← Book details Binteee Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 218

Sashe 27

Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

'Daya cikin yaran sa ne ya bayyana a wajen da 'dan sassarfa wanda da isowar sa ya fara kokarin mikawa Dr Rasheed wani abu amma bai bi takan abin ba.
" ..lock the door.."
Ya fada masa yana me matsawa daga bakin kofar towards inda Zaitun ke durkushe, daga gaban ta ya tsaya sai tai saurin yin kasa da kanta still bakin ta a toshe dayan hannun kuma na rungume da Mufee.
" Me ya kawo ki nan..?"
Bata iya budan baki ta bashi amsa ba sai kai data fara girgizawa da alamun roko.
"...Me ya fito da ke, me kunnuwan ki suka ji...?"
Yayi maganar da buga mata tsawan da yasa ta sakin guntun fitsari.
Duk kammanin sa sun canza sun koma wani abu daban, ashe duk kallon da take masa da fuskar rahamar sa take ganin sa.
Baya kadan taja sbd yanda ta tsure, cikin tsananin kuka da nadamar fitowar tan tafara fadin".. wlh ni babu abinda naji,dan girman Allah kayi hakuri...".
A fusace yayo kanta ya sauke mata wani marin da ya sake gigita"...Don't sorry me...fada min abinda ya fito dake..".
Zaman dirshan Zaitun tayi tana me sakin wani wahalallen kuka tama kasa furta komai.
Bata yi aune ba sai ji tayi ya sa mata abu akai akai wanda tashin farko ta fahimci cewa bindiga ne.
Cak kukan ta ya tsaya ta fara gani taratara yau ita ce bindiga akanta innalillahi...tama kasa karasawa.
" wa ya baki iznin fitowa...?"
Ya sake jefa mata wata tambayar wanda da kaji kasan ransa ya kai kololuwa wajen 6aci.
"...Wlh...bakowa...tsoro, tsoro naji shiyasa na fito...amma wlh ban ji komai da kace...".
Yaron da ke tsaye daga bayan sa ne kadai yayi murmushi fahimtar da yayi cewa rudewa ce ta sa ta fadin hakan.
Yanavso ya bawa Dr hakuri amma yafi so yaga karshen game din.
"...Tsoro ko..?"
Dr ya tambaye ta.
Da sauri ta dage kanta alamar erh jikin ta na kyarma.
"...Yanzu kika fara rayuwa cikin tsoro har sai ranar da abinda kk ji ya bar kwanyar ki...a feel like in fasa mk kwakwalwa yanzun nan but kinci albarkacin Babyn nan..".
Ido ya kara warawa akanta ya cigaba da fadin.." Daga yau duk abinda kikaji ko kk gani ya zam a cikin cikin ki...furta wata kalma ko ishara game dani daidai yake da daukewar numfashin ki daga ke har wannan da hannu na zan fasa mk kai...kina jina...?"
Da sauri take dage kai hawaye na sake gangaro mata fatan ta daya shine ya ingiza keyar ta wajen gidan sa, ya korata, ta gwammaci rayuwa kan titi da wannan rayuwar tare da Dr...ashe dagaske bindiga ta gani a hannun sa jiya, ashe ba mafakar natsuwa ta sama musu ita da ita Mufee ba.
"...Oya back to ur room...".
Yayi maganar yana juyawa cike da sassarfa ya bar wajen illah wancan dayan da yazo.
Shine ya sake maimaita mata ganin bata motsa ba.." tashi ki koma 'dakin ki..".
Kasa motsawa Zaitun tayi illa ido take kara warewa.
" Daki kuma...?"
Ta tambayi zuciyar ta..meyasa bazasu fitar da ni ba.
'Dagowa tayi ta kalle shi yana sanye ne cikin ba'ka'ken kaya fuskar sa ma rufe take da face mask, kamar dai yadda Dr Rasheed yake shima.
"...Dan Allah bawan Allah ku kore ni, ku ce in bar muku gidan ku dan Allah..."
Bai ma bari ta kai karshe ba ya 'dago mata bindiga ya saita kanta, tuni tai tsit ta fara kokarin mikewa amma ta kasa da rarrafe ta fara jan jikin ta har zuwa dakin.

Wancan me zai yi in ba dariya ba bayan ta bar wajen a fili yace" ga kau'di ga tsoro..".

Da kyar ma ta gane dakin sbd tsabr rudewa..in dai hakane ko bakin kofa bazata sake zuwa ba Insha Allahu, ba karamin nadamar fita tayi ba.
" Wannan wace iriyar ukuba ce haka...?"
" Gaba kura baya siyaki...haka kenan zai ta kasancewa da ita a ko wani lkc...?"
Yau kadai take ji cikin ranta da zata sami hanya ba abinda zai hanata komawa can gida inyaso ko kashe ta ne ta kwammaci suyi yafi mata wannan tashe tashen hankulan.
Ranar ko rintsawa batai ba har akayi asubah...Mufee kadai ta iya dorawa saman gadon ita kam kafafun ta ma nauyi sukai mata, haka anan kasan tiles ta sulale..kafin safiya wani zazzafan zazza6i ya kamata.
Me kawo musu breakfast ne ya fara fahimtar halin da take ciki..amma bai tanka ba.
Ita kam ma tashin hankalin da take ciki be bari tabi ta kan zazzabin ba.
Mufee ta bawa abincin taci itama ta tuttura sbd bata san ta bawa Mufeedah abu batare da itama ta ci ba gudun abinda zai cutar da yarinyar.

