Sashe 20
Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sake nufan kan titin tayi da niyyan komawa can 6angaren da ta taso cikin rashin sa'a sai mota tayi ciki da ita...inda Allah ya takaita ma aka yi saurin take birki motar bata wani bige ta sosai ba kawai ta fa'di gaban motar a hankali ta sulale 'kasa sumammiya.
Cikin sauri mai jan motar ta fito ashe ma mace ce wanda yayi daidai da sakin kukan da Mufee tayi saboda buguwar da kanta yayi bayan fa'duwan Zaitun.
Nan take wurin ya hargitse da mutane aka kewaye Zaitun tamkar dama jiran faruwar lamarin ake.
Kwance Mufeeda akayi da ke faman kuka tana fadin...Mam..mi..Mammi" da irin nata harshen.
Wani mutun ne da shima yake kokarin wucewa lamarin ya afku a gaban sa, shine yayi saurin tambayar ko akwai wani nata ko wanda ya santa a kusa.
Babu wanda ya bada cikakkiyar amsa game da Zaitun din dan dagaske bata san kowa ba kamar yadda suma basu san ta ba, ba ta saba da kowa a wurin ba kasancewar ta bakuwa sabon zuwa kuma mai sake jiki sosai da mutane ba.
Haka aka tattara ta da ita da kayan ta Mufee dake ta faman kuka akai asbiti da su.
Emergency aka shiga da ita inda likitoci suka tsaya sosai akanta dan da alama Hajiyan da ta kade ta sananna ce ba karamar mace bace ba, bayan dogon bincike ne likitocin suka gano ba wani mummunan abu bane ya same ta, amma an bari zuwa lokacin da zata farka tayi musu bayani da kanta zai fi.
Zuwa karfe hudu na yamma ta farka cikin sa'a bata jin komai illa kanta da yai mata nauyi.
Ko data juya gefen ta sai taga Mufeeda kwance bisa wani single gadon dake dakin itama din baccin ta takeyi cikin kwanciyar hankali.
Hamdala Zaitun tayi ganin babu abinda ya samu yarinyar ta.
_Dr Rasheed_ shine likitan da alhakin kula da ita yake hannun sa, ko da yazo ya duba ta bayan yai mata 'yan tambayoyi ya tabbatar ba wata matsala bai sake ce da ita komai ba sai juyawa da yayi day niyyar barin 'dakin.
" Likita..?"
Zaitun ta kirayi sunan shi wanda hakan ne ya dakatar da shi daga fitar da yayi niyyan yi.
Waigawa tayi ta dubi Mufeeda gami da komarcda idanun ta kansa kallon...fahimtar abinda take nufi da yayi ya sanya shi fadin" ba abinda ya same ta.."
" Alhamdulillah..".
Zaitun ta furta a fili gami da lumshe idanun jin dadi, wani natsuwa taji ya saukar mata sai yanzun taji hankalin ta ya kwanta sosai fiye ma da 'dazu.
Wasa- wasa taga har dare ba'a basu izinin tafiya ba gashi kuma ita takure take kasantuwar bata yi wasu salloli da suka hau kanta ba..gashi babu wanda ya sake bi ta kansu har sai bayan maghrib kafin taga wata mata kyakykyawa me girman jiki ga gayu wacce da ganin ta kasan Naira sun zauna dai dai gwargwardo.
Ita ta fara shigowa bayan ta kuwa wata budurwa ce da zata girmewa Zaitun da kusan shekaru hudu ko biyar sai dai kana ganin yarinyar kasan tarbiya bata samu muhalli anan ba sai taunan chewing gum take tamkar ba sansanin masu karancin lafiya take ba.
" Hajjaju dama akan wannan abin kika tashi hankalin ki har haka..?"
Tayi maganar cike da rainin hankali tana jifan Zaitun da kallon kaskanci.
" Ki min shiru Shaheeda bana san irin haka fa".
Matar nan da aka kira da Hajjaju ta fadi tana mai karasawa gaban Zaitun dake kwance tana kallon ikon Allah.
