Sashe 37
Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shiyasa ta yanke shawarar kawai zata yi auren, batare kuma da dogon nazari ko mikawa Allah za6i ba kawai ta kafe kai da fata tace ita dai sai shi, cikar burinta kawai ne agaban ta a lkcn ba komai ba.
Ganin ta dage kamar yadda Talatu ta kafe kan dokin naki ne ya sa mijin nata da kansa sanya baki cikin lamarin, zama yayi dasu suka yi magana ta fahimta 'karshe dole yasa Hajiya Talatu amincewa da batun auren amma ba wai a son ranta ba dan baya ga halayyar sa da aka kushe haka kawai ma tana ganin cewar shi din ba sa'an auren Hafsat 'din bane sbd tazarar shekaru dake tsakanin su dan ko a lokacin shekarun sa zasu ninka na Hafsat 'din har sau biyu, bugu da kari wayewar sa ta banbanta da ta Hafsat, yafi ta wayewa da gogewar rayuwa nesa ba kusa ba, a ganin ta mace wayayya wacce tasan rayuwa sosai ita tafi dacewa da shi ba 'yar uwarta Hafsat ba, tsoro take ji kar 'yar uwarta ta cutu.
Sai dai ba laifi shima Jibrin ya nuna mata kauna ya kuma nuna bajintar sa tun da aka fara batun auren har zuwa lokacin da aka sada Hafsat da 'dakin mijin ta ko sau 'daya bai nuna wani hali da za'a zage sa da shi ba, bai kuma bar 'kofar da wani zargi zai bayyana da za'a iya tuhumar sa da shi ba, ba laifi itama Talatu sai taji hankalin ta ya 'dan kwanta da auren Hafsat 'din.
Sai dai abin mamaki Hafsat bata cika sati hudu 'kwarara a gidan sa ba ta fara fuskantar wasu 'kalubale, in da ta fara cin karo da wasu abubuwa da ta kasa fahimtar inda suka dosa, ya kan dawo gidan cike da maye ya zube mata a parlour, tana zuwa kusa dashi idan ya ganta sai yace ta bashi ruwa da zarar yasha ruwan kuma sai ya fara sheka amai daga nan bacci.
Haka zata tsaftace wajen tana yi tana kuka, washegari idan ya tashi ya gansa a wajen kuma in bata yi sa'a ba sai tasha jigba ranar da ta taki sa'a ne yake tsayawa a mari ka'dai, duk wai dan me yasa bata tashe shi ba ta barshi ya kwana parlor ko 'saman tiles.
Ita kam rasa abin cewa ma take yi sai kuka, toh me zatace dashi, da kansa yasan ba iya 'dagasa zata yi ba, sannan a wancan hali da yk ciki ko ta tashe shi ba lallai tashin zai yi ba.
Hafsat ta juri abubuwa da dama tattare da Jibrin, haka zai zauna mata a Palor ya dinga zu'kan tabar sa sai yashaki iya son ransa sannan ya bar gidan ita zata tattare sauran tana kukan takaici, bata son warin taban amma bata isa tayi 'korafi ba sai tasha jibga.
Sai yanzu ta fahimci abinda tun farko yayarta Talatu take mata ishara akan su amma zuciyar ta ta lullu6a ga cikar burin ta ta kasa gani.
Tasani bata mai da hankali wajen za6en abokin rayuwa ba, haka kuma bata dace da samun nagartacce ba, wannan dalilin ya sanya ta fara kai kukan ta ga mahalicci akan ya shirya mata shi, bataso yaran da zata haifa su taso su tarar da shi da wannan halayyar balle har su tuhume ta da rashin za6a musu uba nagari da batayi ba, dan tasan koda basu tuhume ta da tambaya ba dole cikin zuciyar su suji bb dadi.
Koda wasa bata ta6a sanar da yayarta wannan lamari ba a kullun tunanin ta shine zai canza wataran, dole zai san ba daidai yake aikatawa ba ya kuma yi nadamar komai.
Wataran idan Jibrin ya bar gida tun safe in ya ga dama bazai dawo mata ba sai tsakiyar dare, wataran ma ba ya dawowa gidan kwata- kwata, ba zai kuma 'kira ya fa'da mata uzurin sa ba gudun kar ta tashi hankalin ta ba..ba ruwan sa da wannan, idan kuma ita ta kira 'din bazai 'daga wayar ba sai yaga dama, in taci sa'a ya 'daga ma masife ta yake da cewar tana damin sa aiki ne ya rike shi...hmm wai aiki har tsakiyar dare.
Takaici baya barin ta yin bacci, in ta taki sa'a ya dawo gidan washegari ma ta kanci karo ne da abu biyu zuwa uku, inma yazo mata a buge tatul inma kuma yazo da budurwa su shige 'dakin sa har sai ta kwammaci dama bai dawo gidan ba yafi mata, haka zata 'kara kwana cikin wani zullumin tana kuka, in ta taki tsananin sa'a ne yake dawo mata normal batare da yasha komai ba, in kuwa ta nemi su tattauna zancen ya kan tsatstsare ta ko kuma a takaice ya ce aiki ne yake masa yawa shi kuma yake hanasa dawowa kan lokaci, dole bata da tacewa.
A kuma 'dan tsakankanin ne ta fahimci Jibrin yana tu'ammali da wasu 6ata gari, hk zai kawo su gidan suyi mata 'da'd'daya a palor yasa tayi ta musu hidima ko kishinta ma baya nunawa sam.
