← Book details Binteee Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 218

Sashe 55

Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ammi tun bata lura ba har tazo ta fahimci Zaitun 'din, ta kuma jinjinawa irin wannan 'kauna, da gangan watarana ta tambaye ta zaryar me take yi sai cewa tayi Mufee na nake dubawa Ammi kar ta tashi bata ganni ba tayi kuka.
Murmushi kawai Ammin tayi mata sannan tace ki kwantar da hankalin ki da ta tashi zan kira ki ba gani nan akusa ba.

Ita kuwa sam hankalin ta bai kwanta ba domin bata manta halin mugunta da son zuciya irin ta mutane ba...akan Mufee sam bata yadda kowa a duniyar nan.

Duk aikin da take yi tana yi ne saboda yarinyar dan bata so taga komai nata yayi 'kasa sam bata damu da kanta ba shiyasa a kullum take jajircewa wurin ganin tayi aiki ta kula da rayuwar 'diyar ta..tasan 'diyarta mai albarka ce shiyasa ma abubuwa da dama ke zuwa musu da sauki.

Wannan dalilin shiyasa Ammi cire ta a aikin kitchen ta maida ita 6angaren ta, dan acewar aikin zai fi mata sauki tunda akwai nawin kulawa da 'diyar ta akanta kar abubuwan su mata yawa zata fi natsuwa idan gyara da sharan 'dakine ka'dai, sai mopping aikin ta.

Itama sosai taji dadi da wannan canjin ta kuma nuna tsantsar farin cikin ta ga Ammi.

Zuwa lokacin tagama fahimtar cewa ba Ammi ka'dai ke zaune cikin gidan ba akwai matar 'dan ta sai dai da yake gidan nada girma yasa tsakanin su akwai tazara sosai, kuma daga nan Ammi ke tura mai aiki can 6angaren kullun safia, kuma ba kowa Ammi ke turawa ba face Raleeya da ta kasance asali dama dan wancan 6angaren aka 'dauke ta.

Komai kuma daya shafi wancan 6angaren a hannun Raleeya yake, hatta da hidimar abincin su.
Kimanin sati biyu kenan amma kwata-kwata sau biyu kacal Zaitun taga matar da ta kasance itace matar 'dan Ammin mai suna Amrah kamar yadda taji Ammi na kiran ta da shi.

Shima zuwan nata ko kyakkyawan kallo bata samu daga wajen ta ba ita har Mufee, bata damu ba kuwa, hakan ma tasan kaddarar haduwar sun dan dai Ammi ta dawo da ita aikin 6angaren ta me baya ga haka da ace a kitchen take aiki inama zata ganta.

Sau biyu tazo 6angaren Ammin cikin kwanaki kusan goma sha biyar duk da yake cewa cikin gida 'daya suke.

Amma koka'dan Ammi bata ta6a complaint ko nuna rashin jin dadin ta game da hakan ba...Ammi macece mai matukar girmama zamantakewa da kyautata mu'amala, babu ruwanta da shiga sabgar da bata sahfe ta ba, abinda yake gaban ta kawai ne bata damuwa da lamarin wani, ga ta kawaici da nuna kauna ga kowa.

Yayin da Amrah ta kasance yarinya ba wata babba ba, dan shekarun ta ashirin ne da uku zuwa da hu'du, sai dai bata da girman jiki, komai nata 'dan daidai ne, ga ta kyakkyawa mai hasken fata.
Amrah 'yar 'kwalisa ta 'karshe ta iya gayu ga ilimi.

Abu 'daya da Zaitun zata ce bai mata ba game da Amrah shine 'dagawa rashin sakewar ta gare su sannan ta fiya zafin kai da raina mutane.

