← Book details Binteee Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 218

Sashe 25

Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kokari tayi ta 'dan bude ido kadan jin shiru na wasu sakanni ne ce komai ba kuma bata ji alamun ya tafi ba, hakan yasa ta 'dan 'dago dan duban fuskar sa cikin rashin sa'a idanun ta suka sauka akan hannun sa na dama dake ri'ke da 'karamar bindiga.." Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un abinda Zaitun ta furta kenan cike da kidima gami da sake rintse idanu ta kame jikin ta kamkam Mufee kanta dake rungume da ita sai da ta saki dan kara bayan tuni ta bar kukan tana sakin ajiyan zuciya.
Komai sai ya tsaya mata cak.
Sauran mutane uku da ke zaune cikin motar ne sukai saurin fitowa, dama duk hnkulan su na gareshi gudun kar wani abu ya sami shugaban nasu.
Yana jin fitowar su, kuma yasan da fitowar tasu me zasu yi next bindigogi zasu ciro dan attacking koma miye, sanin hakan da yayi ya sanya shi saurin 'daga musu hannu dan dakatar da su ba tare da ya bari ta gani ba, amma ina ba mamaki mantuwa yayi da cewar shima akwai a hannun sa.

Ita kam hankalin ta duk ya bar jikin ta banda 'kyarma babu abinda jikin ta keyi, tunanin ta kaf ya tafi ne ga tunano amfanin bindiga...abu biyu kacal ke dawo mata...ranar da aka harbe Nadia, da kuma daren da 'yan fashi suka shigo gidan Hajjaju wannan ma ta gansu da bindigogi a hannayen su.
Kafin ya sake yun'kurin yi mata wata tambayar tuni Zaitun ta sume a zaune.
Tsaye yaran san suke cirko cirko yayin da shi kuma ya durkushe gaban Zaitun yana sake kare mata kallo dan tabbatarwa idanun sa cewa ita din ce dai ba wata ba.

Bayan fahimtar suman da tayi ne sai ya saurin dafe kansa cike da 'yar damuwa.

Tsaye ya mi'ke daga durkuson da yayi gami da 'daukan bindigar sa...ya koma mota da 'dan sauri, yayin da yaran sa suka take mar baya duk suka shige batare da kowa ya furta ko kalma ba.

Key ya yiwa motar ya tada da niyyar barin wajen amma sai yaji zuciyar sa ta kasa amincewa da hakan...Birki ya taka gami da bawa yaran sa umarnin a shigar da su da kayan su...

Kafin cikar mintina biyar har sun 6ace daga wurin.

Zaitun duk bata san anyi hakan ba sai bu'de idanu tayi ta ganta kwance kan wani gado lafiyayye.
Ta gane hakan ne kuma saboda yanayin yanda taji laushin sa da kuma yanayin yadda dakin yake...motsi tayi da hannun ta da niyyar tashi ta zauna nan ta fahimci ruwa da bata san na menene ba da ake kara mata hakan yasa ta koma ta kwanta tana mai dafe goshin ta da 'dayan hannun ta, Hijab din ta da taji akanta yasa ta gode wa Allah domin tasan shine rufin asirin ta, tunowa da tayi cewar rigar ta a yage take..bata san ya akayi tazo nan din ba kam amma duk da hakan ta gode Allah da ya tseratar da ita...tsintar kanta tayi da fa'din _Alhamdulillahi_ wannan maganar ta tsaya mata iya kan la66an ta ne.

Gefe da gefen ta ta kalla sai taga babu Feefy babu me ko me kama da ita sai wani kyakykyawan mutun zaune nesa kadan da ita ya zuba mata idanu.

Tashin farko ba tare da wani dogon tunani ba ta fahimci waye shi ta kuma tuno inda ta sanshi..." Dr Rasheed..!"
Ta fa'da 'kasan ma'koshi.

Gira ya ha'de ba tare da ya furta ko kalma ba kawai ya mike tsaye bayan ya tabbatar da tashin nata..nan Parlour ya koma zauna ya cigaba da latse- latsen sa cikin laptop..."..ina 'ya ta..?
Ta tambayi kanta tana me kokarin tashi zaune.
" kar dai dagaske sun raba ni da ita?"
Ta tambayi kanta.
Sai kuma ta rushe da kuka...dan ita gani take duk bakin su 'daya ne da Hajjaju, bazata manta ba ko acan asbitin da kwanaki aka kwantar da ita tare ta gansu.

Ko 'kala Dr Rasheed bai ce da ita ba bai kuma dawo 'dakin dan yi mata magana ba har tayi kukan, tayi surutan ta koma ajiyan zuciya..ta kuma sake sakin wani kukan daga baya wanda ya fahimci tana yin kukan ne cike da kewa da kuma damuwa gami da nadama.

Fahimtar da yy idan ba dakatar da ita yy ba har illah zata iya yiwa zuciyar ta yasa shi dawowa 'dakin gami da fa'din"...ya isa hakan nan mana, kukan ya ishe ni haka..."
Cikin kukan ta furta..
" Yarinya ta banganta ba fa ina kuka kai min yarinya...?"
Sai yanzu ya fahimci dalilin tsananta kukan, shi abin ma dariya ya bashi ganin 'yar yarinya da ita da yake da tabbaci 16yrs ma bata haura ba amma wai har yarinya gareta, tun a wancan lokacin yayi mamaki.
Sai da ya dawo ya zauna bisa drawer inda ya tashi dazun kafin cike da kulawa cikin kwantar da murya yace
" Ki kwantar da hankalin ki yarinyar ki tana nan..kuma zaki ganta amma sai kin daina kukan nan...."

Jin hakan yasa ta saurin goge hawayen tana duban fuskar sa.

" Ina ke mk ciwo yanzun?"
Ya sake jefa mata tambaya cike da kulawa.

