Sashe 84
Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ganin tayi baccin ne yasa Zaitun mi'kewa ta 'dauke ta abayan Marwa gami da kwantar da ita sannan ta koma gurbin da ta taso.
Yayin da Marwa ta cigaba da raira kukan ta cike jimamin mahaifin su, hakika mutuwar iyaye ba 'karamin ta6a zuciya yake ba, kasa ma magana tayi illah kukan, Zaitoon ma hawayen take tana mai tausayawa halin da Marwa ta shiga.
*****
Watannin Rayyan shida ne kacal da fara aikin likitancin sa kaddaran nan ta fa'dawa mahaifin su, Rayyan dake rungume da shi idanu ya tsura masa, sam ya kasa tantance abinda ke faruwa.
Sai da likitoci suka yi aikin su dan shi kasawa yayi nan suka tabbatar da cewa Alhajin baya tare da numfashin sa.
" Irin kukan da Yah Rayyan yayi bazan iya misalta miki shi ba kada ma Safaa taji labari, Sultan kuka kai subhanallah abin babu da'di gaskia...Allah ya ji'kan Abban mu...wlh Zaitun mun yi rashi sosai cikin rayuwar mu da bana jin zamu sake makamancin sa a duniyan nan".
" Yah Rayyan yafi kowa shiga ru'dani domin kaf ya ajiye duk wani mazantakar sa ya bu'de zuciyar sa yasha kuka da rashin mahaifin sa.
Tun a lokacin ya qalubalanci aikin sa na likitanci sbd a ganin sa bashi da wani amfani tunda har bai iya ya ceci ran mahaifin sa ba.
Babu yadda Ammi batayi da shi kan hakan ba amma yaki amincewa, duk yadda ta so fahimtar da shi 'kaddara da kuma 'karar kwana, tace lokacin mahaifin sa ne ya riga yy bawai gazawar sa ba amma Yah Rayyan kasa fahimtar ta yy, 'karshe kauracewa tsaddaden asbitin da yake aiki yy, har bayan rasuwar mahaifin mu da kusan watanni biyu bai je aiki ba.
Ammi da kanta daga baya tazo ta fahimci bawai kaddarar bace bae yadda da ita ba kawai dai aikin ne ya fice masa aka bugu da 'kari dama ba wai ra'ayin sa bane aikin duk da hakan bata gajiya da nasiha da nusashshemu akan rayuwa, tsoron Allah da kuma kyautata mu'amalar mu.
Unfortunately kuma sai Yah Kabeer yazo masa da wani batu, domin shi ya fara gano wani boyayyen sirri game da mutuwar Abban mu, abin kamar shiryayyan al'amari ne ba haka kawai ya afku ba, sai da suka zurfafa sosai sannan suka fahimci tun da da'dewa akwai abinda mahaifin mu ke kokarin 6oye musu, sai dai duk iya binciken su sun kasa gano asalin menene kuma suwaye makasan mahaifin namu.
Ranar Yah Sultan ya sha kuka, kuka fa ba kuka irin wanda ake yi na zahiri ba, kuka ne yy kamar ransa zai fita, kukan zuci mai sanya karaya da nakasta kwarin gwiwa, ya kuma yi da hawayen sa hatta wanda bai sanshi ba idan ya dube shi zai fuskanci yana cikin halin tsananin 'kunci.
Wannan lamarin shi ya sake wargaza natsuwar Yah Rayyan da ma sauran.
Babban damuwan su shine basu san ta inda zasu fuskanci lamarin ba...Sultan baiyi 'kasa agwiwa ba wurin bayyana abinda ya fuskanta ga Ammin mu duk da kuwa ba komai ne ya sani ba shima din suna dan 6oye masa wasu abubuwan, ita kam bata wani yi mamaki ba, domin ta jima da sanin akwai wani sirri da Abban mu ya jima yana 6oye musu wanda su basu san menene shi ba, tasha kama shi yana wayar sirri wanda galibi da ya ji motsin ta yake zabura ya kashe wayar, sau da dama tana kama shi cikin yanayi na damuwa, tagumi da kuma hawaye wasu lokutan, amma Abban mu bai ta6a bu'dan baki ya sanar da ita komai ba, 'karshe shawara ta bashi akan ya kai lamarin sa wurin ubangiji, tunda daga ranar bai 'kara 6ata daren sa yana bacci ba, zai yi sallah, ya 'daga hannu sama yana addu'ah yana hawaye, Ammi sosai take tausaya masa hakan yasa itama ta daina bacci, kullum takan taya shi raya daren sa wurin kaiwa kukan su ga mahallici, duk da bata san meke faruwa ba amma tasan zahiri akwai abinda ke damun sa kuma shi Allah maji ro'ko ne....abinda ka'dai zata iya tuna yana yawan ambata shine yarana, Yah Allah ka tsare min yara na, Aseeyah dan Allah ko bana raye ki kula min da yara na...."
'Karan wayar Marwa shi ya katse ta daga labarin da take bawa Zaitoon inda duk 'din su ga wayar suka kai duban su.
Ganin cewa Ammi ce kiran yasa Marwa saurin 'dagawa.
Dawowar ta kawai ta sanar da Marwa ta katse watar dama abinda ya sa ta kiran kenan.
Batare da 6ata wani dogon lokaci ba Marwa ta mike musamman ma yadda tajiyo muryar Ammi wani iri.
Tana nufar kofa take sanar da Zaitoon cewa ina zuwa Ammi har ta iso gida.
Masha Allah kawai Zaitoon tace batare da tayi niyyar mikewa, domin a irin wannan lokacin bata cusa kanta inda suke, zata je yiwa Ammin barka da isowa amma sai ta dan huta tukunna zuwa anjima kadan sai taje...hakan ne yasa ko yun'kurin bin bayan Marwa batayi ba.
