← Book details Binteee Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 88 OF 218

Sashe 88

Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Lokacin shan maganin sa na yammaci nayi ya 'dauka ya sha cikin mintina 'kalilan ya fara fita hayyacin sa dan ma matar sa na tare da shi ne a lokacin ita tayi alerting cikin gida aka fara lalu6o Rayyan da shima daiwar sa kenan aiki amma yadda yaga wannasa yas dole sai da aka dangana shi da asbiti.
Anan aka tabbatar musu da cewar guba yasha sai dai ba mai 'karfi sosai bace.
Sultan ne ya aikata amma saboda karfin hali shine yake so ya dangana lamarin da ma'aikatan gidan musamman Hajja Ladi da kwanaki ya koreta.

A wancan lokacin kuwa har Kabeer ya samu sauki suka dawo gida ba'a san wanda ya aikata hkan ba.

Sultan ne ma daga baya ya fara cusa musu tunani da zargin Alhaji Rufa'i da suka yi tafiya zuwa Maiduguri atare, musamman da yaji ya fra batun auren Rayyan kan cewa ya kamata magana ta cigaba a cigaba da yiwa Abbah addu'a kawai.

Duk 'din su sun fara amince wa da zargin Alhaji Rufa'in musamman da Sultan ya fara rattabo musu sabon bayanin da tun bayan rasuwar Abbah babu wanda ya sake bi ta kan sa.
Rashin.ta6a Alhaji Rufa'i da makasan basu yi ba, acewar Sultan yana da tabbacin suman 'karya yayi ma ko a wancan lokacin daga baya ya farfa'do da gangan.
Kuma acewar Sultan in ba shi 'din da suke tare bama waye yasan cewa suna kan hanya a wancan daren tunda iya sune suka yi tafiyar shine kadai bare acikin su.

Sosai ya basu gamsassun shaidu da suka sanya su fara dasa zargi akansa.
Gaba 'daya hankulan su sai ya koma gare shi da bincikar duk wani motsin sa...Kuma hakan bai sanya shamaki garesu wajen son cika burikan su ba.

*****
Batare da shawarar kowa ba Rayyan ya nemi gurbin karatu ya kuma samu a Uk...cikin lokaci 'kankani ya fara shirye- shiryen tafia a 6oye.

Damuwar rashin mahaifin sa gaba 'daya ya 'dauke hankalin sa daga kan kowacce mace ma ciki hadda Nadia, sai dai takan 'kira shi da kanta su gaisa lokaci zuwa lokaci dan shi har mancewa ma yake da ita a rayuwar sa.

Yana cikin shirye- shiryen tafiyar sa ne Alhaji Rufa'i ya samu Ammi da maganar auren su, dan aganin sa alhakin auren yanzu bisa wuyan sa ya rataya tunda da shi aka faro.

Cikin rashin sani bai san cewa duk kallon biri suke yi masa ba idan ka 'dauke Ammi ka'dai.

Ha'kika ba 'karamin so tayi ta manta da zancen auren ba in ba dan Alhaji Rufa'in ya tunasar da ita ba.
Ta kuwa yi masa godia sosai tace zata yi magana da wan sa duk abinda ake ciki zata sanar da shi.

Da 'kyar Ammi ta sashi amincewa da batun auren dan bai so zancen ya taso a wannan ga6ar ba da yake shirte shiryen barin 'kasar.
Ya so ya dakatar da batun sbd wannan dalilin amma Ammi ta dakatar da shi da cewar sai suyi tafiyar su tare tunda ba wai bazai iya 'dakuna nauyin su bane.

Wannan dalilin ya 'kara masa jin haushin Alhaji Rufa'i cikin ransa dama Nadian ita kanta.

Ganin yadda Ammi ta matsa ne yasa ya basu dama, Alhaji Rufa'i abokin mahaifin sa ne sosai kuma ko bayan rasuwar Alhajin basu ka'dai suka shiga tashin hankali ba hadda shi amma duk basu sani ba, shine ya tsaya tsayin daka wajen ganin anyi komai.bisa tsari cikin satikai shida aka 'daura masa aure da Nadia bisa sadakin da bai ma san nawa bane sai a wajen 'daurin aure yaji yawan su.

