← Book details Binteee Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 218

Sashe 71

Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Hannun sa ta kamo ta ri'ke cikin nata sannan da sanyin murya tace" Haba Rayyan yanzu akan hakan shine ka wani damu kanka?"
" Dole in damu Ammi..a yanzu ke ka'dai nake da shi, ke ka'dai ce zan gani in ji da'di cikin zuciya ta kece ka'dai sanyin raina Ammi taya bazan damu da yanda kike nuna halin ko in kula agare ni ba".
Idanu ta 'dan zaro tana duban sa tace" Rayyan...yanzu har wannan maganar ta kai ka ce ni ina nuna halin ko'in kula agare ka, idan ban kula da ku ba wa zan kula da shi Rayyan..
?"
" Nace aikin nan ma ki barshi Ammi kin 'ki ji na, kullum gani nake tamkar dukiya ta ta gaza 'dauke dukkan 'dawainiyar kine Ammi yasa kike aikin nan....."
" Koka'dan ba dan ku'di nake aikin ba Rayyan...nasha fada mk hakan ko...?"
" Toh ki barshi Ammi...dan Allah..ki zauna waje guda, ki zauna damu...".
Don son kawar da wancan batun sai tayi saurin fa'din" Ba wannan ba yanzu..'dazun fa asbiti muka je da Zaitun yarinyar ta ba lafiya amma meyasa baku lura ba har abin ya shiga jikin yarinyar haka...?"

Rai ya ha'de sosai yana kawar da kai yace" Bata fa'da ba ai shiyasa..."
" Ta bani tausayi wallahi, an ma 'daura mata drip zuwa anjima ka'dan dan Allah kaje ka taho min da su gida".

Ha'de rai yayi sosai bai ce da ita komai ba...tasan kuma ba zai ce 'din ba domin an ta6o 6angaren da baya so ne amma tasan koma me tace da shi Rayyan baya ta6a yi mata musu dan haka bata wani 'daga hankalin ta ba tasan for sure zai je shi.

Shiru ya 'dan biyo sai itace ta sake tambayar sa Amrah fa? Ya take da jikin ta"
Kai ya girgiza mata sannan yace" Tana gidan su tuntuni tace tana bukatar hutu ne kuma a gida..".
" Amma dai ba wata matsala dai ko..".
" Babu komai Ammi in akwai zata sanar da ni..".

Idanun sa ya maida ya lumshe yana tunanin hanyar da ya kamata ya bi domin raba Ammin sa da wa'dannan halittun..sun dame shi sun takura shi..sam baya son ganin su yanzu, barin ma yarinyar da kullum ya ganta sai yaji bugun zuciya sam ya rasa dalili sai dai yasan hakan baya rasa nasaba da tsanar da yy mata ne tun lokacin da ya fahimci 'dakin Safaa 'din sa aka saukar da ita sannan kuma ya fahimci ga ta hanyar da aka samu yarinyar.

'Karfe hu'du da mintina arba'in ya bar wajen Ammi, bai ce da ita 'kala ba haka itama bata sake tuna masa batun zuwa asbitin ba kawai ta bishi da murmushi cikin zuciyar ta take yi masa kyakkyawar addu'ah...kaf cikin yaranta tafi 'kaunar Rayyan tana kuma 'kaunar farin cikin sa...sosai ta zurfafa tunani bayan fitar sa har zuwa lokacin da 'karan wayar ta ya katse mata tunanin.

Idanun ta ta sau'ke kan fuskar wayar gami da sakin ajiyan numfashi..
Recieve taja gami da sada wayar da kunnan ta.
Daga 'dayan 6angaren yace" Ammi sunan asbitin..?"
Saurin sanar da shi tayi hadda room no.
Sai dai har a lokacin shake taji muryar sa ba kamar yadda ta saba ba.

Salmerh😘
[2/10/2022, 11:28 am] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕
*( 'Yata ce)*

Wattpad@
Serlmerh-md

🅿️ *...44*

.......Marwa da driver ya tafi 'daukowa a Zaria da har yasa Ammi tura Rayyan dauko Zaituna hispital tuni sun dawo gida, ko lokacin da Zaitun ta samu labarin dawowar Marwa ba 'karamin farin ciki tayi ba, ko ba komai Marwa mai kaunar ta ce kuma dole ta kaunace ta itama.

Bazata manta yadda suka sha dramma da Rayyan ba kan dauko su daga asbitin dan cewa bazata biyo sa ba dakanta zata iya komawa gida, ma'aikaciyar da ke tare da su tana ta mamakin kalaman Zaitun har tana dan tausan ta da bata baki dan duk zaton ta iyalansa ne din musamman idan ta dubi 'yar kama dake tsakanin sa da Mufee amma Zaitun sam fuskar ta babu sauki.

Fushi yayi ya fice da nufin yin tafiyar sa ya barta amma tuno cewa Ammi ce ta saka shi ya sanya shi kasa tafiya cikin motar sa ya koma ya zauna yana maida numfashin takaici.

