← Book details Binteee Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 218

Sashe 57

Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

" ban manta ba, amma ai da ka nutsu ka saurare ni bazaka furta hakan ba..."
" Ni dai dan girman Allah Hafeez ka maida masa kayan sa, burina a duniyar in samu yardar Allah mahalicci na na rabu da duniyar lafiya, na kuma san hakan bazai ta6a yiyuwa ba har sai na bi mahaifana, bana da mahaifiya sai mahaifi, na kuma yi kokarin wajen ganin na gyara mu'amala ta da shi ko a yanzu na mutu bazan ji bakin ciki ba, domin nasan tsakani na da Abbah na babu wata matsala...ban ta6a kwa'dayin dukiyar sa ba tun abaya ma, so mai yasa zanyi kwadayin rike ta a yanzu....wlh Hafeez bana bukatar komai daga cikin dukiyar sa, ka maida masa abinsa ba mamaki lokacin da Allah yayi fitowar sa suyi masa amfani...".

" Ta ya zan mayar bayan ba hannu na suke ba...?"

" Toh mecece damuwar ka kuma..tun da ba hannun ka suke ba? ka 'kyale ni da maganar hakan nan dan Allah Hafeez, ka mance kawai.."
" Tamkar amana ya bani Adam, sannan ni Alhaji ya wakilta matsayin jagoran da zan isar da ita gare ka saboda yadda dani da yayi da kuma sanin kusancin da ke tsakani na da kai amma komai na wajen Lauyan sa....nan ya zayyane wa Adam duk yadda suka yi da 'Dan Maliki, yadda ya kasafta dukiyar sa kashi kusan biyar, kaso hudu duk ya mallakawa gidajen marayu da sunan Adam kaso guda kacal ya rage yace na Adam 'din ne, ya kuma tabbatar musu da cewar babu haramun cikin wannan kaso gudan dai- dai da 'kwayar zarra.
" Duk da yake munanan harkoki masu yawa Alhaji ke yi amma bai yadda ya sirka dukiyar sa da ta haramun din ba, kowacce da ma'ajiyar ta ka yadda da ni Adam..".
Hafeez ya karasar da taushin murya.
" Toh me ze hana duk a ha'da akai gidan marayun...?"
Adam ya tambayi Hafeez da iya gaskiyar sa.
" Baza'a kai ba Adam, wannan mallakin ka ne, ka daina yankewa mutum hukunci bisa halayyar sa ta baya domin lokaci yana koyar da su darasi kuma ya kan canza su, ina tabbatar maka da cewa matukar ka sake bijire wa wannan lamarin zaka zo kayi dana sani watarana, dana sani ma marar amfani".
Cike da jin haushi Adam yace..." Fata kake min ko me ne hakan Hafeez?".
Hannaye ya 'daga sama" ohh no..gaskiya kawai na fa'da maka...".
Tafiya suka cigaba da yi babu wanda ya sake furta wani abu.
Hafeez 'kasa- 'kasa yace" mutum sai shegen taurin kan tsiya ana baka kana 'kin kar6a".
Abinda kawai ya bawa Hafeez mamaki shine yadda kaso guda cikin dukiyar Alhajin yaso bashi tsoro dukiya ce bata wasa ba da ya tabbatar matu'kar abokin sa ya mallaka ya gama da babin talauci a rayuwar sa, duk wani fadi tashin neman sa sun 'kare hatta jikokin sa sai sun an tara musu, dan shi kansa Alhaji Jibrin sai da ya bashi kyautar 1ml matsayin nasa tukuicin na zama da 'dan sa da yayi da zuciya 'daya, ya bawa Lauyan sa ma tasa kyautar haka ma Hajia Talatu.

Kwanciyar jinya da Adam ya da'de yana yi yasa suk bai san da wannan labarin ba balle yasan anyi haka.

Har suka isa gida babu wanda ya sake tankawa 'dan uwan sa, ko cikin mota magana bata ha'da su ba, kowa abinda yake cikin ransa daban.