A daddafe ta kai su bayi ta watsawa Mufee ruwa itama tayi.
Haka tazo ta zauna gami da rungume Mufee, duk ta zare ta fita hayyacin ta tai tsumu da ita tamkar yakuwan da yaji ruwan zafi.

Mufeeda kam da bata san me duniya take ciki ba sai surutan ta take irin na yara tana lafe a jikin ta.

Salmerh😘
[20/9/2022, 12:32 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕
*( 'Yata ce)*

*Salmerh MD*

_Wattpad@ Salmerh-md_

🅿️ *...18*

Dr Rasheed ya kasance likita ne a zahirin rayuwa da kuma fahimtar kowa ciki kuwa hadda mahaifan sa da sauran dangin sa, Dr Rasheed ya kasance shine yaro na farko kuma 'da namiji tilo wajen iyayen sa inda yaci sunan kakan sa wato mahaifin baban sa Abdulrasheed, dalili kenan da ya sanya mahaifiyar sa ke kiran sa da Abbah yayin da suke tsananin so da kaunar sa tamkar shi daya Allah ya basu, duk kuwa da kasancewar su masu karancin dukiya hkn bai sa sun gaza wajen samar masa ingantaccen ilimin zamani har ma da na addini ba hkn kuma ya cigaba da wakana har ga sauran kannan sa, sun tsaya tsayin daka wajen ganin sun daidaita tarbiyar yaransu yadda ya kamata kuma Alhamdulillahi basu samu tsaiko game da hkn ba, sai dai wasu lokutan rubutacciyar kaddara ta kan yi tasiri ga rayuwar mutun ne sa6anin yadda ake zaton, duk kokarin ka baka isa gyarawa mutun zuciya ba sai abinda Allah mahaliccin sarki ya tsara kuma yaso gani game da bayin sa, san zuciya da kuma babban buri na son tara abun duniya su suka yi tasiri a zuciyar Rasheed hkn kuma ya sanya shi karkacewa daga tubar da iayen sa suk 'dora shi batare da sun sani ba, lokaci guda ya fada mummunar harka ta fashi da kuma garkuwa da yaran manyan mutane ana biyan sa makudan kudade.

Yana da yaran da yk aiki da su guda biyar kacal wadanda su kadai ya aminta da su, kuma da su kadai yake aiki, su kadai ne suka san cewa yana wannan harkar a zahiri bayaga wasu manya da suka kasance masa jagora.

Rasheed yana da wani tanfatsetsen gida da ko mahifiyar sa sai da tayi mamaki lkcn da ya mallaki wannan gida duba da cewa aikin likitan ci kawai yk, kuma mahaifin sa me karamin karfi ne su kansu gidan da suke ciki shine ya canza musu kafin ma ya siya nasa na kansa, domin ada wani dan madaidaicin gida ne suke zaune kuma ya taso a cikin sa wanda yake mallakin mahaifin sa ne, daga baya ya canza musu muhalli wanda ya matukar basu mmk, da 'kyar ma mahaifin nasa ya amince ya koma gidan bawai dan yana zargin dan nasa ba a lkcn kawai dai acewar sa shi ya saka iyalin sa a ciki su inda suke ma Alhamdulillahi ya ishe su rayuwa, sai dai Rasheed sam yace a a daga karshe dai bayan an kai ruwa rana dole mahaifin nasa ya amince suka koma bayan Rasheed ya hada da wasu manya cikin ahalin su da kuma abokan mahaifin nasa.

Bayan komai ya daidaita ne sai yaje ga mahaifan nasa da batun kasuwanci da yake yi ta kasa da kasa na kayan masarufi ya kuma bayyana musu cewa ya dade da fara wannan harkar, ba laifi sun ji dadi sun kuma saka masa albarka.inda daga karshe sukai masa nasiha sosai akan kiyaye haram cikin lamuran sa.

Dr Rasheed yana da matar aure kwaya 'daya mai suna Hameedah yana kuma da yaran sa biyu mace da namiji...Wildan shine babba wanda ya kasance yaro 'dan shekara hudu da haihuwa sai kuma Naina wacce ba ta ajiye shekara biyu kwarara ba.

Ya kanyi duk wani 6oyayyun harkokin sa ne a gefe kuma babu wanda ya ankare da shi har a yanzu, hatta Hameeda bata san da wannan harkar ba.
Ko da ya kasance yana yawan fitan dare a gidan bata ta6a damuwa da hkn ko bin diddigi ba sbd tasan yanayin aikin sa ta kuma san hkn na iya faruwa duk da yk itama din ba wani karatu me zrfi ke gareta ba, a yanzun ne take makarantar kuma yajin aiki da jami'oin gwabnatin tarayya ke yi dole ya dakatar da ita, tsananin kaunar da take yi masa kuma ya sanya a mafi yawan lokuta Hameeda bata ganin laifin sa balle ta tahume shi ta kan yawaita yi masa uzuri.

Dr Rasheed shine ya jagoranci harin da aka kai gidan Hajjaju a wancan lkcn, kuma bakin wani abokin aikin sa yaji komai akan Hajjajun, kuma kawai sunyi zancen ne as in hira dan yana yawaita ganin ta cikin asbitin kusan ma nanne kadai asbitin da tafi mu'amala da su, ya kan ganta amma be san wace ita ba sai lokacin da ta kai Zaitun sannan sai kuma yaga dacewar ziyartar gidan badan komai ba sai dan kawai ji da yy ance tana matukar murza Naira iya son ranta sbd da manyan alhazai take harkokin ta.
Chapter 27 · 0% Book details