Wacce aka kira da Shaheeda kam baki ta kyabe gami da ajiya ledan da dake hannun ta.
" Sannu baiwar Allah.."
Cewan babban matar da kulawa.
" Da kai Zaitun ta amsa ta tana mai kare mata kallo.
" Ya jikin naki ?"
" Alhamdulillah da sauqi sosai...".
Zaituna ta fadi tana mai kokari tashi ta zauna.
" Masha Allahu, zuwa safiya ma insha Allahu inajin za'a baki sallama tunda jikin ba wata matsala".
Shiru ya 'dan biyo baya sai karan taunar chewing gum din Shaheeda kadai da ya cika dakin.
Can Hajiyar ta nisa tamkar ta tuna wani abu ganin yadda Zaitun ke yawo da idanun ta kansu..." kinga baiwar Allah saki jikin ki kinji, nasan baki san mu ba amma nice wadda na kade ki da mota wanda hakan ya faru ne bisa rikicewa da nayi ganin bazata na ganki gabana...ki gafarce ni..."
" Bakomai Hajiya haka dama Allah ya tsara.."
Cewan Zaitun cikin sanyin murya mai cike da rauni...dan duk sunyi laushi daga ita har Mufeeda kuma ta tabbatar duk yunwa ce ke cin cikin nasu.
" Wannan fa...?"
Hajiyar ta tambaya tana duban Mufee dake gaban Zaitun tayi luf cikin.jikin ta.
Itama maida idanun ta tayi kan Mufeen haka ma Shaheeda dake can gefe tana jifan su da kallon kaskanci...
" 'YATA CE.."
Cewar Zaitun cike da tabbatar wa.
" Masha Allahu...kyakykyawa abinta.."
Cewar Hajiyan tana sakin murmushi.
" Hajiya ina so nayi sallah dan Allah.."
"Ahhh..ai ga bayi nan, ki shiga ki yo alwala kiyi sallah sai kuci abinci...Shaheeda miko abincin nan.."
Ta karashe maganar da waigowa tana duban inda Shaheedar ke tsaye.
Wani farin ciki ne ya lullu6e zuciyar Zaitun dama duk tunanin ta inda zata sama musu abinda zasu ci ne musamman ma Mufee da tafi tausayawa..gashi kuma kaf dakin bata ga alamun jakam kayan ta suke ba balle ta yi tunanin amfani da 'yan kudin ta wajen sama musu abincin.
" Hajiya angode.."
Shine kadai abinda Zaitun ta fa'di.
Kafin Hajiya tace wani abu Shaheeda cikin tata kalar shagwa6a tayi saurin fa'din.." Hajjaju dan Allah ki tashi mu wuce..kin manta akwai inda zamu biya ne...?"
Murmushi kawai Hajjajun tayi sannan ta mike..." Bari mu wuce zuwa safiya Insha Allahu zan dawo kinji, Allah ya kara afuwa.."
Daga haka suka fice batare da sun kara ko waiwayan su ba.
Zaitun kam dama ba sabo tayi da kashe jikin ta ba dan suna fita ta mike bata jin komai a jikin ta illah kanta da ke sara mata sosai bayin ta leka sai taga ba mai wahalar amfani bane shiga tayi tayo alwala ta dawo dakin, sai da ta jero sallolin ta kaf sannan ta mike, ledan nan da suka ce abinci ta bude sai taga abinci ne a takeaway har guda uku, ba tare da 6ata lokaci ba suka far wa abincin nan tana ci tana bawa yarinyar har suka jisu full kafin suka sarara bayan sun dage takeaway biyu daya ya rage suka sha ruwan roba da ta gani a ledan shima guda biyu.
