← Book details Binteee Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 212 OF 218

Sashe 212

Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

" Haba Marwata, haba dan Allah, Haba Auta ta shin so kike ki nunawa Allah cewa baki yadda da 'kaddara ba ko me...?"
Kai ta fara juyawa" Ammi na yadda da kaddara mana, na yadda cewa Komai nufin Allah ne, amma Ammi ni me zanyi da aure yanzu, me na tsinta a cikin sa banda ba'kin ciki, Ammi mijina fa yayi sanadin mutuwan mahaifina, shifa ya raba shi da duniyar baki 'daya, mijina fa Ammi yayi sanadin raba ni da yar uwa ta, babban yayana da duka ahalin sa, haba Ammi, kina nufin duk kin mance? aure ne ya shafe min kaf ilahirin farin cikin rayuwa ta Ammi, wanda a kullum nake kwana in tashi cikin bakin ciki da takaicin sa.

Halittar da a kullum nake ikirarin mijina ne kuma dan uwana shine fa ya haihu da matar Yayana Ammi, dan uwana jinin jiki na...Ammi that same person ya shirya kashe min ragowar ahali na...taya zan mance da duk wannan Ammi...wallahi har zucia ta bana son auren nan yanzu Ammi..dan Allah ku barni inyi tafia ta inda babu wanda ya sanni sai Aunty na ka'dai".

'Kit wayar da ke hannun mufeeda ta tayi karan yankewar 'kira.
Domin tuntuni aka 'kira Mufee ta 'daga Batare da ta san tama yi hakan ba.

Yayin da Marwa ta cigaba da magana" Ammi idan zan 'karashe rayuwa ta a haka nan bazan ta6a sha'awar sake yin wani aure ba duniyar nan. Ji nake ban yadda da kowa ba Ammi, Dan Allah abarni in rayu da 'yan cina, abarni in rayu cikin natsuwa ta da farin cikin da na samu a halin yanzu...".
Ta 'karashe maganar cikin kuka Mai tsananin ban tausayi tana mai zamewa daga jikin Ammi tana kokarin durkushewa bisa gwiwoyin ta.
Da sauri Ammi ta tarota ta rungume ta.
Ita kanta jikin ta yayi sanyi sosai, domin da kanta tasan Marwa tayi hakuri, marwa tayi tawakkali fiye da yadda ta tsammata, Marwa ta kunshe abubuwa masu dama cikin zuciyar da ba kowa ne zai iya hakan ba, duk da depression da ya kusan kama mata yarinya amma she fight this battle, nd she fight it alone batare da kowa ba, tayi yaki da zuciyar ta sosai domin da badan haka ba da yanzu wata maganar ake ba wannan ba.

Mufee ma ganin yadda Auntyn ta ke kuka da gudu ta zo ta rungume 'kafafun ta...tace " Anty"!
Ammi bata 'kara fa'din komai ba illah hakuri kawai da take 'kara bata.

Bata san.ya zata yi ba amma itakanta bata san ana sake tauye Marwa...yarinyar nan ta shiga rudani iri da kala cikin rayuwar ta tun tana yar karama da ita, kama da ga kan rasa 'yar uwar ta Safaa da tayi har zuwa yau din nan bata samu cikakken farin ciki ba.

Cikin rai Ammi ta ayyana dole zata yi magana da Rayyan kan Marwa.
Sai da ta bari Marwa ta natsu sannan tayi mata nasiha sosai.
Kan duk abinda ya samu bawa jarrabawa ce daga ubangijin sa...kuma duk yanayin da kaddara tazo mk dole ne ka amshe shi hk nan kuma da hannu bibbiyu domin shine cikar imanin bawa ga Mahaliccin sa.
Sa6anin hakan idan ka aikata tamkar ka gaza yadda da kaddara ne, dan hk ta kwantar da hankalin ta, kar tace zata biyewa past din ta ta kasa daidaita rayuwar ta ta gaba while tana da daman hk.
Lokuta da dama nadama na zuwa bawa ne bayan lokaci ya kure masa, so kai da ka samu dama kafin kurewar lkc yi kokari ka amfanu da shi...ba duk halittun Allah aka zam 'daya ba, sannan kowani bawa tafe yake da tashi kalan kaddarar inma mai kyau ko akasin hk..tace Marwa ba wai muna tilasta ki kan batun aure bane, kawai munayi ne sbd munsan shine sittirar ki kuma alkhairin rayuwar ki, muna fata ne wannan ya kasance mk na har abada kuma abin alfahari agareki...taushi zuciyar ki akan komai kinji uwata.."!
Sosai Ammi taja hankalin ta har sai da taga ta dan sake kafin ta kyaleta...tace tashi ki shirya ko.

Ko da ta koma dakin ta kuwa Rayyan ta fara 'kira sai dai bai 'daga ba.

Shi kuwa ya na can Office abubuwa sun rinca6e masa, baki 'daya sun sha kansa ko bi takan wayoyin nasa ma bai yi ba.

Haka nan kawai sai yaji yana bukatan makusanci wanda zai riga taya shi wasu abubuwan ko da bai nan, sannan yana bukatan driver again amma har yanzu zuciyar sa ta kasa yin na'am da koma waye.
Shiyasa ya kwammaci ya tuka kansa zuwa duk inda yake so duk da hkn na dan takurashi wasu lokutan.
Amma mutane sun riga sun dasa masa shakkan su cikin ransa..bai ma san ta ina zai fara ba a halin yanzu.

Lokaci guda kawai Bello ya fado ransa, Bello wani matashi da ya gani can cikin 'yan uwan Zaitoon.

