Sashe 56
Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hannun sa 'Dan Maliki ya kamo duk biyu ya rike cikin nasa hannun ya cigaba da magana...Adam na jin yadda hannun ke rawa sosai amma bai janye hannun sa ba.
" Naji da'di sosai da ka tuna dani har ka ziyarce ni ba tare da ka yi duba izuwa ga tarin kurakuraina ba, ban ta6a zaton zaka zo gare ni ba ko cikin mafarki..hakika kai 'din 'dan halak ne, Allah yayi maka albarka ya yiwa rayuwar ka albarka ya kara haskaka imanin ka, amma ina mai sake rokon ka Adam ko bazaka yafe min ba, ko da bazaka sake ziyarta ta ba, dan Allah ko da sau 'daya ne cikin rayuwar ka, ka dube ni kai min duba irin na uba a zuciyar ka ko nima zanji da'di, na maka alkawarin zama nagartaccen uba daga rana irin wannan har 'karshen rayuwa ta, mahaifiyar ka ta riga ta koma ga mahaliccin ta, na sani Hafsat mace ce nagartacciya wacce har ta bar duniya babu wani abu guda da zan fito in nuna ko ince tai min na 6acin rai, duk abubuwan da suka ta faruwa nasan son zuciya ta ne kadai ke kawo su, kuma bazan 6oye maka ba na shiga tsananin tashin hankali da rudani game da rashin Hafsat na kuma yi nadamar duk abubuwan da nai mata abaya wanda ban kai ga neman yafiyar ta ba Allah ya kar6i rayuwar ta, bana son in sake wannan kuskuren a yanzu ga ni ga ka tun numfashi bai 'kare min ba da harshe na idanuwa na kallon ka nake rokon ka Adam ka yafe min kaji ka yafewa wannan mahaifin da ya rayu da tsananin son zuciyar sa shikadai batare da damuwa na na 'kasan sa ba..."
Hannun Adam dake cikin nasa yaji rikon ya bambanta, sosai Adam ya tamke hannun sa cikin na mahaifin nasa yana jin wani nutsuwa na shigan sa da bai ta6a jin makamanciyar sa ba..ba 'karamin mamaki 'Dan Maliki yayi ba da jin hakan sosai ya tsurawa hannayen nasu idanu cike da mamaki, a hankali Adam ya fara magana.
" Ni ban ri'ke ka cikin zuciya ta ba, nasan komai mukaddari ne, na kuma san akwai son zucia akwai jarrabawa, sannan akwai 'kaddara, na rasa Zaitun yes nasan nayi rashi but rashin Zaitun ba shine 'karshen rayuwa ta ba, ba shine karshen farin ciki na ba, tunda ina daku ina da kai, ina da Hajiya sannan ga Hafeez ku ka'dai kun ishe ni rayuwa amma komai ya wuce ban isa in canza komai ba, kamar yadda nima 'din ban fi karfin Allah ya jarrabce ni da daya daga cikin duk abubuwan nan ba...".
Da sauri 'Dan Maliki da farin ciki ya gama mamayar sa yana girgiza kai ya furta" Insha Allah babu ko guda da zai same ka, daga yanzu har karshen rayuwa ta addu'a zan ta rokon Allah ne ya kare min kai....".
Murmushi kawai yayi 'yar kadan sannan ya cigaba da fa'din..." A yau nazo gareka ne, ba dan neman alfarma ba, badan in maka jaje ba, ba nazo ne musamman dan wani abu ba nazo ne kawai a matsayi na na 'daa izuwa ga mahaifi na...."
'Dan Maliki da ya kasa hakurin jin 'karshen kalamin Adam sake rungume hannayen sa yayi yana fadin.. _Alhamdulillah_ nagode, nagode, nagode 'daana ubangiji Allah ya yiwa rayuwar ka albarka, ya baka 'yayan da zasu yi bika suyi maka biyayya Allah ya cigaba da haskaka rayuwar ka ya haska gaban ka da bayan ka, Allah ya jikan mahaifiyar ka ya kai haske 'kabarin ta....".
Addu'a kawai yake ta jerowa harshen har na sarkewa.
"...Thank u Abbah...Amin Nagode sosai nima ka yafe min..."
Adam ya fada yana duban sa cike da rauni.
" Bakai min komai ba, baka ta6a min laifin komai ba Adam..kuma har abada bazaka ta6a zama mai laifi a waje na ba da iznin Allah...".
Murmushi Adam yayi sannan ya mi'ke a hankali ya zare hannun sa cikin na mahaifin nasa sannan yace " Zan tafi..."!
" Thank u son..Allah yai maka albarka.."
" Amin Abbah.."
Har ya juya sai kuma ya tuno wani abu hakan yasa ya juyo " Baka bani labarin kowa naka ba, I mean labarin familyn ka gaba 'daya..."
Ka samu abokin ka Hafeez akwai komai tare da shi bani da isasshen lokacin da zan ma bayani da baki shiyasa na takaita komai....
Daga haka aka zo aka fice da 'Dan Maliki Adam na kallo amma bashi da ikon dakawatar da su, haka ya fita yana mai jin babu da'di but deep down yana jin sanyi cikin zuciyar sa, shi kansa 'Dan Malikin yanzu nutsuwa yake ji tana shigar sa, tamkar wanda akace masa freedom za'a bashi a yau din, bai ta6a zaton duk damuwar sa akan Adam take ba sai yanzun, hakika 'ya'ya Rahama ne, a yanzu wasai yake jin zuciyar sa ba kamar kwanakin da suka shu'de ba.
Adam na fita suka ci karo da Hafeez da ke ta kai kawo a inda yake zaman jiran sa.
