Sashe 3
Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Zama Zaitun tayi itama sannan ta gaida matar dan sakin fuska musamman da ta lura matar kamar bata da matsala ta wajen sakin fuskar ta ga ko wanda ma bata sanshi ba.
" Sai dai ban gane ki ba wallahi.."
Matar ta fada tana 'yar dariya.
Zaituna ma murmushin tayi " Bakuwa ce, amma ta gida...wancan dakin na hanyan waje nake dazun na shigo..."
"...a a Masha Allahu...gaskiya nayi farin ciki sosai kice zan samu abokan hira, gashi kamar ma bayan ki da goyo..."
Takai karshen maganar ne tare da mikewa ta taho ga Zaitun da alamu abinda ke goye abayan Zaitun din take da niyyan karba.
Fahimtar hakan da Zaitun tayi ne ya sanya ta ware goyon ta sauko da ita ta bawa matar idanun ta kur akan yarinyar tana sassanyan murmushi.
"..Tabarakallah masha Allah...ai kuwa ga yarinya...ya sunan ta...?"
Tana duban fuskar yarinyar ta fadi hakan tare da gyara mata rigar jikin ta da duk ya tattare zuwa sama.
"..Aisha sunan ta...."
Cewar Zaitun wanda tun kafin takai ga karshen abinda tayi niyyan fada ta jiyo sallama da hayaniyar raya na tunkaro su.
Gaba daya sai suka kai duban su ga yaran domin hayaniyar tasu ya dauki hankalin su gaba daya.
Da gudu 'daya ya taho ga matar nan yana fadin "Mama!..Mama kinsan abinda Siyama tayi?"
Kai ta girgiza masa alamar a a " Wlh mama gidan su Fatima 'yar ajin su ta shiga wancan na farkon layin wai anjima zasu je Partyn suna dan ance sunan Babyn Mufeeda shine itama wai daga yau sunan Teddyn ta Mufeeda....kuma Mama ba da cewa tayi sunan Teddyn nata Aisha bane..?"
Yayi maganar ne cike da zafin kai tamkar wanda akai masa ba dai dai ba.
Dududu yaron bai wuce shekaru uku zuwa hudu ba sai dayar da ya kira da Siyaman wacce bazata haura biyar ba itama.
Siyaman kuwa hade rai tayi sosai tana duban kanin nata da ke kokarin shigar da gulma ga maman nasu.
" Toh kai ina ruwan ka ne Abdul ai naga Teddyn ba naka bane ko...kuma ma mama ai zan iya kiranta da suna biyu kamar irin nawa ko...?"
" Hakane mama na...daga yau sunan Teddyn ki Aishatul Mufeeda".
Tsalle Siyama ta buga cike da farin ciki take maimaita sunan cike da jin dadi.
Ya isa hakan nan toh...sai kace baku ga bakuwa ba bazaku gaida ta ba"..
Da sauri yaran suka risina suna gaida Zaitun sai taji sun birge ta sosai suka shiga ranta.
Haka ta amsa musu cike da murmushi sannan suka gaida maman sun ma wanda sai a lokacin suka lura da Babyn dake hannun mahaifiyar tasu..atare suka zubar da basket din makarantan dake hannayen su suka nufo jikin ta sosai kowa na fadin abinda yazo bakin sa.
" Laaa mama Babyn waye..?"
"..Mama ki bani na dauka na iya rikewa".
"Kai Siyama me yasa kun cika hayaniya ne da wai? da kyar na samu Ahmad yayi bacci gashi ihun ku zai sa ku tasar min da shi tun yanzu..."
Shiru yaran suka yi suna duban Babyn da ke hannun tan.
" Maza ku wuce ku cire uniform dinnan azo a watsa ruwa aci abinci ayi sallah saura inji wata sabuwar fitinar kuma..."
" Mama idan nayo wankan zaki bani Babyn in rike ko?"
Cewar Siyama cikin marairaita tana daukan baske din ta.
" Wannan kam ai tana nan daga yanzu har sai kin gaji da daukan ta ma maza je a yi wankan a fito tukunna kar ayi lattin Islamiya"
" Toh mama miye sunan ta ?"
Ta sake fada cike da murna jin cewa suna nan.
" Sunan ta daya da Teddyn ki..."!
Farin ciki sosai ya bayyana kan fuskar Siyama har da dan tsallen ta ta shige ciki tana yiwa Abdul albishir din sunan Babyn daya kasance daya ne da Teddyn ta.
Sai a sannan hankalin su ya dawo kan juna
" kai yaran nan ba dai hayaniya ba."
Cewar Maman Abdul tana murmushi.
Zaitun kam mikewa tayi itan ma tana murmushin ta sa hannu ta kar6i Yarinyar ta suka koma nasu dakin.
Zama kawai tayi bisa takalman ta da sune kadai makwafin abin zama a dakin, da hannun ta daya tayi tagumi zuciyar ta cike fal da tunanin ta ina ma zata fara ne...? Lissafin abubuwan da take bukata a yanzu haka tana ganin 6ata lokaci ne, babban damuwar a yanzun shine murdawar yunwa da take ji cikin ta nayi, idan bata manta ba yau din tun safe bata sanya komai acikin nata ba.
" Dole in nemo wani abin yanzu".
Tayi maganar ne gami da mikewa dai dai lokacin da Siyama ta bayyana bakin kofar da 'yar sallaman ta, amsa Zaitun tayi tana bin yarinyar da idanu cike da mamaki ganin ta dauke da flask din abinci.
" Ashe gefen dakin Hajjan mu ma kuke..?"
