← Book details Binteee Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 164 OF 218

Sashe 164

Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Na kan lura da kallon da mutane ke min a hanya ta amma sam kallon bai dame ni ba, abinda suke furtawa biyo bayan kallon shima sam bai bai dame ni ba, in motsa hannu na inji yarinyar na nan tare da ni shine ka'dai buri na, ban sani ba hukunci na kuskure ne ko kuma akan dai- dai nake ba.

Kwance na samu Inna ta tana hutawa, da zuwa na kuwa na dur'kushe bisa gwiwoyi na na ringa mata kuka..bata ce da ni 'kala ba wanda cikkn kukan nake fa'din" Iyami tace bazan zauna mata a gida da yarinyar ba Inna, Innani ni dai ina son ta dan Allah kar ku raba ni da ita..."
Kuka nake sosai, ina jin yadda kaina ke min sara sbd yawan kukan da nayi amma sam ban bi ta kansa ba.

Inna ta ma bata ce da ni uffan ba illah yarinyar da ta amsa daga hannu na amma a yanayin ta na fahimci bata ji dadin maganar ba.

Bari na tayi a 'dakin ta fita ta hura wuta tayi mata wanka, ruwan 'dumin ta bata ta sha take kuwa cikin sa'a sai tayi bacci...sai lokacin Innani ta dawo da ita ta kwantar da ita bisa katifa sannan ta sake fita waje, rigar da ta cirewa yarinyar shi taje ta wanke ta kuma dawowa ta zauna gefe na.
" In kin gama kukan sai kije kiyi wanka kiji da'din jikin ki ke ma, ni kam bansan me zan ce da ke ba yanzu tunda kin riga kin za6awa kanki abinda kikaga yafi maki...amma ki sani duk abinda zai biyo baya ni babu ruwa na, kinga wannan ma somin ta6i ne matukar kk cc ke a kullum sai abinda kk niyya ko ra'ayi zakiyi to kuwa ki shirya tar6ar 'kalubale iri daban daban...".

" Innani ki daina min mugun fata dan Allah..."
Kai ta girgiza sannan tace" Kema kinsan har abada bazan ta6a yi miki mugun fata ba, magana ce dai ta gaskiya nake fada miki, kuma ya zam min dole ne in fada miki 'din tunda a yanzu idanun ki rufe suke, wala alla ko zaku bu'da su ka'dan ki fahimci abinda ake hango mk..."
" Inna..."!
Na fada da niyyar magana sai tayi saurin dakatar da ni da 'daga hannun ta 'daya.

"..Ba maganar ki nake bu'katan ji ba, so nake ki gane ki kuma lura.. tun ba'aje ko'ina ba gidan mahaifin ki na neman yafi 'karfin ki sbd rigimar ki...jiya yaron nan Habu yazo ya same ni kan yadda kuka yi da shi..kan kin 'ki amincewa a maida yarinyar nan..."
Kuka nake sosai sbd ko a maganar Inna ta ma fahimci ita kanta ba so na take da yarinyar ba...duk da hakan sai da naso fahimtar da ita cewa ba bu fa wanda yasan inda dangin ta suke toh in haka ne wajen waye za'a maida ta dan Allah in dai ba salwantar da ita ba....?"
" Sannu mai imani sarkin masu tausayi, yanzu kam za6i ya rage naki ai ni babu abinda zance miki..tunda gashi har kin sa magana ta cika gari ta fannin da ba hakan yake ba, kuma ina tabbatar miki da cewa mawuyaci ne jama'a su fahimce ki kamar yadda kk tunani.....".

Ban sake ce da ita uffan ba haka itama bata bar inda nake ba.

Sai da nayi kuka na na gaji nayi shiru dan kaina kafin Inna ta ta fara lalla6ani...." Ba wai nufi na in raba ki da yarinyar bane so nake ki fahimci kalar gagarumin aikin da zaki kwasowa kanki, kinsani na sani ba gata ne da mu cikin garin nan ba balle muyi tunanin akwai mai tsaya mana..Yayan ki ne ka'dai, kuma yana iya bakin 'ko'karin sa, bai kamata sbd tsananin rigima ki sake kwaso masa wani nauyin na daban ba..."

Cike da shagwa6a gami da son kawar da zancen nace da Innani ni dai yunwa nake ji...".

" Baki 'dauki azumin bane"?
Ta tambaye ni da kulawa tana dubana.

Kaina na girgiza mata gami da fa'din" Ciwon kai da zazza6i ke damu na kuma tun jiya banci abuncin kirki ba..".
" To kije dai kiyi wankan sai ki zo ga can kunu kisha kafin in sama miki wani abin mai kauri ki sanya a cikin naki".

Sai bayan la'asar liss Hamma Bukar yazo gidan har 'yar rama naga yayi saboda tashin hankalin da na santa shi ciki.

Sai da suka gaisa da Innani kafin ya wuto 'daki wuri na inda ya same ni zaune na tasa yarinyar gaba ina kallon ta.

Kaina 'kasa na gaida shi saboda kunyar abinda nake shirin saka shi.
" Ya yarinyar ina fatan tana lafiya..?".
Da" erh "na masa shi ina mai wasa da yatsun hannu na.

Shiru ne ya 'dan biyo baya sannan yayi gyaran murya gami da 'kiran suna na.