Bayan fitar sa ne ma'aikaciyar ta cigaba da tausan Zaitun tana nuna mata rashin dacewar taurin kai wa miji anan ne Zaitun ta fahimci me wannan ma'aikaciyar ke nufi a zabure ta mike tana zaro idanuwa.

" Bafa komin sa bane mu ki rufa mana asiri dan Allah...ba matar sa bace ni..".
Cike da mamaki ma'aikaciyar nan ke duban Zaitun.
Sai kuma a hankali ta sauke idanun ta kan Mufee da ke kwance kan gadon asbitin fuskar ta da alamun tambaya.
Sai kuma ta 'kara duban fuskar Zaitun.
Tana so tayi tambaya amma sai ta ma rasa mai zata ce da Zaitun din.
Cikin.zuciyar ta ta gama yanke cewa toh indai dagaske ita ba matar sa bace toh yarinyar nan fa..bata yadda za'a yi ace wannan gayen bai ha'da jini da yarinyar nan ba.."
Ita kanta Zaitun ganin irin duban da ma'aikaciyar nan ke yiwa Mufee ya sa jikin ta yin sanyi.
Ashe ba ita kadai bace ke ganin wannan abin, ashe ba ita kadai ke ganin 'yar kama tsakanin iyalan Ammi da Mufeen ta ba, musamman ma Rayyan da Raihana da Marwa ta ta6a nuna mata pic din ta cikin waya.

Kafin suyi wani yunkuri sai gani sukayi an sake turo kofan, bai yi wata wata ba kawai da shigowar sa direct ga Mufee ya isa ya sa hannu ya dauke ta ya rungume a kirjin sa yayi waje da ita.

Sam baya ta6a shayin daukan yarunyar sbd koda wani lokaci jikinta tsabtace yake sannan yakanji nutsuwa a zuciyar sa matukar ya kasance tare da yarinyar waje guda, rashin sanin takamamme abinda ke sashi hakan yake sashi birkicewa da san neman dalili har hakan ke sashi ya hantare ta a lokuta da dama.

Kafin Zaitun tayi wani yunkuri sai gani tayi ya fice mata da yarinya batare da ya tanka ta ba, da gudu ta bishi abaya, shima da gangan ya yanke wannan wannan shawarar dan ya riga yasan lagon ta tun da jimawa.

Sauran tarkacen su ma sai ma'aikaciyar nan ta biyo su da shi abaya tana murmushi da ganin wannan dramma ta su. Duk da bata san tsakanin su ba amma sosai taji sun matu'kar birgeta.

Da zuwa mota ya shige da Mufee ya gyara zama, ya rufe motar yana shirin tadawa Zaitun ta karaso da gudu tana huci ta bude motan ta shige itama tana masa duban tuhuma amma bata iya tayi magana ba.

Mika mata yarinyar yayi fuskar sa babu yabo babu fallasa.
Daria ke cin sa ta ciki yadda yaga tayi zuru zuru amma bashi da hujjan darawa agaban Zaitun dan babu hakan tsakanin su sam.

" Rike abarki ba cinye ta zanyi ba malama...".
Da sauri ta kar6e ta tana gyara mata kwanciya ajikin ta zuwa lokacin jikin nata da sauki sosai.
yYana shirin tada motar ma'aikaciyar nan ta iso da dan sassarfa...ta mika masa kayan su tana fadin.
" Haba Daddy, haka ake yi? da ga dauko 'diyar ka shikenan sai a manta da uwa da kuma kayan amfani...?".
Hannu yasa ya amshi kayan yana fa'din " Thanks" da 'yar murmushi saman fuskar sa ganin kamar bazai kara fadin komai bane ya sanya ta maida duban ta ga Zaitun ta cigaba.." Toh Madam Allah ya 'kara afuwa ya kuma tsare na gaba..".
Da kai Zaitun ta bata amsa tana daga mata hannu.

Har suka iso gida babu wanda ya jara tankawa kowa..daga compound kuma suka rabu kowa yayi hanyar sa.

Bayan kwana biyu da dawowar Amrah sannan ta shigo gidan Ammi.
Ta jima tare da Ammi kafin suka samu zama da Zaitun dan yi mata ya jikin Mufee da yake Ammi ta sanar da ita.

Zaune a 'dakin Zaitun suke da Marwa suna 'yar hira, Marwa ke fadin" Gani nayi duk kin rame ga Mufeeda ma ba kamar yadda na santa ba duk tayi sanyi ashe rashin lafiya kuka yi..Ammi ke sanar dani wlh dazun" .
" Mufee tayi dai amma ni lafiya ta kalau..".
" Nima Ammi bata ce min da ke ba amma yadda na gankin tuni na karyata zuciyata...har ma fa kinfi yarinyar lalacewa".
'Yar daria Zaitun tayi tana sunkuyar da kai.
Tasan rama dole ce dan yadda nutsuwa taso barinta da jinyar Mufeedan amma ita bata san ramar tata har ta kai wani matsayi da wani daban ma zai gane ba.
Chapter 71 · 0% Book details