Sashe 183
Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kwafa ya rin'ka saki yana me sar'kafe hannuwan sa.
Bayan fitar su Ammi tana murmushi tace" Ayi hakuri dai mazaje...wannan fushin hk yy yawa.."!
" Ammi kin dai ga abinda nk fa'da mk ko? wlh yarinyar nan ta gama raina ni a gidan nan...ko ba komai a sama nk da ita, sannan su'din iyalai na ne, ni ke da ikon siya ko 'kin abu idan nasan zai cutar da su ba wai itace zata rin'ka nuna min iyayi da gadara ba...".
" Ni dai nasan Zaitoon bata da raini, kuma har abada bazata ta6a raina ka ba na sani, sai dai ko in wani abin kayi mata, sannan ba wai iyayi ko gadara take yi maka akan 'diyar ka ba dan na san me kake shirin fa'di, tana yi ne kawai dan kare lafiyar 'diyar ta.."
" Ammi 'diyar ta fa kk ce..."
" Yes..har abada Mufeeda wld surely remain her daughter ko da babu ranta a duniyar...batun iyalai kuma a side Pls...kasan akwai wani dogon tsauni da baka haura ba a gaban ka ko?
Akwai wani matakin da dole sai mun haura shi, auren ka da yarinyar nan 'kaddararren abu ne da ya riga ya faru, kuma ya faru ne a dai dai ga6ar da baki 'dayan mu bamu zaci hakan ba, kuma bamu da daman hana sa sbd a lkcn yiwuwar sa muka fi bu'kata fiye da sa6anin hk, hatta ita dana tabbatar har ayanzun ba wai ta sanya shi akan ta bane balle ya dame ta bata da ikon hana kanta a lokacin.. nasani, sbd tausayi da kuma 'kaunar ta da son kyautata mana, ina kuma da ya'kini har ayanzu babu son auren a 6angaren ta, so dan Allah ka daina takura ta, ka daina 'kunatata mata sbd hkn na iya haifar da tsana mafi muni..kaucewa hakan kuwa sai an bi komai a tsanake kuma bisa tsari, ni kaina bazan so a takura ta ba gudun shiga hakkin ta, domin mun tauye ta abaya, tsawon rayuwar ta sadaukar da shi tayi agare mu, kayi tunani akai Rayyan, tun ha'duwar ta Mufeeda zuwa yau din nan menene guda daka tana yin sa sbd kawai jin da'din ta?
Babu shi.
dan haka abari har sai mun tabbatar ta amince mun kuma samo yaddar iyayen ta akan auren kafin muyi tutiya da shi, wanda Insha Allah ina kyautata zaton kwanan nan zamu je gare su da yaddar Allah, kuma idan basu amince mata zama damu ko kuma batun auren ba Rayyan dole ne mu bar mu su 'diyar su, haka itama idan bata amince da sake zama da mu ba dole ne mu barta tare da iyayen ta ma'ana zaka sawwa'ke mata ta zauna tare da mahaifan ta, yarinyar nan tayi mana 'ko'kari sosai, ta tauye kanta da iyayen ta sbd 'diyar ka, yarinyar da bata ta6a sanin wace ita ko tabbaci akan asalin ta ba, ta tauye farin cikin ta ta sadaukar da duk lokuta mafi muhimmanci gare ta sbd Mufeeda, ta bautu iya bautuwa sbd kai kanka Rayyan...a lckn da kafi bu'katar taimakon wani makusanci naka, a lkcn da duk ma'kiyan ka zasu fi saurin samun kusanci da galaba akanka sbd baka san inda hankalin ka yake b amma ta kula da kai tsakanin ta Allah...sau da dama idan na zauna Rayyan rasa me zan yiwa yarinyar nan nake dan nuna mata godia da yabawa bisa abubuwan da tayi mana, kaga kuwa bazan so asake ce sbd son zuciyar mu mu takura ta akan abinda bata da ra'ayi ba har abada, tamkar 'diyata ta ciki na nake ji d ganin ta, bazan so bakin ciki ko damuwar ta ba kamar yadda bana 'kaunar ganin ta su Marwa haka har abada bana fatan ganin 'kuncin yarinyar nan....dan haka kayi hakuri da komai har zuwa lkcn da zamu ga abinda Allah zai yi..a halin yanzu wannan aure da shi da babu kusan duk 'daya ne...kaima ka kalle shi a haka nan kawai, inda hali ma hatta ita Mufeeda a bar mata abarta tare da ita tukunna....".
Jikin sa yy sanyi sosai..kuma yasan gaskiya Ammi ta fa'di, but still cikin maganganun akwai wa'danda suka ba haushi da kuma mamaki.
Wannnan maganar ta Ammi yasa yama kasa fa'din komai.
Shiru kawai yayi ya koma ya jingina bayan sa da jikin kujera yana duban Ammin da lumsassun idanun sa..daga 'karshe ya lumshe su gaba 'daya yana murza goshin sa.
Ta wani fanni yasan gaskia ta fa'da, domin da kansa ma yasan yarinyar tayi 'ko'karin da takai ayaba mata da lambar yabo mafi daraja, amma bai san meyasa yake ji can 'kasan zuciyar sa tamkar maganar Ammin bai samu muhallin kirki a ransa ba.
Ammin ce still bayan shu'dewar wasu 'yan da'ki'kai ta cigaba da fadin" Sannan 'yar uwar ka Marwa tazo min da wani batu ko ince neman alfarma na kuma yarje mata...".
Ta 'karashe maganar da 'dagowa ta dube shi sosai dan ganin yanayin sa.