Dolen sa haka ba dan yaso ba ya tattara Nadia suka tafi tare.

Kabeer ne ya fara dasa ayar tambaya akan Sultan dan haka kawai sai yaji zuciyar sa bata yadda da shi ba, tun bayan bikin Rayyan abubuwa suka 'dan sarara musu har suka tattara suka koma gidan sa wannan karan hadda Safaa suka koma inda ta cigaba da zuwa makarantar ta acan.

Gidan babu kowa yanzu, Ammi ma sun bude wata kungiya a Abuja so ba sosai take samun zama ba, Marwa na school Raihana kuma ta koma gidan mijin ta.

Tuni soyayyar dake tsakanin Sultan da Safaah ta riga ta fito fili, Ammi dai kam tayi na'am da hakan yayin da Kabeer yaji abun mai masa tsari ba, sam bai ga dacewar aure tsakanin Sultan da Safaah ba haka kawai yaji bai amince da ha'din ba ba wai dan yana da wani dalili ba.

Sun zauna da Sultan sunyi magana da yake Sultan nada kaifin 'kwa'kwalwa hakan yasa duk da Kaberr bai fito fili ya bayyana ba amma sosai ya fahimci manufar sa sai dai bai nuna masa ba shima.

Sai dai level 'din haushin Kabeer da ya 'kara hauhawa masa a zuciya.

Ji yake matu'kar aka hana wannan ha'din toh an gama da shi ne a duniyan nan, kenan duk wahalar sa ta tsawon shekaru ya tafi abanza.

Cikin kwanaki biyu rak ya samowa kansa mafita.

Bai yi 'kasa a gwiwa ba ya sake shiri da wani 'karamin kwali ya nufi gidan Kaberr da shi.
Ashe mage ce aciki.
Bayan motar Kabeer yaje ya ajye kwalin sannan ya fita batare da ya 'karasa ciki ba dan ban da mai gadi babu wanda yasan da zuwan sa.

Yana fita ya 'daga wayar sa ya 'kira Kabeer 'din yacevda shi Ammi na neman su gaba 'dayan su wai yanzun nan akwai maganar da take so su tattauna.

Kabeer yayi 'ko'kari wajen ganin ya 'kira Ammi domin ya tabbatar amma wayar Ammin na shiga ba'a 'dagawa, ashe already wayar na tare da Sultan ne.

Sai da ya tabbatar ya 6ata wani abu a jikin wayar ta kuma bashi ya duba mata matsalar sannan ya aikata duk shirin sa.

Ganin Ammi bata 'daga wayar ne ya sashi dole badan yaso ba suka fito, shi da Safaah matar sa da kuma Zamrud 'diyar sa duk basu bar kowa ba, dayake bayan maghrib ne babu wanda ya yadda ya zauna shikadai a gida...ashe ajali ke kiran su.

Da shigan su motar Safaah. kabeer da Zamrud suka fara jin wani iri ajikin su amma basu bi takan yanayin ba.

Sun fara tafiya har sun hau babban titi kawai yanayin.ya ta'azzara gare su har idanun Kabeer suka fara juyawa bayan rikidewa ja da suka yi, ga uban atishawa da suke jerawa, ya fara zargin wani abu kawai suka fara jiyo kukan mage daga bayan booth 'din motar kamar wasa.

Wani uban birki da ya taka tsakiyar titi cike da mamakin yadda akayi mage ta shigo masa motar da wannan lokacin har ma ya mance da cewar tsakiyar titi suke.

Kafin yayi wani yun'kuri cikin abinda bai fi seconds shida ba abin ya faru, wata babbar motar da ke tafe abayan su ta haura musu babu sassauci koka'dan tamkar matu'kin motar baya gani.

Daga shi har sauran babu wanda ya sake jan dogon numfashi illah Kabeer da Zamrud ita ka'dai.

