juyawa tayi da niyyar barin wajen cikin rashin sa'a Dr Rasheed ya bayyana bakin 'kofar da alamu ya gama abinda ya kaishi dakin ne.
Jin karar bude kofan ne ya sata juyowa a firgice idanun su suka sarke cikin na juna...Zaitun tuni hawaye ya cika mata idanu suna gangarowa.
'Dayan hannu ta kai ta rufe bakin ta da shi dan kar sheshshekan ta ya fito at same time ta zube bisa gwiwowin ta da alamun roko.
Dr Rasheed har a lkcn kallon ta yake da mamaki, sam bai ta6a zaton zata fito daga dakin da take ba, bai ta6a zaton zata iya kawo kanta har nan ba.
Chapter 26 · 0% Book details