Ko dan yatsan sa bai motsa ba balle wani sassa na jikin sa hatta idanun sa na nan a lumshe bai bu'de ba ya dai dafe kansa da hannun da yake murza goshin da shi.
Cigaba da magana Ammi tayi inda tace" Marwa ta ro'ke ni akan tana so dan Allah abarta taje taga Sultan ko da sau 'daya ne tak...".
Da sauri ya bu'de idanun sa ya sau'ke su akan Ammi inda yake binta da duban mamaki.
Tace " Yes na kuma amince mata..sbd wasu dalilai..."
" Ammi Sultan kuma?...bacin bb auren me zata je tayi a wurin sa...?"
" Rayyan kar ka manta fa Sultan shima 'dana ne, kuma har abada ahakan yake ko bayan bb ni, sannan miji yake ga Marwa miji kuma mafi soyuwa a zuciyar ta, kayi tunani wata nawa da rabuwar su? Wata nawa bata sashi a idanu ba? A lkcn da ya iso ya kamata ta ganshi a lkcn ta cikaro da shi cikin mummunan yanayin da har sai da yasa ta fice hayyacin ta, baka tunanin rashin sa wani irin gagarumin illah zai iya jawo mata indai har aka cigaba ahakan..ka barta taje, ko ba komai ma ai Sultan tamkar wanta ne kuma hannun ka bai ta6a ru6ewa ka yanke ka yarda...".
Idanun ya sake lumshewa yana sakin huci mai zafi daga bakin sa.
Bai ce komai ba kawai ya mi'ke tsaye gaban rigar sa yake gyarawa fuskar sa tamkar bai ta6a daria ba sam, dan yau maganganun Ammin duk babu wanda ya yi masa da'di har a ransa.
Ganin yana niyyar fita batare da ya bata cikakkiyar amsa ba yasa tace" Ina magana bakace komai ba...zuwa yaushe zaku je..?
Gira ya 'dage ya 'dan waigo" Ammi dani ne..?"
" Yes...haka na tsara! duk lkcn da ka shirya sai ka kaita Zaitoon sai ta rakata.."
"Hmm " kawai yace ya sa kai ya fita.
Salmerh😘
[30/8/2023, 9:44 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕
*( 'Yata ce)*
*Wattpad@*
_Serlmerh-md_
🅿️ *...99*
.......Tunda Amra taji batun kotun nan hankalin ta ya kasa kwanciya, gaba 'daya ta nemi natsuwar ta ta rasa...tsoro da fargabar ta a kullum 'kara yawaita yake, kusan kullum da shi take kwana ta kuma tashi da shi...tsoron tonuwar sirrin ta da ta riga tayi amanna da cewa rufe ruf yake.....
Dama tunda taji Anty Madeena ta ta6a fara yin maganar ta fara jin fargaba dan ta fahimci sirrin nata ya fara bayyana amma bayan haka bata kuma jin komai game da hakan ba, kwatsam sai kuma ga batun kotu.
Ita kanta tasan Sultan mai laifi ne, amma shakkan da take ji a halin yanzu ta tabbata ko shi Sultan din bai kaita shiga firgici ba.
Tsoro take ji sosai, ba na komai ba kuwa sai na ratsowar sunan ta ko yaron ta Arfan cikin kotu gaban alkali, gaban 'dimbin jama'ar da ita kanta bata san iyakar su..kuma a har yanzun babu wani makami guda da ta rike da tke tunanin zai iya fidda ta cikin zargi domin bata kawo tonuwar sirrin ta nan kusa ba.
Sai yanzu ma take ganin wautar ta, gaba daya ta rainawa kanta da wayon ta a halin yanzu...wannan sanarwa da Ammi ta fito tayi sai take ji tamkar dan ita kawai aka yishi, domin a tara jama'ah a kuma bayyana sirrin ta gare su.
Innalillahi kawai take fada.
Baki 'daya wa'danda ke tare da Amra sai da suka fahimci sauyin yanayi da tsantsan damuwa da ta shiga.
Tsoron makomar ta take a wajaje da dama..ba ga iyaye ba, ba ga al'umma ba, ba ga kotun ba, ba ga shi kanshi uwa uba Rayyan ba.
Bayan yanke Ameera, layin Marwa tayi ta nema bata samu ba sbd wayar da ta sake 'din na 'dan bata matsala hakan yasa ba ko da yaushe ake samun ta ba..uwa uba yanayin da itama take ciki.
Gidan Ammi Ameera ta fara zuwa kuma tun asali dama ita tana da 'dabi'ar fara zuwa sashen Ammi gaida ta kafin isa 6angaren Amra..tun ma lokacin Amra na gidan haka take.
Ko yanzun ma kamar yadda ta saba haka tayi.
Ammi na jin da'din wannan halayya Ameeran sosai, ta kuma ji dadin zuwan ta na yau 'din bisa na ko yaushe.
Dan ko bb komai tana so taji motsin su Amra amma Rayyan ya hana kowa zuwa ko tuntu6ar su acewar sa ai da kanta ta tafi so shi bb ruwan sa.
Anan ne Ameera ke sanin cikakken bayanin ai Amra na gida sun je hutu tuntuni inda Ammi ta sakaya maganar sbd fahimtar cewa Ameeran bata san komai ba.
Bata sha wani wahalar zuwa gidan mahaifin Amran ba da yake ta sanshi, sunsha hira da Amra sosai anan take bata labarin duk abinda ta sani game da zaman kotun.
Sai a lkcn hankalin Amra ya 'dan kwanta bayan fahimtar ai bb sunan ta a zaman kotun har akayi aka gama.
Dan tana da tabbaci da ace akwai sunan ta da Ameera bazata 6oye mata komai ba.