"...Ni...ba komai.."
ta bashi amsa cikin sauri tana 'dan turo bakin ta irin ita ba wannan ce damuwar ta ba..kanta na tsananin ciwo amma bata shi take ba.
" So..zaki iya tafiya yanzu kenan?"
kai ta 'daga masa alamar "ehh.."
Waya ya 'daga yy kira inda yayi magana da harshen turancin da Zaitun ko ka'dan bata jin sa.

Nan take ba a wani dade ba taga wani ya shigo hannun sa rike da Mufee.
Mufeeda na ganin Zaitun ta fara 'daga hannuwa da nuna alamun son isa gareta.

Dan haka ya matso ya kawo
mata yarinyar, ai da ganin Mufee jikin ta ta washe baki gami da rungume ta har ta ma mance da karin ruwan da ke hannun ta...itama Mufee sai ajiyan zuciya take sauqewa da alamu tasha kuka sosai.
Jikin fess an mata wanka an canza mata riga tayi kyau abinta...zuwa yanzu ta gama fahimtar cewa Dr Rasheed shine ya taimake ta bata manta sautin muryar ba sam sai dai wani abu guda daya tsaye mata.
In bata manta ba taga bindiga a hannun sa jiyan, kuma ta san shi likita ne, toh menene hadin ma'aikacin asbiti da rike bindiga...ko duk cikin ceton lafitar mutanan ne tamkar dai yadda ya faru da ita.

Dole Dr Rasheed ya cire mata karin ruwan kafin ta karkata bakin allura ta janyo wani abin daban, yana murmushi yake jinjina kaunar juna da suke yi ita da 'diyar tata.

"..Zan turo driver sai ki fa'da masa gidan ku ya kaiki kafin a fara neman ki".
Ya fa'di hakan bayan ya mike tsaye da niyyar barin 'dakin...
Bata tanka shi ba har sai da ya kusan fita daga 'dakin kafin kamar bata son yin magana tace"..mu ba wani gida da muke da shi, kuma babu wanda zai neme mu, kawai ka barshi da kaina ma zan tafi...nagode sosai da taimakon ku".

Cak ya tsaya ba tare da ya jiyo ba...tunani yake cikin zuciyar sa..." me yarinyar ke nufi da wannan maganar?

Baya ya dawo ya tsaya a kanta.
" Me kika ce?"
Ya sake jefa mata tambayar yana mata kallon tuhuma.

Zaitun sake maimaita masa tayi tana gyara rigan dake jikin Mufeedah.
Hannun sa duk biyu yasa cikin aljihun wandon bakin jeans dake jikin sa, sannan yana gyara tsayuwa yace " Dama can a ina kike rayuwa kafin ha'duwar ki da Hajiya Mardiyya?"
Shiru tayi bata ce da shi komai ba...tunanin amsar ma da ya kamata ta bashi take, in hasashen ta yazo daidai yana tambaya ne akan Hajjaju domin tare tasan ya ta6a ganin su lkcn da ta kaita asbitin su amma ita bata san asalin sunan Hajjajun ba, in kuwa akanta yake magana bata da wani dangantaka da ita Hajjajun kade ta kawai tayi da mota har ta kai ta asbiti daga nan kuma gidan ta.
In kuwa itan ce ai tasan yasan duk wannan tunda shine likitan da ya duba ta a lokacin...toh me kuma yake son sani bayan wannan.
" Tambayar ki nake yi ko...dama menene alakar ki da Hajiya Mardiyyan...?"

Salmerh😘
[20/9/2022, 12:32 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕
*( 'Yata ce)*

*Salmerh MD*

🅿️ *...17*

Jin canza salo da tambayar tasa tayi ne ya sanya Zaitun 'dago idanun ta ta dube shi suka hada idanu, saurin kawar da kanta tayi gefe...kawai sai taji zuciyar ta ta aminta da shi 'dari bisa bari, take damuwar ta fara rage nauyi a zuciyar ta, haka kawai sai take jin sa tamkar wani garkuwa ne a garesu baki 'daya.

Wani sabon hawaye ne ya 6alle mata na tausayin kansu, amma sai tai saurin share hawayen, a hankali ta bu'di baki tace" Ni ban san su ba...Hajiyar ce ta kaini gidan bayan mun baro asbiti a wancan lokacin, ita ta taimaka mana ba tare da nasan su din wa'danne irin mutane bane, lokacin da nazo na farga da hakan na fara tunanin rabuwa da su a lokacin su kuma suka shirya raba ni da 'yata shiyasa na gudu, jiya na bar gidan da dare saboda in tseratar da yarinya ta garin hakan Allah ya hada mu da wadancan a bakin titi...yanzu bani da kowa bani da inda zanje, kawai zan tafi ne, ina so inyi nesa da su inda bazasu sake gani na ba".
Tana gama fadin hakan hawayen ta ya kara karfin kwaranya.
Bai ce mata komai ba illa kallon ta da ya tsaya yi sosai yaji ya tausayawa mata, domin shi yasan wace Hajiya Mardiyya, farin sani yai mata tun ba yau ba, kusan mintina biyu yana tsaye a wajen kamar ba zai sake magana ba sai kuma can ya furta" Kafin ha'duwar ki da Hajiya Mardiyya...?"
Bata ma bari ya kai karshe ba tayi saurin tarar sa da fa'din..." Bara nake bamu da kowa kuma a haka muke rayuwar mu..."
Tayi saurin fadin haka ne gudun kar yace zai tambaye ta asalin garinta da kuma dangin ta balle yayi tunanin mayar da su...

Kallon sakanni Dr Rasheed yai mata sai kuma ya juya ya fita yana me ciro wayar sa dake aljihun sa.
Chapter 25 · 0% Book details