Wannan dalili kuma shi ya rage kaso mafi rinjaye daga dukkan wani kyawun ta da suke gani a zahiri, dole ta 'darsa musu jin haushin ta musamman Raleeya da tafi kowa sanin halin Amrahn ta kuma fi kowa shan hantara da masifa a wajen ta musamman da yake ita ce ke zuwa yi mata komai, ta kan iya sata yin girki sau uku lokaci guda da sunan duk wadanda akayin basu mata ba, ko kuma tace ba yanda take so akayi ba, ita kuma bazata tashi tayi da kanta dan kwanciyar hankalin ta ba.

_Share to other groups..._

_Salmerh_ 😘
[20/9/2022, 9:29 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕
*( 'Yata ce)*

Wattpad@
Serlmerh-md

🅿️ *...34*

.......Satin Adam biyu a asbiti kafin aka sallamo shi, duk ya rame ya zam tamkar ba shi ba, abu 'daya kadaivne bai canza game da shi ba shine gayun sa, shima 'din ba kamar baya ba dan a har yanzun ba cikin natsuwa yake jin kansa sosai ba.

Duk yadda Hafeez da Hajiyar sa suka so ya kara samun nutsuwa ki yayi, Hajiya da kanta tai masa alkawarin nema masa Zaitun ita dai burin ta ya samu natsuwa amma ya kiya.

Adam yasha bakar wahala wajen neman Zaitun amma sam ya gaza cimma burin sa, bai kuma ji ko da wanda ya ganta bane balle lbrn inda suke...sai da Adam ya koma tamkar mahaukaci sbd neman Zaitun amma ya rasa ta, gefe guda ga damuwar abinda mahaifin sa ya aikata ya kasa barin zuciyar sa.

Daga baya ya nemi gidan mahaifiyar Dr Rashed da tunanin ko tana tare dasu amma suka ce basa tare da ita, sun nemi ta biyo su amma taki amincewa hkn kuma basu san ina take ba a halin yanzu.

Da 'kyar Adam ya saduda ganin kamar Zaitun tayi masa nisan zango ne nisan da baya jin zai iya samo ta anan kusa..dole badan yaso ba ya hakura amma bai cire rai da samun ta ba watarana.

Sai da aka sake shafe wasu kwanaki kafin da ban baki Hafeez ya sa shi agaba suka kaiwa Alhaji Jibrin ziyara a prison, a hakan ma da 'kyar aka barsu ganin sa, dan killace yake a wuri na musamman.

Hakika 'dan Adam ba'a bakin komai yake ba, idan kaga yadda 'Dan Maliki duk yayi sanyi bazaka ta6a 'dauka wannan mutumi mai izan nan bane, bazaka zaci cewa wannan mai tunkaho da dukia da karfin mulkin siyasan nan bane wanda jama'a ke matukar martabawa...rayuwa kenan.
" Al..ha...ji"!
Adam ya furta sunan sa a mamakance gami da mi'kewa tsaye ganin cikin 'yan kalilan din satikai gaba 'daya kamanin sa sun sauya zuwa wani daban, zama yayi bisa kujerar da ya mike yana jin idanuwan sa na tara ruwa...Innalillahi wa inna ilaihiraji'un...
Ya furta a fili 'kasa 'kasa yana jin wani abu mai kama da tashin hankali yana shigan sa.

Shi har 'Dan Malikin da ya zaune kujerar dake zaune facing da Adam 'din kasantuwar baya iya jure doguwar tsayuwa a yanzu jiri ke 'diban sa, dukkan su kwalla suke zubdawa, babu wanda ya iya furta komai daga cikin su

Abu guda da yafi damun 'Dan Maliki ya kuma fi tsaye masa a zuciya bakomai bane face tunanin yadda Adam zai kar6i maganar, dama tun ma kafin faruwar lamarin ya riga yayi nadamar komai ya kuma zanta da Hafeez ya sanar masa duk niyyar sa, sai dai bai san ta yadda 'adn nasa zai kar6i zancen bane, tuni kuma ya fara neman gafarar ubangijin sa yana.fatan kuma ya yafe masa duk kuraransa kafin.lokaci ya 'kure masa.