Duk yadda Adam yaso ya zame hakan faskara yayi, domin wanan karan Hafeez nuna masa yayi cewa erh shima fa ba baya ne wajen tirjiya da taurin kai, ya kuma nuna masa erh lallai ya isa da shi, da gudummuwar Hajiya Talatu komai ya kammala, dan itama ta tsaya tsayin daka wajen ganin bai bijirewa sakon da mahaifin sa ya bari a basa ba.

Adam dagewa yayi akan aha'de duk a mi'ka gidan marayu kamar yadda ya bada sauran amma suka ce sam baza'ayi haka ba...Hajiya Talatu da dama babban burin ta a duniyan nan bai wuce ace taga Adam 'din ta ya zam wani abu shima a fadin duniyan nan ba hakan yasa ta dage sosai kan lamarin, haka Lauyan Alhaji Jibrin 'din shima har ransa sai da ya sosu da taurin kan Adam 'din gashi yana so ya mika masa komai ne zai bar kasar zuwa wani taro...'karshe dole Adam ya sa hannu ya kar6a badan ransa yaso ba.

Aganin sun kasa fahimtar sa ne kawai, amma ai Allah da kansa yace mu gujewa haramun, kuma yace duk jikin da aka gina shi da haramun makamashin wutan jahannama yake kasancewa, abinda yake tsoro kenan dan shi yasan waye 'Dan Maliki.

Sai da Lauyan 'Dan Malikin ya sake tabbatar masa da cewa asali Alhaji bai ha'da dukiyar kasuwancin sa da ta siyasar sa waje guda ba, haka ma dukiyar da yasan ba ta hanyan halal ya same ta ba baya shigar da shi cikin kundin dukiyoyin sa, daban yake ajiyar su..kamar dai yadda Hafeez ya sanar da shi.
Anan ne ma Adam ya fahimci cewa already 'Dan Maliki ya riga ya canza sunayen kan komai daya dangancesa izuwa ga shi Adam 'din yayi mamaki kwarai da dagaske.

Duk da tunanin sa zai kula masa da komai ne kafin lokacin da Allah zai yi fitowar sa daga gidan maza amma shi 'Dan Maliki da alamu ba 'kudurin sa kenan ba, sa hannun Adam kawai ya rage a duk tarin takaddun dake hannun Lauyan Alhajin shikenan komai ya sauya..daga ranar da 'dora hannun sa kan takaddun da sunan signing daga lokacin ya tashi daga Adam ya koma attajiri Adam.

Haka ya bi duk ya sa hannu, yana jin wani iri, something that bai ta6a zaton faruwar sa ba yau shi yake faruwa da shi, transfering all the assets of that Famous Politician former senate Jibrin Adam 'Dan- Maliki izuwa ga shi 'Dan bunburutu mai aiki a fuel station...abin akwai ta6a zuciya sosai.

Basu rabu da Lauya ba kusan sati suna abu 'daya yana nuna masa komai da ya danganci takardun, sati gudan nan kaf Adam bai samu ya nutsu ba sam bai zauna ba, tun yana danne gajiya da jin haushin abubuwa cikin ransa 'karshe har ya fara ba'kin rai yana ciccin magani.

Sai da suka kammala komai kafin shi da Lauyan suka koma wajen 'Dan Maliki inda ya kama sati uku kenan bayan waccen ziyarar da suka je da Hafeez.

Da wannan damar Alhaji yayi amfani ya sake yi masa bayanin komai, duk da yake zuwa wannan lokacin jikin Alhajin sai a hankali amma yana kokarin dannewa kar su fahimci baya jin dadi, hawan jini da Diabetes 'din sa suka motsa lokaci guda.

Shi ya sake yiwa Adam bayanin asalin waye shi da kauyen su dake can jihar yobe 'kar'kashin 'karamar hukumar Gujba mai suna _Katarko_ mafiya yawan al'ummar garin fulani ne, sai tsirarun wasu kabilun daban amma Fulanin sun rinjayi garin kamar dai yadda 'Dan Maliki ma ya kasance bafulatanin usul shima.

