Sashe 124
Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Amrah tana kuka take ha'da musu kaya..da 'kyar Mummyn nata ta samu ta nutsu har akayi kwanaki biyu sannan tasaka driver ya maida ta gidan mijin ta ganin ta kasa kwantar da hankalin ta.
Bayan ita a ganin ta gata take yi mata.
Duk yadda taso fahimtar da ita rashin muhimmancin auren ga Rayyan Amrah bata fahimtar ta.
Taso ta nuna mata manufar auren ta kuma bata tabbacin Rayyan fa bai san da batun auren ba kwata kwata, babu mamaki kuma da zarar ya samu lafia ma ya saki yarinyar tunda ba shi yace yana so ba, baya ga haka ma kin manta 'yar aiki ce kika ce? Ki tuno waye Rayyan ki sannan ki kiyasta ta yadda zai amincecda auren wata yar aikin gidan sa..."
Duk Amrah bata nutsu ta fahimci Mummyn ba balle ta gane abinda take nufi.
Tun dawowar ta gida kuwa Ammi ta owa6i kowa akan btankata ko sake maida abinda ya wuce.
Hatta da Anty Madeena Ammi rokonta tayi akan dan Allah kar ta tanka Amrah, da kanta ta tafi da kanta ta kuma dawowa dan haka su zuba mata idanu kawai.
Hakan kuwa akayi tsakanin su sai dai idanu da dauke kai dan kowa na jin haushin kowa cikin ransa.
Sosai kumacsuka dauke kafafu a 6angaren Rayyan yanzu sbd gudun fitina inji Ammi musamman sbd ganin Amrah ta dawo.
Sun kuma san baya da karancin samun kula a yanzu ballecsuji damuwa...dan Zaitoon na yin iya kokarin ta kamar yadda ta alkawarta abaya.
Sukan je ne kawai su duba shi da safia da kuma kafin dare in angan su zaunevtare da shi yanzu sai dai in bukatar hakan ce ta taso.
Arfan ne dai kam suka ce dama ai nasu ne, Anty Madeena ce dai kam yaron ko kallo bai ishe ta ba balle uwar sa.
Salmerh😘
[23/11/2022, 4:32 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕
*( 'Yata ce)*
*Wattpad@*
_Serlmerh-md_
🅿️ *...72*
........Tsakanin Amrah da Zaituna babu wani maganar kirki sai dai banzan kallo da harara dake tasowa daga 6angaren Amrah, zagi kuwa babu irin wanda bata sauke mata, sai dai Zaitun bata ta6a tankata ba, bata ta6a 'daga idanu tayi mata duba sau biyu ba sai ma 'karin kyautatawa da take yi mata dan har a yanzun Zaitun bata raba kanta da yiwa Amrah hidima ba.
Ganin daman ta ta sararawa Zaitoon da yawan masifar domin bata kula ta, kuma tana jin shakkar ranar da zata kaita bango tasan abin bazai musu kyau ba sam..domin bata mance dukan da ta ta6a sha a wurin ta ba.
Zaitun ba shiga sabgar ta take yi ba, illah ayyukan gaban ta kadai koda yaushe take kokarin sauke nawin su akanta, dama Amran ce ke takalo ta amma sanin da tayi cewar ita tai musu kutse cikin rayuwar su yasa bata ta6a tankata ba.
Kuma har yau 'din nan Amrah bata yiwa Rayyan komai wai dan ta tallafawa Zaitoon da wani abin ko kuma dan samun lada bata ta6a ko kwatantawa ba.
Takan dai yawaita jifan Zaitoon da habaicin dama aikin ta kenan, sbd kwa'dayi da shishshigi sai da tayi abinda yasa aka aura mata Rayyan, toh ta gama bautar da kanta duk a abanza ne domin tana da ya'kinin da Rayyan ya dawo hayyacin sa ubanta zai ci...aceawar Amrah Mmn Arfan kenan...lolz
Zaitoon bata ta6a tankata ba, after all ita kanta tasan abinda Amran take fadi gaskia ne..kuma cikin shirin zuwan lkcn take kusan kowacce rana, tunda Allah ne ka'dai yasan lkcn da zai farka, yanzu ne, anjima, gobe ko rana ta gaba.