Kai na 'daga na 'dan kalle shi sai yace" Sam ni ban so rayuwar ki ta kasance hakan ba 'kanwa ta, kin dai riga da kin san buri na, amma da alamu wannan abinda ya farun duk yana shirin rushe min komai, bazan ta6a jin da'di ace yau bakya gidan mahaifin ki saboda wani dalili na daban ba, amma babu yadda zanyi na riga na sashi a mizanin 'kaddara kuma na amsa fatana Allah ya bamu ikon cinye shi...ni dai duk abinda zan yi ina yin shine ta fannin da nasan bazai cutar da ke ba..saboda farin cikin ki da kwanciyar hankalin ki nake yin wasu abubuwan, haka kuma dalilin kenan da ya sanya ni cewa amaida yarinyar amma kika 'ki amincewa, babu yadda zanyi Zaituna, na barki da ita amma ki san wani abu..'dazun Baffah Liman da kansa yayi min bayanin cewa shi daga yanzu babu wani batun aure tsakanin ki da Baabagana, a fa'dar sa wai bazai ha'da zuri'a da mutane masu biyewa son zuciya ba, kin dai san me hakan ke nufi ko...?"
Shiru nayi masa kaina a 'kasa.
Yayin da ya cigaba
" Ko baki gane yanzu ba nasan wataran zaki fahimta tunda a yanzu kusan duk jama'ar gari irin kallon da suke yiwa al'amrin kenan, bana fatan inga an tozarta min ke amma babu yadda zanyi..buri na kawai kiyi farin ciki kinji.. zan yi magana da Innani ki cigaba da zama anan kafin in shawo kan lamarin acan gida...Allah ya taya ki rainon 'diyar ki ya baki ikon kulawa da ita, haka kike so ince ko...".
Ya 'karashe da sigar zolaya.

Duk da jiki na yayi sanyi 'kalau amma hakan bai sa na kasa murmusawa ba, na sake sunkuyar da kaina.

Kalaman Hamma na sun fi komai sanya ni cikin natsuwa, idan yana fushi ji nake tamkar an tafi min da nawa walwalar ne, yanzu kuwa da na fahimci ya sakko ya kuma yarje min in zauna da yarinyar sai naji natsuwa sosai ya shige ni kamar bani da wata damuwa...abu guda da yafi tsaye min shine kalmar _rigima_ da mahaifiya ta ta furta gare ni, ban tashi sanin da gaske rigimar nayi ba sai lkcn da abubuwa suka kusa tafia min da natsuwa ta.

'Daukan yarinyar Yah Bukar yayi yayi mata addu'a sannan ya ajiye ta ya mi'ke yayi mana sallama ya fita.

Dabino ya bani yace idan ansha ruwa in tauna in bata abaki...da yake bai san cewa bana azmi yau 'din ba.
Da fitar sa ni kuwa na tauna na ringa bata dan dama tausayin ta ya fara kamani tun da mahaifiyar ta ta haife ta ruwan 'dumi kawai ake bata sai ruwan Zam- zam.

Daren ranar ne ma Innani taje ta nemo madarar shanu ta bata tasha ranar kuwa tasha baccin ta sosai bata koyi mutsu-mutsun kirki ba kamar tasan halin da ake ciki.

Innani babu ruwan ta haka zata wanki yarinyar ta kuma wanke mata rigar ta da take sanya mata guda 'daya jal da yake har a lkcn babu wata, idan an cire an wanke sai ya bushe sannan ake sake sanya mata...daga ruwa sai madarar shanu idan an samu an siya ake bata in kuwa ba'a samu ba haka nan take zama da ruwan ka'dai, abin ya fara damu na, in bama ikon Allah ba ai yarinyar ba 'karamin wahala zata sha ba, amma Allah ya yassare min abubuwa da dama, ya kare min ita, ya ciyar min da ita a lkcn da ni kaina ban sani ba, ya kuma wadata da lpy ingantacce har zuwa girman ta.....

Mun shafe kwanaki biyu a gidan Innani amma banga Dijeh ba banga alamar ta ba, haka kuma banga aboki na Ummaru ko sau 'daya balle su Khausar, Goni kam dama tuni ya koma, nasan kuma babu mamaki iyayen su ne suka hana su zuwa inda nake sai dai wani abu da basu sani ba shine ni duk hakan bai dame ni ba in dai zan bu'de idanu inga yarinyar nan kusa dani toh banda damuwar komai.

Salmerh😘
[6/1/2023, 8:07 am] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕
*( 'Yata ce)*

*Wattpad@*
_Serlmerh-md_

🅿️ *...92*

......Tun da handbag in matar ya kasance a wuri na ban ta6a dubawa ba, sai da rashin takamamman abinda yarinyar zata ci ya dame ni kafin na 'dauko jakar na duba da yake ko lokacin da zan tafi gidan Abban mu ban tafi da jakar ba nan na barta gidan inna ta.

Ku'di na gani masu 'dan yawa a ciki, nasan akwai su domin tun a wancan ranar Nadia taso yi min kyautar su amma na'ki amsa.

Sam banji wani iri ba dan ba sune a gaba na ba, damuwa ta kawai yarinyar ne.

Guda biyu na zaro daga ciki 'yan dubu dubu na 'dauki hijabi na na fita wurin salele mai Chemist.

Gaishe ni nayi ya masa da sakin fuska sai nace" Dan Allah ko ana iya samun wani magani da za'a ringa bawa yara matsayin abincin su?"
Ko 'dar ban ji game da yi masa tambayar ba domin nasan ya riga da yasan komai.

'Yar dariya yayi yace" Ya Baby...?"
" Tana nan..."
" Lpy..."
na rarrabe amsar ina mai kawar da kaina daga kallon sa.
Chapter 164 · 0% Book details