Duk bayanin da yake Adam duk bai tanka masa ba, Lauya ka'dai ke 'dan rubuce rubuce yana 'dan tanka maganar Alhajin, yayin da Adam ya tsurawa 'Dan Malikin idanu har sai da ya fara tsarguwa da kallon amma bai tanka ba...ya cigaba da bayanan sa.

Sai daya kai aya yana jira Adam yace wani abu kafin amma yaji Adam shiru.

Dukkan su duban su suka mayar gareshi...amma abinda ya fito bakin sa sai ya basu mamaki, domin ba amsar da suke son ji bace daga bakin sa.

" Abbah baka da lafia sosai shine kake 6oyewa ko?"
Idanu ya fitar da zummar karyata batun da Adam yazo da shi din amma bai.saurare shi ba.
" Sun kaika asbiti ne ko kuwa kawai magani suke baka anan?"
Shiru Lauya yayi yana duban Alhajin shi kansa ya fahimci ba lafia yake ba karfin hali ce kawai yake sashi dannewa.
Yayin da 'Dan Maliki ya zaro idanu baki.ya bude zai ce wani abu sai kuma take tari ya sarke shi tankar dama jira yake ayi maganar, masu tsaron sa ne suka yo kanshi da sauri suna tambayar lafia, Adam ne yayi musu bayanin cewa baya da lafiya ne sukai shi asbiti ko kuma su basu shi zasu kaisa.

Basu yadda su bashi Alhajin ba amma cikin 'kalilan 'din lokaci angama shirya komai na tafiya asbitin, dan ciwon Alhajin kamar dama jira yake lokaci guda duk ya galabaitar da shi.

Can babban asbitin gwabnati dake jihar aka kaisa bayan 'yan gwaje gwaje dole aka bashi gado, 'daki na mussaman suka kaishi inda suka 'daure hannun sa da handcuffs suka ha'da da karfen jikin gadon banda tsaro da suka sanya a kowani kusurwa dake asbitin gaba da bayan 'dakin da yake duk jami'an tsaro ne ke gadin shige da fice.

Duk yadda Adam yaso a barshi ganin sa hanawa sukai, dole ya hakura ya koma gida har sai an koma da shi prison kafin zasu iya ganin sa.
_Sai dai muce fatan samun lafia Alhaji Jibrin 'Dan Maliki._

Hankalin Adam ba 'karamin tashi yayi ba da ciwon Abban nasa, gaba daya yaji ma komai ya fice masa aka, duk wani zumudin sa da son ganin dangin sa da yake duk yaji sun gushe lokaci guda, mahaifi ba wasa bane yanzu ya sake tabbatarwa zuciyar sa, yanzu ya sake tabbatar da irin 'kaunar da yake wa Abban nasa.

Duk da ba'a bari ya isa wajen sa har ya gansa amma hakan bai sa ya gaji da zuwa asbitin ba ko daidai da rana guda ba, kusan kullum anan yake yini, kwanan sa biyar a asbitin sannan aka sallamo shi suka koma koma da shi prison anan Adam ya samu damar ganin shi, sosai jikin sa yayi sanyi, duk 'Dan Maliki ya canza masa rama sosai yayi ko wani jijiya dake karkashin.fatar sa ta bayyana kanta a fili.

Gam ya rike hannun Adam cikin nasa sai wasu kalamai yake faman jera masa kamar ba cikin hayyacin sa yake ba.

Adam kasa jurewa yayi saida yayi 'kwalla sbd tsananin tausayin halin da mahaifin nasa yake ciki.

Daren ranar bai iya ya yi.m baccin kirki ba, duk ya karar da daren wajen nemawa mahaifin sa sassauci wurin mahalicci, yana nema masa gafara da fatan samun sauki, ya kuma yiwa mahaifiyar sa ma addu'ar dacewa da Rahamar Allah.
Chapter 57 · 0% Book details