Yana ganin sa ya taho da saurin sa fuskar sa da alamun damuwa yace..." Ya akayi ka dade haka, ka fa bani tsoro.."!
Murmushi Adam yai masa gami da fa'din " Worry not ba gani ba...".
Ido Hafeez ya zaro yana fa'din" kai din..?
Da mamaki, domin rabon da yaga fara'a kan fuskar abokin nasa har ya manta.
Tafiya suka fara izuwa ga tashar da zasu samu motar da zata maida su gida dan dukkanin su har yanzu babu wani da ya mallaki motar hawan kansa.
Hamdala kawai Hafeez ke yi cikin zuciyar sa gami da nuna jin dadin sa a fili.
" Hakika yau 'din farar tafia suka yi...basu yi tafiyar banza ba domin ga dukkan alama ta janyo gagarumar nasara tsakanin Adam da mahaifin sa.
Kasa jurewa yayi yana duban Adam yace.." Kamar ba kai ba..."
" Da akayi yaya...?"
" Ka fini sani ai 'dan air, yau ni Hafeez zanyi bacci har da minshari".
Ya fa'da da 'karfi yana duban sama gami da dafe 'kirji da hannun sa 'daya.
Duka Adam ya kai masa sai ya goce yana fa'din" Kai kyale ni in nuna wa Allah godiya ta..fatan kasa mi Alhajin lafiya...."."
Turus Adam yaja ya tsaya,
" Wani Alhajin kenan? kana nufin Abba na..?"
" Toh fa , sabon salo, nasan ban da ni ai, naka ne kai kadai duk duniyan nan babu wanda ya fi dacewa ya furta hakan sama da kai, amma ai ka amsa min tambaya ta dai ko..?
Daria dukkan su suka sanya sannan Adam ya fara fa'din " yana nan 'kalau ya mace in gaida ka da Hajiya ta..".
" Masha Allah abu dai yayi kyau...".
" Ya fa'da maka wani abu ne..?"
" Kamar me fa..?"
Shima ya maida masa amsar tambaya madadin amsar da yake bukata.
" Kaifa 'dan yawa ne wlh...wani abu dai haka bai fada maka ba...".
" Abubuwa da dama ya fada min..har ma yai ta samin albarka ni har zuri'ar da zan haifa gaba 'daya...".
Comment nd share to other groups please.
Salmerh😘
[23/9/2022, 10:51 am] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕
*( 'Yata ce)*
Wattpad@
Serlmerh-md
🅿️ *...35*
........." Ba wannan nake son ji ba Malam...kana nufin Alhaji bai sanar da kai komai ba? bai ambaci suna na ko sau 'daya cikin maganar sa ba...?".
Cewar Hafeez cike da nuna rashin jin dadin sa a fili.
Adam na dariyar shakiyan ci yace" Ji wani zance kai kuma, meyasa zai ambace ka bayan gani kuma gaban sa....?"
Wannan karon cike da jin haushi Hafeez ya kai masa naushi ya goce yana dariya sosai.
" Ka dallah malam sakar min mara...ba dai so kake kaji ba? Toh ya sanar da ni ya baka ajiyar kundin tarihin ahalin sa...kaga nima zan samu dangi nan kusa".
Murmushi Hafeez yayi yana hararan sa yace.." Shine sai ka wahal da ni..?"
Ba 'karamin dadi Hafeez yayi da wannan annuri da farin cikin da ga abokin sa a ciki...fuskar sa cike da fara'a yace" Toh bayan haka fa...?"
" Babu komai"
Inji Adam yana tafiya Hafeez ma kokarin jerawa da shi ya sake fadin" Ka tuna dai...".
" Ka manta asali ni ba gwanin mantuwa bane...?"
"Ai shikenan, amma dai ba kundin tarihi ka'dai Alhaji ya bani ajiya ba, har da kundin tattalin arzikin sa gaba 'daya ma'ana dukiyar sa wacce ya mika ta kacokam ga 'dan sa 'kwaya 'daya tilo wato _Adam Shaheed Jibrin 'Dan Maliki.._ ."
" Wasa kake ".
Adam ya fadi cike da nuna rashin kulawa ga maganar.
Ganin hakan yasa Hafeez fizgo hannun sa cike da kufula yace" meyasa kake maida komai wasa ne Adam? wannan batun fa ba na 'kananun ku'di nake maka magana ba, ina maka magana ne akan 'dimbin dukiyar mahaifin ka da ya tara ya kuma mallaka ta gareka...".
Ganin kamar Hafeez 'din dagaske yake ya sa Adam 'dan 6ata rai yana dakatawa da tafiyar ya fuskanci Hafeez 'din da kyau.
" Kafi kowa sanin bana bukata meyasa ka kar6i ajiyar sa..? ka maida masa abinsa".
Ya bashi amsa da iya gaskiyar sa sannan ya cigaba da takawa, wannan karam da 'dan saurin sa.
Cike da jin haushi Hafeez ya fara fa'din" Ba za'a maida ba Adam, bazan maida masa komai ba, wai anya kana cikin hankalin ka kuwa..?"
" Kafi.kowa sanin matakin da hankali na yake ba sai na maimaita ba maka ba, kamar yadda kafi kowa sanin ba dukiyar sa ta kawo ni gareshi ba?"
" Shi kansa ma yasan wannan ba ma ni ba, amma duk da hakan bai sa ya kasa mallaka maka ba...".
Fuska Adam ya had'e sosai ya wani 'kankance idanu yana duban Hafeez yace" wai dagaske kake ne...?"
Kai Hafeez ya jinjina masa alamun tabbatar wa.
" Ka mayar masa dukiyar sa Hafeez kwandalar sa bana bukata, ka manta ire- iren hanyoyin da yabi wajen tara dukiyar ne...?"