← Book details Binteee Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 128 OF 218

Sashe 128

Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ni kam Mamaki sosai Amrah ke bani, mamakin yadda koka'dan ba ta jin kunyar abinda take yi, bata san sai yaushe zata canza ba, mutum gaban iyayen sa ki ringa nuna halin ko in kula da lafiyar sa har haka..ko albarkacin rashin lafiyar ta sama ai sai yaci.

Tasan kawai haushi ke cinta haushin kuma bana komai bane face na wai an masa aure da ita, auren da ita kanta tasan ba zuwa ko'ina zai yi ba, auren da shi da babu duk 'daya ne duk 'din su sun sani....toh in kuwa haka ne menene abin damuwa kuma...

Duk da yake har ga Allah bansan yadda ake zama da miji ba amma nasan yanayin zaman Amrah da majinyacin mijin ta akwai matsala aciki...sam ba bisa tsari abubuwa ke tafia ba, Amrah sam damu da shi ba...ni kuwa da kullum nake ji na tamkar matafiya me ze sa in saki jiki ko kuma a damu da wanzuwa ta.

A hakan ma Amrah ta 'dan rage zafin kishin ta ne ganin Zaitoon bata ta6a nuna mata cewar dai- dai suke yanzu ba, aikin da take mata ada da tana matsayin 'yar aikin ta bata canza ko guda ba.

Haka ta ha'do mata Tea ta kawo mata Amrah ta kar6a idanun ta na kan T.V..ganin Zaitoon zata koma 'daki ya sanya ta fa'din.." Yau 'din kuma ni kike so in gyara masa 'dakin ne ko me..?"
" Na riga na yi ai".
Shine amsar da ta bata atakaice batare da ta waigo ba, itama bata damu ba dan idanun ta na kan T.V ne.

Anty Madeena da Anty Raihana sosai suka garga'de ta akan yiwa Amrah hidima dan acewar su matsayi 'daya suke da ita a yanzu agidan cikin abubuwa da dama kuwa ta kan fahimci abinda suka fa'da 'din shi suke nufi sai dai ita sam bazata iya ba, har kullum bata ganin sauyawar matsayin ta da na baya a gidan, shiyasa tace baza ta iya daina yiwa Amrah hidima ba kamar yadda bazata daina yiwa kanta kallon ma'aikaciya a gidan ba, abu guda ne baza ta 'dauka ba shine rainin hankali da cin fuska...banda su ma Anty da wata magana ita yaushe a ina ma ta isa ha'da kanta matsayi da iyalin Rayyan.

*****
A 6angaren Rayyan kuwa 'kar'kashin pillow ya cusa magungunan da ya kar6a a hannun Zaitoon, yasan basu ha'da ala'ka da shi ta ko wacce siga ba, yasan ba maganin.da zasu amfani lafiyar sa bane sai dai su kassara shi, dan yasan magani farin sani.

Sun yi magana da Ammin sa duk da shi dai bai bu'di baki ya tanka ta ba amma cikin magananun nata ya fahimci tsananin damuwar da take ciki akan sa.
Baya ga haka ma duba 'daya yayi mata ya fahimci ramar da tayi sbd damuwa.

Sai da ta gama fa'din duk abinda zata fa'da gami da jero masa tambayoyin da zata yi masa 'daya bayan 'daya yana bata amsa da kansa yana jin wani rauni gami da tausayin mahaifiyar tasa na ratsa shi matu'ka.

Tambayoyin duk da tai masa game da lafiyar sa ne, me yake ji meke damun sa a yanzu.
Ta so ta kira Dr Fawwaz ta sanar da shi amma Rayyan ya hana ta.

Tace ta kira masa Sultan nan ma yace a a..'karshe fita tayi zuwa 'dauko maganin sa acewar ta, tana fita kuwa ya tashi ya sake sawa 'kofar key ya wuce bayi da maganin dan sam bai yadda da shi ba...barin ma da tace wai aikowa da shi akayi...bai ta6a zargin kowa kan komai na rayuwar sa kai tsaye ba amma wannan karan tashin farko abinda ya fara zuwa bakin sa shine _SULTAN_, batare da wani dogon nazari ba ya yanke hukuncin Sultan ya kawo shi....

Domin ya fahimci maganin ba daga Ammi bane yazo bata ma san da zaman sa ba, da farko yy tunanin ko ta bayar akawo ne aka canza shi amma dalilin sanar da shi da tayi cewar bari taje ta kawo masa maganin sa har tace mantawa tayi, yasa ya fahimta, ta kuma ce tama 'kira Sultan tace ya sa Marwa ta dubo maganin a 'dakin ta ta kawo su bashi bata san ko sun 'dauko ko kuwa sun manta ba...sunan Sultan da yaji cikin bayanin yasa ya tabbatar da zargin da zuciyar sa keyi akansa.

Cikin sinc ya gwada zuba yawun sa ka'dan sai ya bu'de bakin kwalbar ya 'diga 'daya maganin ciki lokaci 'kan'kani yaga yawun nasa ya tsinke yana komawa kamar ruwa...shi dai haka kawai yaji maganin bai kwanta masa ba dan yasan Ammi bazata ta6a aikowa ta hannun wasu daban ba sa6anin ahalin ta.

Ruwa ya sake ya kora wanda ya zuba 'din sannan ya fito, adana magungunan yayi ta yadda babu wanda zai san inda ya ajiye, sake bu'de 'kofan yayi sannan ya koma ya kwanta kamar yadda kowa yasan yadda yake kwance tun farko.