Siyama ta fada tana me ajiye abinda ke hannun ta.
" Ki bani in dauke ta na iya nima, na iya daukan Teddy na ma har goya ta nake yi a bayana.."
Duk da Zaitun bata san mene Teddy din ba amma tana kyautata zaton Teddyn bai kai darajar yarinyar ta ba..dan haka bazata iya bawa Siyama yarinyar ta dan ta rike ba.
" Ki bari bacci take yi yanzu idan ta tashi sai kizo ki dauke tan ko.."
" Uhum..Maman Mufeeda ai ma zaki goya min ita ko...?"
"Insha Allah"
Ta fada tana kara waro idanun ta kan Siyaman jin sunan da ta kira ta da shi..
" Maman Mufeeda!"..Maman Mufeeda wai!!
Ita din wai..yau din..?"
Lallai..ta fada a fili tana 'yar murmushi.
Har siyama ta juya zata fita Zaituna tayi saurin dakatar da ita da fadin wannan fa .."
" mamana tace in kawo"
"Kai kuma har haka da wahala..bama fa na jin yunwa ki kai muku kawai kuci kinji"
" Ai namu da yawa ne Maman Mufeeda ki ajiye anjima idan kinji yunwa sai kici".
Siyama na kokarin sanya silifas dinta ta tafadi hakan da alamu bata da niyyan komawa dashi.
Wannan yarinya ba dai surutu ba..ta fada cikin ranta a fili kuwa cewa tayi
" Kice angode.."!
Abinda kadai taga zata iya furtawa sannan ta dawo da duban ta kan madaidaicin flask din.
Duk da cewa a yanzun babu wani abinda tafi bukata sama da abincin amma sai taji wani iri cikin zuciyar ta, gani tayi tamkar ta dorawa matar nawi.
Kasa ko bude flask din tayi balle ma akai ga zancen cin abinda ke ciki kawai ta zauna shiru, tana ji cikin ranta dole ta nemo mafita, ita da kanta ta yanke shawarar da taga ya fi mata dan haka ba kuma zata zo ta dora nawin ta akan kowa ba...dole ne tasan abin yi.
Duk da uban yunwan da take ji yake addabar ta kuwa hakan bai sa taji sha'awar cin abincin ba.
Gefe ta ajiye flask din ta cigaba da tunanin abinda yake damin ta arai.
Kokadan bata so tunanin gida yazo ranta, shiyasa da taji kamar kewan gidan zai shigo tunanin sai tai saurin kawar da shi.
'Yar yarinyar dake bacci saman cinyar ta ta tsurawa idanu tana ayyana yawan bacci irin nata kusan koda wani lokaci bacci yarinyar take daga taji cikin ta ya dan dauka shikenan sai bacci, sau da dama ma sai Zaitun ta tashe ta ta kara mata madaran da kanta in bahaka bazata yanke baccin cikin lokaci kalilan ba.
Ta lura yarinyar sam bata da fitina irin wacce yara ke yi din nan.
Jiyo tashin kiran sallah ya sanya ta daidaita zaman kayan sun ta kwantar da yarinyar akai, bakin Pampon da ta ga su Maman Abdul na diban ruwa taje ta dauro alwala itama ta dawo, bata yi mamaki ko jin dar din amfani da famfon ba dan kuwa akwai a masallacin dake can garin su da yawa na alwala da gwabnati tayi musu.
Kayan ta ta janyo bayan ta idar da sallahn ta warware kayan gaba daya. Ragowar kudin da ya rage mata ta ciro ta irga dubu sha daya ne da dari biyar da naira hamsin..idan ta hada da wanda ta kashe tun a gida da na mota da ta biya abincin da ta ci har zuwa kudin hayar da ta biya akalla kudin sun tasamma dubu sittin da 'yan kai.
'Dif taji kirjin ta ya buga lokaci guda...tsoro ne taji ya mamaye ta, sosai ta jinjina yawan kudin da tun farko bata lissafa su ba sai yanzun.
Hakan ma ba dan Ya Bukar da ke dan siya mata wasu abubuwan da kudin sa ba da kila zuwa yanzu ma babu wannan kudin sun kare gaba daya.
" Toh yanzu idan suka kare ya zanyi"?
Wata zuciyar ta ta jefa mata wannan tambayar kuma sosai tambayar tayi tasiri cikin ranta.
Lallai dole ne in nemi mafita ko dan yarinyar nan..yanzu haka kam bata da matsala kan madaran yarinyar dan akwai ragowa me dan dama sosai amma sam bata so ya yanke musu.
Lissafi tayi ta ga cewa cikin kudin zata iya siyan madaran kimanin gongoni uku gudun kar ya kare dacwuri inyaso sauran kudin sai tasan yadda zata yi da shi.
Gashi bata da abinda zata na yiwa yarinyar shinfida dashi illa zanbuwan ta kadai kuma tana gudun sanyi ya kama mata yarinyar.
Aranta ta yanke cewar idan tayi sallah zata koma wajen Maman Abdul ko zata samu inda zata siyawa yarinyar abin shinfida da sauran kudin dake hannun ta.
Sai dai kuma bata so matar taji kamar ta takurata ne da yawa shiyasa ko da ta idar da sallahn kasa komawa tayi.
Abincin ta hanyo da ya kasance jallop ce ta shinkafa, haka ta dan tsatstsakura ta toshe inda take jin yunwar ta mayar ta rufe shi...ita kadai acikin dakin amma jin ta take a tsarke tamkar wacce ke aikata ba dai dai ba.
Bata kuma kara fitowa ba duk da kuwa abubuwa da yawa tana da bukatan su a lokacin.