Sashe 157
Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tausayin ta sosai ya kamani, cikin natsuwa ta yadda zata fi fahimta ta na furta" Hajiya ki daina maganar idan yana damun ki, ni ba sai kin sanar da ni komai ba, ba bukata ta in san wace ke ba ko ban san ki bama zan iya taimaka miki iya iyawa ta balle ke da nake da yakinin cikin wannan halin ko maikyin ki ne bazai ki taimakon ki ba indai yana da tausayi aran sa.."
Kai matar ta girgiza min sannan cike da 'karfin hali ta 'dago kai tana murmushi tace" Ai dole ne in baki labari na 'kanwa ta, baki so idan mun ha'du a wani wuri ki yi saurin tunawa da ni..?"
" Wallahi ko iya haka ma bazan ta6a iya mantawa da ke ba, na koyi wani ilimi tare da ke sannan na fahimci abinda ban san haka yake ba tsawon rayuwar da nayi a dunia, sannan kin mallaki abinda ko cikin bacci na na gansu da farin ciki nake farkawa balle kuma a zahiri kinga kuwa babu ta yadda zan iya mantawa da ke a rayuwa ta...".
Na bata amsa cike da yakinin da na tabbatar hkn yk har a zucia ta.
Tace
" Hakane amma duk da haka ya kamata kisan ni wacece da kuma inda na fito, sannab nima ina so in san ke wacece domin kin yi min taimako sosai, kinga rikicewa driver yy sakamakon 'karan harbe harbe da muka jiyo ta ko ina harma bamu san takamammam 6angaren da abin ke fitowa ba.
Tafiya kawai yake batare da sanin inda ya nufa ba sai dai da yake a rikice yake shiyasa tu'kin be yi wahalar 'kwace masa ba muka gangara gefen hanya bai kai ga saita tu'kin ba ma muka ci karo da wata bishiya can bakin titi, shikam ma bansan wani yanayi yk ba a halin yanzu..nima 'din nasan kila Allah yy niyyan ha'da ni da ke ne shiyasa ya tseratar da ni..."
Hawaye ta goge gami da ajiyan numfashi idanun ta ta sau'ke kan babyn dake hannun ta sai ta girgiza kanta, a hankali ta sake 'dago kanta sannan ta cigaba da fa'din" Kin ga ikon Allah..ciki na bai ko kai lokacin haihuwa ba amma wuya ta sani haihuwar dole..ina da saura kusan sati uku fa agaba...amma Alhamdulillah zan ce, tunda cikin kudurar sa gashi ya raba ni da su lpy.
Ban ce da ita komai ba banda kallon fuskar ta da nk.
Allah ya yiwa matar wani baiwa ne na kyau da cikar kamala, kyau irin mai matu'kar birgewan nan...komai na matar mai kyau ne..duba 'daya zaka yi mata ka fahimci cewa 'yar gayu ce ta gaske banda hutu da karara ya bayyana kansa a zahiri.
Kai ta jinjina sannan ta maida idanun ta kan jakar ta tace" Ban san inda wayata take ba...amma bani jakata zan rubuta miki wani abu".
Ta fada da wani irin sanyin muryar da ni da kaina sai da jikina yy sanyi kalau, mi'ka mata jakar ta nayi ina jin babu da'di cikin raina.
"....Yanzu kam amanar mu duk a hannun ki yake ni da abinda na haifa, daga yanzu har zuwa lokacin rabuwar mu kinji...."
Ta fada tana mai lalu6a cikin jakar fuskar ta da murmushi.
Nima murmushin nayi mata mai sanyi sannan ta cigaba" Insha Allahu ko na tafi zan dawo saboda ke ka'dai Zaitoon...kin min halacci kin taimaka min a lokacin da nafi bukatar taimako, baki 'kyamace ni ba duk da nasan ni din a yanzu abin 'kyama ce...nagode kinji, nagode sosai 'kanwa ta...miji na kansa idan yaji labarin ki zai so yi miki tukuici da duk abinda yasan zai faranta miki, domin bashi da wani buri a duniyar nan fiye da yaga na haife masa abinda ke ciki na, shi mahaifiyar sa da duk familyn sa sun 'dokantu da son ganin abinda zan haifa musu..suma nasan zasu so ganin wacce ta taimaka har jikokin su suka samu second chance na sake rayuwa a duniya...ban san me zan baki ba bani da komai yanzu amma ga wannan dan Allah kar kice min a a, nagode sosai da taimakamin da kika yi..ina miki fatan alkhairi, Allah ya baki miji na gari ya raba ki da iyayen ki lpy..."
Tayi maganar tana mika min ku'di da bazan iya cewa ga adadin su ba.
Baki na na furta" Ameen sbd jin dadin addu'ar da tayi min nake kuma girgiza mata kaina da sauri nace" Hajia ni kam me zan yi da ku'di ki bar abinki zasu yi miki amfani ai..kinga nima Hamma na ya na bani idan bani da shi...nima nagode da kk yadda da ni Ubangiji Allah ya raya miki ya ranki ya sa musu albarka".
In sun girma kice musu ina kaunar su..kuma zan cigaba da kaunar su har karshen numfashi na...".
Murmushi matar tayi min kana tace" 'daya ce ai ta rage Zaitoon, shi wannan bai ma zo da rai ba"
Ta yi maganar tana kallon wanda ke ri'ke a hannun ta wanda ta ha'da shi da duk mabiyan su ta lullu6e shi tare da su.
Kai na girgiza cike da alhini ina duban yaron nima.
Hawaye naji yana gangaro min..a hankali nace" Kenan shi bashi da rai ko?"