Kafin jama'a su gama tururuwar neman agaji Sultan ne kan gaba wajen basu taimakon karya.

Zaku sha mamakin cewa da shi cikin wannan babbar motar da ta bibiyi bayan su batare da sun san cewa su take bi ba.

A zahiri ba taimakon su yake ba so yake yaga wanda bai 'karasa cikin su ba ya 'karasar da su.

Zamrud ya fara fahimtar tana numfashi sai Kabeer da ko 'dan yatsan sa baya iya 'dagawa.

Cikin nuna rashin imani da tausayi a 6oye garin fito da Zamrud cikin motar ya mur'de wuyan ta.

Hakan ya faru ne akan idanun Kabeer amma bashi da damar motsawa balle ya dakatar da shi.

Idanu ya lumshe ya kuma bu'dewa yana jin yadda hawayen sa ke gangarawa gefe da gefen fuskar sa.
Sultan ne ya mur'de wuyan 'yar..gudan jinin sa bayan duk soyayyar da yake nuna mata....ashe soyayyar 'dan kada Sultan ke yiwa Zamrud.
wannan wani irin butulci ne?

Ha'kika yau yaga cin amana ganin idon sa, bai ta6a zaton haka halin Sultan yake ba, bai ta6a zaton suna rayuwa ne tare da makashin su ba, shakka babu Sultan ne... Sultan ne ya kashe musu mahaifi...ya kuma dasa musu zargin Alhaji Rufa'i da gangan, badan ma Allah ya rufa asiri ba da ba 'karamin tafka abin kunya zasu yi ba.

Sai da ya ciro Zamrud ya shimfi'de bayan ya tabbatar bata numfashi sannan ya koma kan Kabeer ya fara kukan 'karya.

Kan Kabeer ya 'dora saman cinyar sa yana kiran sunan sa yana faman jijjiga shi.
" Yah Dan Allah kar ka tafi ka barmu ya zaka yi mana haka Yayah..?"
Kabeer idanun sa 'kyam akan fuskar Sultan yana ji inama...inama, inama da ba acikin wannan halin ya gano waye Sultan ba.
Ji yake da yana da hali da babu abinda zai hana shi bayyana sa ga 'yan sanda koda hakan shine abu na 'karshe da zai aikata kafin numfashin sa ya barshi amma babu dama...ji yake da yana da dama idan bai ga bayan Sultan ba bai haifu cikin Ammin sa ba.

Jikin sa kaca- kaca da jini ta ko'ina saboda rashin wasu sassa na jikin sa amma ahakan Sultan ya rungume shi kai kace duk dunia babu mai 'kaunar sa sai shi ka'dai.

Cikin hakan batare da kowa ya farga ba ya danne ma'kogoron Kabeer yana kan kukan 'karyan bai 'daga ba sai da ya tabbatar 'dan numfashin da ya yi masa saura ya tafi.

Bazan iya misalta muku irin tashin hankalin da wannan ahali suka sake samun kansu ba...rayuka ne 'dai 'dai har guda hu'du.

Rayyan kansa wannan karan sai da ya kusan kwantawa asbiti saboda tsananin tashin hankali.

Sultan ya shirya kashe shi ne kawai saboda alamu da yagani na cewar bazai yadda abashi auren Safaah ba...duk da ma akwai wannan 'kudurin a ramsa, cikin lissafin wa'damda zasu tafi harda shi amma alamu da ya nuna cewa kamar baya ra'ayin ha'din auren su ya sanya dole mutuwar sa ta matso kusa cikin jadawalin lissafin Sultan.
Duk dama bawai soyayya tasa yake son auren Safaah 'din ba kawai saboda wata manufa ce tashi ta daban ne.

Wannan karan ma ankai ruwa rana kafin gidan nan suka dawo dai- dai, sai dai dole a halin yanzu basu da walwala.
Bayan rasuwar da kusan watanni hu'du sannan Rayyan ya koma Uk amma bai koma tre da Nadia ba.
Chapter 88 · 0% Book details