Addu'ah yake cikin ransa Allah yasa kar yarinyar nan ta fa'da ta ganshi da 'kafafun sa, dan yasan ma'kiyan sa ba ha'kura suka yi ba, tunda a yana kwancen ma ba fasa kawo masa hari suka yi ba, yafi so ya gama tabbatar da zargin sa kafin zartas da hukuncin koma waye ke bibiyar rayuwar sa...dan hk fitar bazata yake so yy ma kowa bayan ya samu 'karfi sosai ajikin sa...Ko Amrah ma ba 'karamin mamakin ta yake ba, domin tun da yafara gane kansa ya fahimci bata damu da shi ba sam, a yini bai fi sau 'daya take zuwa inda yake ba, wataran ma sai dare take zuwa duba shi hakan kuwa bai ta6a damun sa ba illah mamakin ta, ya kan tuno soyayya da 'kaunar da Amrah ke yi masa kafin kwanciyar sa amma yanzu duk babu su.
Hak'ika lafiya ni'ima ce lafiya jarice, duk halin da zaka shiga a duniyan nan idan ka tsinci kanka cikin masu lafiya kawai ka gode masa domin yayi maka baiwa, a hakan ma kwanciyar yayi babu abinda ya illatu a jikin sa illa hannun sa amma Amrah take yin banza da shi.
A hakan fa zaka tarar wasu hankali suka rasa, wasu kafa wasu hannuwan suka rasa, wasu ji wasu gani,.amma shi duk Allah bai raba shi da ko guda ba, ciwom hannun sa kuma yasan da zarar an gyara shikenan...toh miye dalilin Amrah na guje masa...illa wannan yarinyar da kullum bata gajia da shigowa hidima da shi.

Abinda ya lura ma har abinda bai dace ita tai masa bama ita a wurin, sosai abin ke 'daure masa kai, yakan kuma yawaita tuno masa da marigayiyar matar sa dan halin su da bambamci sosai da Amrah yasan da itace ba haka zata watsar da shi ba ga wata 'yar aikin ta ba...cikin ransa yai mata Addu'ar samun Rahama wurin mahalicci, ya sa abinda ta haifa suka kuma koma tare da ita ya kasance mai ceton ta ne...yin wannan addu'ar ya tuno masa da Mufeeda, hakan yasa shi dakatawa da addu'ar tasa yayi tsam da ransa...tun tashin sa sai biyu kawai yaga yarinyar, ji yayi tamkar ya tambaya akawo masa ita amma yasan kwatanta yin hakan koda sau guda ne dai dai yake da jefa rayuwar ta cikin ha'dari.

Bayan kwanciyar sa da kusan awa biyu kafin Amrah ta shigo duba shi...ko zama bata yi bama lokacin kuwa bacci ya 'dauke shi me 'dan nawi so bai san da shigowar ta ba.

Ko da Ammi ta dawo bata tashe shi ba, zama tayi tana jiran tashin sa a baccin yayin da zuciyar ta ke cike taf da farin ciki mara misaltuwa.

A haka Zaitoon tazo ta tarar da ita.
Nan ta sake gaida ta, Ammi sosai take yabawa 'ko'karin ta gami da yi mata godiyar kyakkyawan albishirin da tayi mata a yau 'din.
Zaitoon na murmushi tace bakomai Ammi.

Ammi tace yau kam kije ki huta wa ranki kema zan taya ki aikin kinji.
Zaitoon tace" a a Ammi zanyi...ai aiki na ne..."

Maganganun sun ne ya tada Rayyan a bacci ya kuwa zuba musu idanu yana kallon su gami da sauraran su.

Zaitoon ce ka'dai ta lura da tashin sa domin sau biyu suna ha'de idanu Ammi ce dai bata lura ba, so ganin tashin nasa ne ya 'kara mata 'kwarin gwiwar barin dakin.

Har ta 'karasa ficewa kuwa Rayyan bai motsa ba, sai bayan fitar sa ne da Ammi ta dawo da duban ta gare shi sannan ta ga yana kallon ta.

" A a ashe ma ka tashi...sannu babana...zaka iya tashi ka zauna ne ko kuwa kwanciyar yafi maka...?"
Tayi maganar gami da mi'kewa tsaye da niyyar tallafa masa.

Bai tankata ba, dan bai san meyasa tun tashin sa yake jin harshen sa nayi masa nawi wajen furta kalmomi ba.
Duk da hakan abinda ke mai kai kawo a zuci yake son fa'di a bayyane, so yake ya tambayi Ammi wani abu dake kulle masa tunani.
" Ya jikin naka...?"
Ammi ta tambaya di kulawa fuskar ta da annuri cikakke.

Da kai ya bata amsa.
Ammi ta ta6a jikin sa da wuyan sa, hannun sa da ta lura alamun baya motsa shi har yanzun bayan uban 'dauri da akai masa tun ranar farko...aka kuma yi tunanin ya ha'de aka kwance shi bai fi kwanaki goma baya ba.

Hannun ta kamo a hankali ta 'dago ya rintse idanu gami da cije bakin sa yace.." Wash Ammi...".
Tace" Har yanzu yana ciwo ne...?"
Kai ya 'dage mata sama...alamar erh.
tace " Ikon Allah...sannu, bari Fawwaz ya iso asan me za'a yi, ko kuwa dai asbitin zamu je kawai mu same shi..dama kasan dole a koma ai for check up.
" a a Ammi..."!
Ya bata amsa cikin sauri.
Duban fuskar sa tayi da alamun tambaya.
Sai ya wani yatsine fuska yana komawa baya ya kishingi'da yana gyara zaman hannun sa mai ciwon da hannun sa na hagu saman jikin sa.

" Alhamdulilla jiki na da sauki sosai bana jin komai yanzu sai ciwon jiki..shima with time zai warware.."
" Amma kasan dole ne sai an maka check up 'din ai ko...?"
" Za'a yi daga baya Ammi.."
Chapter 128 · 0% Book details