Domin Dr Fawwaz ya 'kara tabbatar musu da cewa yana iya farkawa cikin ko wani lkc shiyasa maganganun Amra basu ta6a damun ta ba balle taji haushin su.
Amrah bata da'de da dawowa gidan ba zirga-zrigar Sultan ta yawaita sosai a sashen, abin mamaki kuma a duk shigowar tasa ba lallai ne kaga ya isa ya duba jikin Rayyan ba...sabgogin gaban sa yake yayi ficewar sa kawai.
Idan baka sani ba kuma sai ka 'dauka sbd Rayyan yake shigowa sashen, musamman yanzu da yake su Anty ba zama sosai suma suke a 6angaren ba yanzu, hakan yasan kowa ke aikata son ransa batare da tsoron Allah ba.
Sukan yini basu shigo 6angaren ba...sbd Ammi ta hana su yawan zarya a sashen afadar ta cewar tunda ga matan sa har biyu tare da shi su din sai su dan sarara.
Nan ma hakan bai yiwa Ammi ba, masifa ta fara wa Anty Raihana da kananun mita akan ta koma 'dakin ta, dole badan taso ba ta fara shirin tafia, dama kusan kullum suka yi waya da yaron ta Bassam sai yayi mata kukan taki dawowa...ita dama tana tunanin Rayyan ne, tsananin tausayin sa ke ninkuwa mata a zucia, gani take tamkar hankalin ta baxai kwanta ba idan tayi nisa da shi.
Anty Madeena ma na shirin komawa gidan ta da suka canza dan wancan bazai zaunu ba dole sai an masa gyara sosai.
Shiyasa yanzu ri'kon Mufee ya fara dawowa hannun ta, sau tari ma da ita ake mi'ka yarinyar makaranta..wani bin sukan kwana su kuma yini tare su da juna.
Amrah rayuwar ta take son ranta duk ta mance da batun rashin lafiyar Rayyan ba 'karamin holewar su suke da Sultan ba..a hakan kuma ba 'karamin kishi take ji cikin zuciyar ta akan Zaitoon ba.
Abu guda ke taka mata birki shine sanin manufar auren nasu shiyasa sau tari ta ke dan iya danne kishin nata tai ta dariuar mugunta cikin ranta.
Zaitoon ma ranar da ta fahimci abinda ke faruwa ba 'karamin ka'data abin yayi ba.
Sam bata ga aikin wayo ko dabarar Amra anan wajen ba.
Sau tari bata sanin shigowar Sultan sai dai taga fitar sa kawai.
Wani sa'in kuma ko taga shigan sa bata sanin lkcn da yake fita.
Kuma tasha cin karo da shi yana 'dakin Amra tamkar shine mijin ta ba Rayyan da ke kwance.
Ba tun yau ta fahimci kazamtacciyar ala'kar da ke tsakanin su ba tunda da kunnan ta ta ta6a ji suna magana akan Arfan cewa na Sultan ne ba Rayyan ba.
Ta kuma fahimci hakan ya faru ne bisa kuskuren da su kansu basu san da shi ba, a zaton wannan kadai ya isa yasa Amra shiga taitayin ta ashe ita kam sake bu'de mata 'kofar holewa ma yayi.
( Yah Rabbis- samawati ka tsarkake mana zucia...Ameen).
Kwanaki tana jin gwagwarmayar da suka.sha akan yaron domin lkc guda ya fara rashin lafia sosai suka rasa me ke damun sa, 'karshe da suka dangana da asbiti nan aka tabbatar musu da cewar yaron na dauke da cutar sickler ne.
Sun sha wahala sosai har sai da aka 'kara masa jini..kuma Allah cikin ikon sa aka rasa jinin da yazo 'daya da nasa sai na Sultan.