Sai da ya tashi a aiki ya bi gidan direct, nan Ammi ke masa maganan tafiyan Marwa yace ai Adam ma ya 'kira sa da yamman ranar, kuma shima duk kan batun ne, abin ya 'kona masa rai matuka, dan zaton sa Marwa ta tilasta shi ya kira ya rokesa kawai dai ya basar ne.

Duk da Ammi bata da tabbaci amma a zahiri tace" anya kuwa..bana jin Marwa zata aikata hkn gaskia?"
Ita dai tana kokonton Marwa ce ta sanya shi. Amma rashin tabbas yasata jan bakin ta tayi shiru.

Toh wayar tata ma tun lokacin data taho da Mufee nan bayan sun lallashi Marwa wayan ke 'dakin Ammi kuma har yanzu gatanan dake tana silent ita dai ko 'karan wayar bata ji ba.
Rayyan yace" Yanzu ina take?"
Tana can 'dakin ta.
" Hmm"
Yace ya cigaba da kallon wayar sa.

Ashe Marwan yake kira, sai kuma yaji bata picking.
Dan 'karamin tsaki yaja mai sauti.
Ammi me yasa bata 'daga waya toh?"
" Wai Marwa kk kira?"
Yace " Yes kuma bata picking call din".
Ya yi maganar fuskar sa 'daure tamau.
" Gafa wayar can saman drawer Mufeeda ta kawo shi nan tun azahar..Sai dai ka 'kira landline".
Umarnin zuwa saman Ammi ya bata kawai ya ajiye kan wayar.
Bata 6ata lokaci ba kuwa sai gata.
Fuskar ta duk ya kumbura haka ma idanun ta...kallo daya zakai mata kasan cewa tayi kuka.

Duk yadda yake jin zafin rai amma duba daya yai mata yaji tausayin ta ya tsirga masa ilahirin jiki da zuci.

Gaban sa ta dur'kushe tace" Ina yini Yaya? Ya aiki"
Cikin sassanyan sautin da ya sakwme karya nasa zucia.

" Alhamdulillah".
Yace ata'kaice.
Ta waiga ga Ammi tace
" Ammi barka da hutawa.."
" Yauwa Marwa".

Bayan shu'dewar wasu 'yan da'kiku
sannan ya 'kira yi sunan ta cikin sanyin sauti yace.
" Marwa"!
Tace " Na'am"
Tana mai sagowa ta dube shi.
" Shine kika ha'da ni da saurayin ki dan kina son kiyi tafia ko?"
Bata san me maganar tasa ke nufi ba dan haka kawai zuba masa idany tayi tana kallon shi.
Ji tayi aranta sam kamar ba da ita yake wannan maganar ba hala yayi batan hanya ce yayi.
Toh ita ina ma taga saurayin balle har ta ha'da su da yayanta.
Ganin yanayin ta ya sa shi fahimtar cewa bata gane kan maganar tasa ba dan haka sai yace..." Adam ya 'kira ni akan dan Allah na baki daman yin tafiyar nan, nasan kuma ke ce kika sanya shi kirana..."
Sai lokacin ma ta tuno da Adam a yau din.
A kuma lokacin ta sake tuno cewa ashe fa har an riga an bashi auren ta lokaci kawai ake jira ya cika.
" Ni kuma Yaya? wlh yau ma duk ban yi waya da shi ba, ni babu abinda nace masa koma ba yau din ba...."
Gauron numfashi ya sauke, yace " Ki shirya, next week zaki wuce kuma 1 Week kadai zaki yi ki dawo in kika wuce haka.. Marwa..."
Ya 'dago ya sanya idanun sa cikin nata yana me bu'de idanun sosai alamun gargadi.
Basai yace komai ba.
Ita kanta tasan me yake nufi dan haka sai tayi 'kasa da nata idanun cikin sauri.
Farin cikin daya tsirga mata a wannan lokacin ya rinjayi komai a wannan da zai zo mata sa6anin sa.
Dan haka take murmushi ya mamayi fuskar ta, ya kuma kore duk wani takaicin dake kunshe cikin zuciyar ta yinin ranar.
With an exitement tace
" Nagode Yayah..Ammi thank u..Allah ya kara girma".

Tana gama fa'din haka ta mi'ke.
Ammi tayi caraf tace" Wayar ki na ciki, Mufee ta taho da shi tun dazun ke kuma baki biyo sahu ba.
Bata yi musu ba ta 'dauko wayan, sai ma yanzu ta tuna da ita baki daya.

Tana shiga dakin ta ta fa'da kan gado ta lumshe idanu.
Ji tayi aranta tana so da bukatar fa'da ma wani ataya ta farin ciki..Safaa da ta fado ranta tayi saurin kawar da tunanin ta domin tasan 6ata mood in ta zatayi nan take..ta riga tasan that soul has gone forever nd she ll never ever come back to her.."

A hankali ta bu'de idanu ta 'dago wayar.
Tarin missedcall 'din da ta gani su suka kusan firgita ta.
Me ya faru Adam yayi min irin wannan missedcall haka ta tambayi kanta.

Ba shi tayi niyyan kira ba amma hka nan kawai ta danna kiran layin nasa dan tsintan zuciyar ta tayi da son jin meke faruwa.

Shiru tayi bayan ya amsa kiran.
Yayin da shi kuma ya saki ajiyan zucia.
A hankali ya kira sunan ta
" Marwa"!
Tace" Na'am".
" Kin tada min hankali yau Marwa"!
" Kayi hakuri".
" kin hana ni sukuni, kinsa na kasa jin farin ciki..wai me ke faruwa ne?"
" Babu komai Yah Adam".
" Marwa"!
Tace " Umm".
" Baki sona ko?"
Tayi shiru.
" Please tell me"
" Ba haka bane".
" me yasa baki 'daga wayata Marwa?...throughout d day kinki picking call dina...why please.."?
Chapter 212 · 0% Book details