Yasan kuma.wannan duk shirin ubangiji ne, ya riga ya tsara masa sai ya kar6i wani hukunci tun anan dunia kafin haduwar su aganin sa shiyasa har maganar ma ta bayyana bai kuma yi bakin ciki sosai da hakan ba, a iya sanin sa abinda ya shuka ne zai girba amma tunanin sa Adam ne, musamman da yasan cewa yana da ciwo sanadin damuwar sa sai ga wannan kuma...wani hali zai shiga, ya zaiji idan wannan labari ya riske shi...kullun tunanin sa kenan.

A yau kuma da Adam ke zaune gaban sa banda tsananin kunyar sa babu abinda yake masa kai kawo, sosai yake jin babu dadi idan ya tuna makomar da Adam din zai iya fadawa, sai gashi ayau 'din daya gansa ma duban farko ya fahimci Adam din ba karamar wahala yasha ba duba da yadda duk ya rame ya zam sai 'kashi duk wata kumari tasa babu ita...wai sai yaushe ne zai daina azabtar da zuciyar bawan Allahn nan.

'Bangaren Adam kuwa rasa ta inda zai fara ma yayi, bai san me ze ce da mahaifin nasa ba, shin jaje zai masa ko kuma gaisuwa game da faruwar lamarin?, bazai iya ko guda daga ciki ba, gaba 'daya ji yayi komai ya kwance masa, wata zazzafar 'kauna da tausayin mahaifin nasa suka diram masa lokaci guda fin ma kaunar da yake yi masa abaya, meyasa ya za6i wannan hanyar wajen tara dukiyar sa..?
Meyasa bai yi tunanin makomar da hakan zai iya jefa shi ba da duk masoyan sa...?
Sosai yake zubda 'kwalla kansa a kasa, ya ma kasa duban 'Dan Maliki sau biyu tun duban farko da yayi masa bai iya ya 'kara ba, gashi wannan karon Hafeez bai biyo shi sun shigo ciki ba cewa yayi zai jira shi awaje balle ya 'kara masa 'kwarin gwiwa.

'Dan Malikin ne yayi 'karfin halin magana ganin lokacin sa na tafia kamar yadda aka bashi.
'Yar murmushi ya 'ka'kalo wacce ta tsaya masa iya saman fuskar sa, yana duban Adam yace..." wannan karon ma hakuri zan baka 'dana, koda wani lokaci kalmar kenan, sai dai ina fatan ya tsaya hakanan, hakika na kasance mai tsananin san zuciya ta batare da tunanin baya na ba, batare da tunanin me gobe na zai iya haifarwa ba...Na san na sanya zuciyar ka cikin 'kunci duba da yadda naga duk ka rame ba kamar yadda na san ka abaya ba.." Dan Allah kayi hakuri kaji, Hafeez ya sanar da ni komai har da batun rabuwar ka da waccen yarinyar...Zai...Zaitoona ko?...ni kaina banji da'di ba ina kuma ji araina da ina da dama da duk lungun da ta shiga a fadin duniyar nan sai na binciko maka ita, amma ina fatan ni ka'dai 'dinnan na kasance iya mugayen kaddararorin da zazu faru da kai anan dunia, Allah yasa iya 'kuncin da zan sakaka kenan a duniyar nan, Allah yasa sun 'kare kenan.."
" nayi maka alkawarin daga iya abinda ya faru bazaka sake jin wani mummunan abu daga gareni ba har abada 'daana ."

Kai ya girgiza da zummar maida 'kwallar sa amma hakan ya kasa yiyuwa, sosai ya bawa zuciyar sa dakiya wajen ganin sheshshe'kan sa bai bayyana a fili ba gami da rarraba kalaman Mahaifin nasa cikin ransa"...me kuma zan sake gani ya tambayi zuciyar sa aganin sa duk abin da zai sake biyo baya ba zai kai abinda duk ya riga ya faru ba game da mahaifin nasa..."
Cikin zuciyar sa duk yayi wannan tunanin yayin da a fili kuwa bai iya ya furta masa komai ba....
Chapter 55 · 0% Book details