Kai ta jinjina min tana kallon fuskar yaron tace" Kamar mahaifin su ne da shi na san da zai fi kowa farin ciki idan ya gansa, amma Allah bai tsara ya rayu tare da shi ba.."
Ta 'karashe maganar tana mai 'dagowa ta dube ni, dai dai ina share kwallan da ke sauko min.
Cike da mamaki na tace" Kuka kuma 'kanwa ta, baga little princess 'din ki tare da ke ba..kar ki damu kinji, Allah yafi mu sanin dalilin da yasa ya 'dauke shi.."
Da kai na amsa ta.
" Share hawayen toh in baki wani lbr...".
Yadda tace din nayi amma hawayen sun kasa tsayawa.
Ita kuma ta cigaba" Auren mu ya dauki wasu shekaru yanzu amma sai wannan shekarar Allah ya nufe ni da samun haihuwa wanda ya kasance babban abin farin ciki ga duk familyn da nake aure, ma'aikaciyar lafiya ce ni hakan yasa ban sha wahala wajen gano yara biyu ne a ciki na ba, sai dai na 6oyewa miji na hakan da burin yi masa bazata sai kuma kinga yadda ta kasance...."
Tace" Ya hana ni wannan tafiyar amma na nace sai nayi...ido ta lumshe tana mai saukar da hawaye...
Nima ina hawayen nace" Ki tashi muje gidan Innah ta toh kuyi wanka in yaso sai in kar6o miki wayar Hamma Bukar ki 'kira mijin naki ki sanar da shi in da kuke.."
Na fada ina mai yunkurin mi'kewa.
" Ya sunan garin naku?" Ta jefa min tambaya.
Da sunan garin na mu na amsa ta duk jiki na yayi sanyi.
Jinjina kanta tayi amma sai naga tamkar bata da niyyyan mi'kewa kamar yadda ni na yunkura duk da ni din ma ban kai ga mikewan ba.
Ganin hakan yasa na sake fa'din" Hajia ki tashi mu tafi ko.. naga kuna bu'katar kulawa sosai, Inna ta zata kula da ku har zuwa lokacin da za'a zo a tafi da ku".
Jinjina kai tayi tana murmushi tace" Haka kawai fa yau 'din ina jin da'din hira dake, babu wanda ya min shaidar surutu daga dangi na har gidan miji na amma nasan ke kam zaki ce matar nan surutu ne da ita ko?"
'Yar daria nayi, domin ji nayi matar nan ta gama kamo tasha ta.
Kamar tasan abinda ke raina.
So nake ta tashi mu wuce gidan Inna ta amma ita ta tsaya surutu ni kuma ba shine damuwa ta ba a wannan lkcn.
" Bari dai in tashi muje din..kar na 'kure hakurin 'kanwa ta.."
Ta 'karashe maganar tana yunkurin mi'kewa tsaye...nima sai na mike.
Ganin yadda zanin jikin ta ya 6aci sosai ne ya sanya saurin cire Hijabin kaina na mi'ka mata nace" Hajia ki cire mayafin na ki 'daura shi kan zanin jikin ki sai ki rufa wannan..bai dace mu ratsa cikin mutane kina a wannan yanayin ba..".
Nayi maganar batare da na dubi fuskar ta ba.
Kallo mai kyau tayi min sai kuma ta girgiza kanta alamar a a.
Da sauri nace
" Dan Allah ki rufa kin ga fa zanin ya lalace kuma sai mun bi cikin gari kafin muje gida...".
" To ke haka zaki tafi?"
" Kar ki damu da ni Hajia ai ni garin mu ne bakomai..."
" Yanayin jikin ki da ke kanki bai nuna alamun kin saba cire hijab din kanki a ko'ina ba...bana so in shiga hakkin ki kanwa ta..."
" Hajia ba komai, yau ka'dai dai nasan bazai zame min damuwa a zuciya ba, baya ga haka ma ai a yanzu kam nasan kin fini bukatar sa...".
" Nagode sosai...."
Tace tana amsar hijabin.
Kamar yadda nace mata haka tayi sai ya kasance daga jinjirar dake rungume jikina babu komai...fayau nake ji iska na shiga na ta ko'ina ba.
Da gaske fa naji wani iri kasamtuwar ban saba hakan ba.
Amma karo na farko kenan a rayuwa ta da naji har a raina zan iya ratsa cikin garin namu batare da hijabi na ajiki na kamar yadda na saba ba, koma 'dan kwali babu akai na sai 'kananun kitson da suka sakko min saman kafa'da ta.
Bana jin da'din yanayin amma haka ta daure saboda rufa sirrin matar agani na yafi min kwanciyar hankali...tausayin ta tare da yaranta shi yafi komai tsaye min ya mamayi zuciya ta a wancan lokacin.
Nice ke ri'ke da jaririya mai numfashin yayin da matar ta rungumi 'dayan da tace bai zo da rai ba.
A hankali muke tafiyar dan matar 'ko'kari kawai take yi amma da kyar take 'daga 'kafafun ta take takawa.
A can gida kuwa hankalin Hamma Bukar in yayi dubu ya tashi, kowa na gida Goni ma tuni ya iso, gari shau kamar ba'a yi halitta ko guda a ciki ba kowa ya nemi ma6oya sbd tsoro illa Yaah Bukar da sam ya kasa samun natsuwa kasantuwar har yanzu ban koma gida ba, sosai yayiwa Iyami mita akan tura ni jejin da tayi bayan tasan ma baisashshiyar lafia gare ni ba, daga duba 'daya idan ka yi masa zaka fahimci tsananin tashin hankalin da yake ciki.