Take taji natsuwa ta shige ta jin ta dam Mufee ma a koshe, rungumo Mufee tayi abu daya ne yanzu matsalar ta shine sanyi da suke ji, amma bai wani 'daga mata hankali sosai ba, dan ta jima da lura da Mufeeda duk irin sanyin da ake da zarar ta shigar da ita jikin ta ta lullu6a mata Hijabi shikenan bata sake motsin kirki, dan haka wannan damuwar sanyi bata wani dame ta sosai dan tana da yadda zatayi da Mufee.
Haka kawai sai take jin tamkar su tabbata a haka a dakin asbitin...amma tasan hakan ba me yiyuwa bane.
Washe gari kuwa kamar yadda Hajiyan ta fadi aka basu sallama bayan Dr Rasheed ya sake duba ta haka sun 'dunguma motar Hajiyan batare da tasan inda za'a kai su ba, kuma bata ga fuska daga wurin kowa da zata iya tambaya ba dan yau din Hajiyar ma a 'dime take.
Gida ne tsararre daya sha kyau har ya gaji, Zaitun tun da take bata shiga gida irin wannan ba, kenan yau din shine karonta farko data'' shiga irin hakan, wanda kafin yau din sai dai ta hango su daga nesa ko kuma ta wuce ta kofar irin gidajen batare da tunanin itama akwai ranar da zata zo har ta iya tsintan kanta a irin gidajen ba.
Parlour suka yada zango wanda suna shiga Hajiya ta fara kwala kiran wata me suna _Na'eema_ bakin ta uku kafin Na'eeman ta amsa gami da fitowa dan kwalin ta a hannu tana kokarin daurawa a kanta.
" Ina kuka shiga ne haka da bakwa jin kira.?"
Tayi maganar tana me zama bisa daya daga cikin kujerun parlour.
" Wallahi Hajjaju bacci ke shirin dauka na..."
cewar Na'eeman da itama ta zauna daura da Hajiyar.
" Ga dai aiki na samo miki amma kafin nan bari inga ko ta gida ce"
Tayi maganar tana me maida duban ta Zaituna.
" Baiwar Allah sai gaki a gida na ko?"
'Murmushi kawai Zaitun tai mata.
" Ni suna na Hajiya Mardiya..amma anfi sani na da Hajjaju kamar dai yadda kika ji 'yan matana na kira na da shi...nasan bazaki gane ni ba amma ni nasan ki...kwanaki kalilan da suka gabata na ganki a wurin can har na baki sadaka kafin na wuce kuma ko ajiyan ma wallahi dan ke kadai na bi wancan titin cikin rashin sa'a kuma sai ga abinda ya faru...".
Cike da mamaki Zaitun ta dago kanta ta dubi Hajiyar tabbas ta tuna wata mace ta bata sadakan gudan Naira 'dari biyu sai dai a lokacin bata da cikakkiyar natsuwan da zata tsaya gani balle har ta tuna wacce ta bata sadakan.
Jin shiru daga 6angaren Zaitun ya sanya Hajjaju cigaba da fa'din.." Nasan abu ne mai wahala ki iya tunawa amma babu wani abu, tun inda aka kade ki mun bincika ko dakwai 'yan uwan ki amma bamu samu kowa ko wanda ya sanki a wurin ba, fatan zama tare damu bazai zame miki matsala ba..?"
Ta 'karashe da sigar tambaya.
Kai Zaitun ta girgiza mata alamar a a.
" Da kyau...kin taimaki kanki yarinya.."
Cewar Na'eema kenan tana murmusawa...yayin da Hajjaju ta cigaba da fadin
" Zaki zauna tare da mu ki zam 'daya daga cikin ahalin gidan nan...?"
" erh Hajiya Insha Allahu."
" Ki 'kirani Hajjaju nafi jin dadin sunan haka..".
" Ni nice shugabar gidan nan akwai kuma sabbin tsaruka namu na 'yan gidan nan da zasu biyo baya amma kafin bayyana su gare ki sai naga kin saki ciki damu tukunna, a yanzu dai ina so naga walwala a fuskar ki kamar yadda zaki gani ga sauran 'yan uwan ki fatan kin fahimce ni..?"
Da kai Zaitun ta bata amsa.