Hankulan su ya Ammi ya tashi sosai da jinuar yaron, banda rudani da suka shiga na.yadda aka yi yaron ya kasance mai cutar sickler domin a sanin su Rayyan jinin sa lafiyayye ne.
Duk irin ru'danin da suka shiga Anty Madeena kallo ma basu ishe ta ba, sai ma inta lura da yadda Sultane ke rikicewa sai ta kya6e baki cikin ranta take ayyana ranar da zata tona sirrin su ga kowa.
Sultan da Amra basu samu kwanciyar hankali ba har sai da yaron nan ya dawo dai-dai, a hakan wai duk Sultan na karyar sbd Rayyan yake komai...alhali tun bayan haihuwar yaron da ya tabbatar nasane kauna da soyayyar yaron suka yi masa ram da zuciya.
Amra ce ta fara ziga Sultan akan 'kaunar da taga su Anty ke nunawa Mufeeda dan abin na mata ciwo sosai, musamman lkcn da Arfan bai da lafiya duk ta lura da Anty Madeena yadda ta nuna halin ko in kula da su, sa6anin yadda take yiwa Mufeeda, tari wannan idan yrinyar tayi sai ta tabbatar na lfia ne kafin take samun natsuwa.
Wani gefen kuma haushin ganin yadda su Marwa suka ha'de kansu da yaron ta da yake 'dan gida alhali ita Mufee ba kowan kowa bace agare su face karere...'diyar 'yar aikin gidan su.
Bata san cewa 'kaunar daga zuci take ba, 'kaunar daga indallahi ce, dole yadda zaka ji naka a zuciya sai yafi na wani daban nauyi.
Tace sam ni ban yadda da su ba ma, da farko na 'dauka ko tayata rainon 'diyar ta take sbd itama na musu hidima da Rayyan...amma daga baya sai fahimci abin nasu fa ba haka yake ba, kauna ce ta gaskia wlh suke wa yarinyar, har wani 'yar kama naga yarinyar keyi da Marwa fa bansani ba ko dan na kwana biyu banganta bane oho...amma ada ban ta6a lura da kamannin nasu ba sai yanzu...haka nan kawai nk ji araina suna da alaka, kuma ma idan ka lura zaka iya tabbatar da magana ta, kaga har yau babu wanda yasan dangin Zaitoon balle asan uban 'diyarta ta....
Shiru Sultan yayi ya tsura mata idanu, zuciyar sa yake ji na fa'duwa sosai gami da luguden gudu.
Ya jima da fara zargin wata ala'ka 'ka'k'karfa tsakanin su da yarinyar nan sai dai rashin 'kwakkwaran hujja bayaga kammannin bai ga komai ba, duk iya tsawaita tunanin da yy da hakan ya kasa hasaso ta inda hakan zai iya faruwa, sannan gefe guda yafi tsoron ace wannan yarinyar jinin Rayyan ce..duk yasan Rayyan farin sani, yasan matan banza basu ta6a birge Rayyan balle wata tarayya ta ha'da su...wannan dalilin yasa bai bawa zargin nasa muhimmanci ba duk da haka da gangan ya shirya harin gidan Anty Madeena domin ya 6atar da kowa, ya so ya 6atar hadda zargin sa gaba 'daya amma bai samu nasarar hakan ba.
Sai kuma gashi yau Amrah na sake yi masa ishara akai.
Sai yanzu yaga wautar sa da kansa..meyasa tun farko ma bai binciki wace ita da dalilin zuwan ta gidan ba har ya yadda ya bar zuciyar sa fadawa tsananin kaunar ta ta yadda bai san ta ina zai fara raba kansa da shi ba.
Hakika shi sauna ne, akan hakan sam tunanin sa bai yi aiki ba.
Tun bayan faruwar lamarin bai sake bi takan yarinyar ba but maganar Amrah yanzu ya sake ankarar da shi...dole ne kuwa sai ya binciki lamarin ya kuma dauki mataki in dai zargin su shi da Amrah ya kasance gaskia.