Hankalin Hafsat ba 'karamin tashi yayi ba data fahimci hakan gashi a lokacin Talatu sun tafi aikin Hajji da mijin ta.
Haka tai ta rike damuwar ta bata ta6a fa'dawa kowa ba, haka ko makwabtan ta bata bari sun fahimci komai ba duk kuwa da zumuncin dake tsakanin su.
Lokacin da Talatu suka dawo kafin nan kuwa duk Hafsat ta 'kare ta lalace sai haske ka'dai da ta 'kara, a lokacin da taje gaishe ta da barkan dawowar su a sannan ta sanar da ita bayan tambayar da Talatun tai mata na dalilin ramar ta, abin nema yake yafi karfin ta gaba 'daya tsabar 6acin rai bata ma san lokacin da ta kunce mata komai ba, duk wasu abubuwan da ta dade tana 6oyewa tsab ta sanar da ita, amma abin mamaki sai Talatu ta 'kara mata zafi, duk wasu takaicin ta na lokacin auren sai a nan ta samu ta huce su, duk bakin cikin da ta kunsa na dagewa da auren da Hafsat tayi tun a farko tsab ta zazzage su, tana yi tana kuka haka Hafsat ma na kuka, 'karshe suka rungume junan su suka cigaba da kukan a hk..amma har Hafsat ta koma bata iya ta tanka kan batun ba.
Sai daga baya da ta huce gaba 'daya ta kuma fahimci damuwar Hafsat 'din kullun gaba yake ba raguwa ba sannan ta shiga lamarin sosai gashi ma laulayi ya sako Hafsat 'din gaba gadan gadan tsoron ta kar abin yazo yai mata yawa har ya kai ga illatata, duk da yake ba 'karamin farin ciki tayi da samun cikin Hafsat din ba amma tsanar da ta yiwa Jibrin yasha gaban komai.
Bata da matsalar komai a gidan auren ta, irin nustuwa da kwanciyar hankalin da take ciki gidan mijin ta sau tari ta kanyi tunanin da ana rabawa da tabbas sai ta raba ta bawa 'yar uwar ta rabi da quartern sa, amma hakan ba me yiyuwa bane sam, abu 'daya da Allah ya hana ta cikin rayuwar auren ta shine haihuwa, kuma bata cire rai da samun sa ba shima 'din dan ita akaran kanta ma ta jima tana son ta samu ciki ban da maigidan ta da 'yan uwan sa da suka fita damuwa amma har a lokacin Allah bai basu ba, sai ga Hafsat daga yin auren ta lokaci kankani ya azurta da samun ciki bayan ko cikakkiyar nutsuwa bata samu gidan auren ba ma.
A kan zuciyar ta take jin Hafsat dan ita ka'dai ce danginta take ji a kaf fa'din rayuwa, kauna da burin ganin farin cikin Hafsat shine mura'din ta a ko wani lokaci, ace kuma yau ga wannan Hafsat 'din 'dauke da ciki a jikin ta bata jin akwai wanda zai kaita kaunar cikin nan koda kuwa mahaifin cikin ne.
Son dunia Hjy.Talatu ta 'dora wa cikin nan kamar a jikin ta yake, banda tausayin Hafsat din daya sake cika mata kirji, tana ji dole ne a wannan ga6ar tayi wani abu dole ne ta tsayawa Hafsat wajen ganin ta samu 'yan cin ta, bazata sake bari Jibrin ya cutar mata da 'yar uwa ta kyale ba, duk yadda taso 6oye kauna da farin cikin bayyanar cikin Hafsat din sbd tsanar halin Jibrin amma kasa jurewa tayi.
Manya ta ha'da da maigidan ta da yake babban mutun ne shi mai kuma dattako ta ha'da da manya daga cikin dangin mahaifan su inda ta sanar da su halin da Hafsat take ciki.
An zauna da Jibrin an yi masa fa'da an kuma nuna masa kuskuren sa ya amince tamkar gaske ya kuma basu haku'ri gaba 'daya, hatta ita Hafsat din sai da ya bata hakuri da kansa batare da wani yace ba, amma suna dawowa gida ya kama Hafsat ya jibga son ransa ya mata dukan tsiya, dukan da yasa hatta cikin jikin ta sai da ya fita duk wai sbd karar san da takai.
Hajiya Talatu ba 'karamin bakin ciki tayi da faruwar lamarin ba taci alwashin sai ta kai 'karar sa ga hukuma a hukunta sa amma maigidan ta ya hana ta, acewar sa tsakanin mata da miji ba'a shiga, ciki kuma Allah ke bada shi idan yaso zai 'kara basu wani aduk lkcn da yaga dama, batun duka ne dai sai da aka sake masa magana dan sai da Hafsat tayi sati kwance a gadon asbiti kafin ta 'dan warware..kowa baiji da'din lamarin ba.
Daga asbiti Hajiya Talatu gidan ta ta wuce da ita wasa-wasa sai da Hafsat ta shafe watanni hudu bata koma gidan ta ba, duk yadda Jibrin ya nuna damuwar sa Hajiya Talatu kallo bai ishe ta ba, karshe mijinta ne da Jibrin ya biyo ta hannun sa ya sa dole badan ta so ba ta maida Hafsat 'din 'dakin amma da 'kwakkwarar kashedi ga Jibrin ya kuma amince.
Comment
Share
Vote
Salmerh😘
[20/9/2022, 12:34 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕
*( 'Yata ce)*
Wattpad@
Serlmerh-md
🅿️ *...24*