" Ammi barka da isowa..."
Marwa ta fada gami da zama gefen Ammin.
Bayan gaisuwa da shiga tsakanin su abu na gaba da Ammi ta furta shine 'kira min wayar yayan ku ina kiran sa baya tafiya tun 'dazun.
" Ai kuwa haka Yah Sultan ma yace layukan sa duk basu tafiya...amma bari in dauko wayar mu gwada muyi comfirming..".
Ko da koma 'dakin ta dan 'dauko wayar bata tara da Zaitoon ba hatta Mufee da tasan bacci take ma Zaitoon.bata barta ba 'daukan abinta tayi suka koma 'dakin su.
Batare da wani dogon tunani ba Marwa ta 'dau wayar ta koma ga Ammi.
Koda suka kira din kuwa still numbers din sa basu tafiya.
Hankalin ta ba 'karamin tasho yayi ba.
Ga Landline ta koma ta kira numbern office 'din sa direct nan ma ba'a 'daga ba, ta kira kusan sau uku sannan aka sanar da ita baya kusa tambaya tayi amma yana lafiya akace mata erh.
Tace dan Allah anemo mata shi yanzun nan tana son magana da shi.
Tsawon mintina talatin taji shiru kawai sai securities 'din sa suka zo ranta, take ta lalubo Huzaifa a waya abin takaici wai ai shima kwata- kwata yau 'din basu ma hadu ba bai fito aiki ba...bacin duk karshen wata ko kwana guda ba'a 'karawa ake biyan su albashin su.
Umarmi ta bashi ma duk inda yake yazo gida ya dauki mota ya je office din su Rayyan ya dauko shi zuwa gida ko kuma daga can inda yaken ya wuce sai su dawo tare.
_( ~Mu dai babu ruwan mu, Ko Marwa bata cigaba da bamu labarin ba zamu binciko da kanmu mu cigaba....~ 🤪)_
*A cigaba da gashi....* 👇🫶
Salmerh 😘
[16/10/2022, 9:06 am] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕
*( 'Yata ce)*
*Wattpad@*
_Serlmerh-md_
🅿️ *...52*
_.......Cigaban labarin._
Abban su na da zurfin ciki, taurin kai da kuma kafiya akan abu shiyasa itama Ammi bata tsanantawa kan tambayar sa abu domin tasan in ba niyya yayi ba he won't tell her anything.
Abinda kawai bata sani ba shine takamammen dalilin da ya sa aka kashe shi, wannan kuwa bata 'dorawa kowa laifi ba...amma batun da Sultan yazo mata da shi ya matu'kar jijjiga ta ashe da dagaske akwai abinda Alhaji ke 6oye mata ba hasashen ta bane kawai ba.
Sai gashi Sultan ya fara bincikowa domin haka ya nuna mata tamkar shi kadai yake binciken as in shi yafi damuwa da lamarin Abbah fiye da sauran.
Kai Ammi ta fara juyawa tana kuka sosai, Sultan bai ma san ya bu'de baki cike da mamakin Ammi ba sam bai san yayi hakan ba, cikin ransa ya ayyana shi kam ya gama kuka ai tun daren ranar da ya ci karo da lamarin da yake zaton suke 6oye masa har Ammi, ba 'karamin aiki ke gaban sa ba a halin yanzu bayada lokacin 6atawa wajen kuka.
Duk da ba shi da cikakken labari kan binciken da yayyen nasa ke yi amma dole sai ya san inda suka dosa, shin dagaske binciken suka fara ko kuwa, shin sun samo wata alama ko kuwa, son sanin hakan yasa yazo ga Ammi da tunanin ko zaiji wani abu daga bakin ta, dan shi 6oye masa suke da tunanin shi yaro ne, yayin da shi kuma yake gani kamar suna 6oye masa ne sbd kasancewar sa bare a cikin su.
Kuma ko wayar Abbahn nasu already tana hannun Rayyan ne, duk da Sultan yaso ya riga kowa samun wayar sbd wani dalili nashi amma hakan bai samu gare shi ba.
Shigowar sa kenan ya tadda Sultan da Ammi na tattaunawa a palorn ta dake sama.
Sosai jikin sa yayi sanyi, musamman da ganin yadda hawayen Ammi ke zuba 'kasa abanza.
Nan take jijiyoyin kansa suka fito sosai, sai idanun sa da suka yi ja, a hakan ya zubawa Ammi idanun sa, yana kallon hawayen ta dake 'diga, fatan sa Allah yasa ba gaskiya bane abinda yake zargi, in kuwa hakane yayi al'kawarin koma waye ke da hannu cikin mutuwar mahaifin sa bazai barsa ba.
Da sanyin murya Sultan dake gaban ta yace" Please mana Ammi ki daina kukan haka nan...ni ya kike so inji idan ke da kanki kina shiga irin wannan halin a yanzu..."
Ya 'karashe maganar yana sunkuyar da kansa gami da shafo kan nasa da duk hannayen sa biyu, duba 'daya zaka yi masa ka fahimci cewa yana da babban damuwa a zuciya.
"..Sultan"
Ammi ta 'kira sunan sa cikin tsananin karayar zuciya.
Bai amsa ba illa kai daya 'dago yana duban ta.
"...Dan Allah Sultan yadda ka fara binciko abin nan kai ka'dai ka rufa min asiri ka binne shi kai ka'dai kar 'yan uwan ka suji, Sultan mahaifin ku ya shafe shekaru a 'kalla uku yana jaddada min amanar ku..dan Allah kar ku saka kanku cikin abinda zai zo ya dame mu har in kasa ri'ke amanar da Alhaji ya bar min..."