Sashe 122
Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Rabon da ya tako 'kafar sa gidan ganin Rayyan ko gaishe da Ammi awanni Arba'in da takwas kenan yanzu...banda zurfafa tunani da rashin sukuni babu abinda ke dawainiya da shi...wannan shine Fitsarin Fako, shi da ya shirya shiryayyen mugunta ga Rayyan dan kashe shi banda rashin nasarar da ta same shi sai gashi lokci guda ana shirin zabtare masa wani yanki na farin cikin sa ahakan ma Rayyan na kwance ne, kenan duk wancan shirin da ya jima yana tsarawa da lokaci, dukiya, tunani da ilimin sa duk Rayyan zasu amfana ba shi ba?
Kenan nasarar ta Rayyan ce ba shi ba..?
Erh mana...tunda gashi lokaci guda ana shirin aura masa yarinyar da 'kaunar ta ke neman halakashi, yarinyar da ta kasance bugun zuciyar sa, yarinyar da bayan ita ba ya iya yiwa sauran mata kallo mai muhimmanci ciki kuwa hadda matar sa Marwa, hakika kaunar ta ba 'karamin kamu ya yiwa zuciyar sa ba.
Kenan abinda yayi masa wata nasara ya kara masa ba ci baya ba.
Gashi su Raihana sun kane kane sun kasa bada wata damar da zai 'karasa shi abin na.masa ciwo a zucia.
Duk kuma yadda yaso ha'duwa da Zaitoon abin ya faskara dan sam ya rasa damar hakan.
Yayin da Zaitoon ke can tana 'kokari sosai wajen ganin ta danne damuwar da take jin zuciyar ta a ciki gudun kar su Ammi su fahimta suji kamar erh dagaske sun tilastata din ne.
Amma sau tari idan ta ke6e ita kadai yanzu banda kuka bata da wani aikin yi, sai ta ringa gani tamkar ba dai- dai ta aikata ba da amincewa batun da tayi, wani sa'in kuma sai ta ji cewar ai ba wani abu bane dan ta amince tunda na lkc ne da zarar ya farka zai sallama mata, wannan 'dan tunanin ke 'kara mata 'kwarin gwiwa kusan ko wani lkc.
Kamar wasa kamar gaske sai gashi an fara kasantuwar lissafin lokacin, tun daga ranar data amince musu basu sarara ba har zuwa ranar da ya kasance kwanaki biyu kacal suka rage a 'daura mata aure da Rayyan, ta kuma tabbatar bazasu sarara din ba har sai sun tabbatar an 'daura dagaske.
Saidai batasan me yasa ba, a tsakanin kwanakin maganar tafi tsaye mata a zucia, bata san menene dalilin dayasa maganar ke ta6ata sosai har hakan ba, batasan meye dalilin da jiki ta da zuciyar ta suke sake shiga rudu da girgiza har haka ba, shin maganar sabo yake agare ta ne ko kuwa tunanin me goben ta zai haifar mata ne?
Ga dai tanan amma Allah kadai yasan halin da take ciki.
Meye matsayin ta? meye sakamakon rayuwar ta anan gaba? Duk bata sani ba, wanne sabon shafin zata sake bu'dewa? Shima bata sani ba...wace 'kaddarar ke sake tunkaro ta, wacce sabuwar kaddarar zata jefa su ita da 'diyar ta duk bata da masaniya.
Sultan be samu daman ganin Zaitoon ba har sai da ana gobe 'daurin aure kafin ya faki ido har 'dakin ta ya same ta, a lkcn kwance take tana tunani, ita ka'dai a 'daki domin rabon ta da Mufee ma idan bata manta ba tun safia, tana can wajen su Anty Madeena dan tun su Raihana na dariyar yadda Anty Madeena ke bawa yarinyar kula har suka daina suma suka bi sahu, bisa alkwarin da ke tsakanin ta da Rayyan kuma basu yanke shawarar bayyana boyayyen maganar ta su ga kowa ba shiyasa su Raihana basu san dalilin sha'kuwar dake tsakanin ta da Mufeeda ba a tunanin su kawai dan sun yi zama tare ne shiyasa, kuma su kansu shaida ne akan yadda Mufeedan ke shigewa zukatan mutane lokaci guda sbd tsabta da kuma kulawar da take samu bayaga haka ma Allah ya zuba wa yarinyar tsantsan farin jinin mutane duk da yake ba magananniya bace sosai..amma tabbas a jinin ta ne tamkar dai na uwar ta.
Sanin haian da sukayi yasa basu ta6a zargan komai ba ciki kuwa hadda Ammi.
Sai dai 6angaren Sultan abin ba haka yake ba...shima da farko yayi tunanin ko da suna son hillatar Zaitoon din ne ta auri 'dan su shiyasa suka dauke mata nawin yarinyar ta, sai dai daga baya ya fahimci sam ba haka kadai bane domin yanayin kauna da shakuwar ya zarta tunanin sa ya kuma kasa hasaso komai.
Anty Madeena kuwa babban abinda ke dakatar da ita bayyana matsayin yarinyar ga kowa shine cewar da Rayyan yayi bai gama binciken ba tukunna ta 6angaren sa...baya ga haka da tuni ta bayyana yarinyar tasan zasu yi matukar mamaki da jin hakan, ko batun auren Zaitoon ma ta karfafa shi ne sbd abubuwa biyu, farko batun Amrah burinta a 'kona zuciyar su kwatankwacin yadda suka 'kona tasu zuciyoyin, abu na biyu kuma sbd Rayyan, ta tabbatar idan Zaitoon ta kasance 'karkashin ikon sa binciken su zai fi zuwa masu da sauki...za samu duk abinda suke da bu'kata cikin sauki da iznin Allah.
Zaitoon kam kwance take tana tunani, domin a wannan lokacin bata da wani abokin hira sai ita sai tunanin ta kadai, tama mance da duniyar da take ciki kawai taji motsi, a firgice ta mike zaune.
Ga mamakin ta sai taga ashe Sultan ne.
Idanu ta fitar waje sosai bakin ta na dan rawa tace..." Yah Sultan...lafia...?".
" Bani da tabbaci Zaitoon domin daf ake da kaini 'kasa....!"
Ya bata amsa yana me 'karasowa inda take yayin da tayi saurin mikewa tsaye ta sauka a gadon tana sake fuksantar sa gami da hade giran waje guda.
Kallon ta ya tsaya yi cikin ido yana sake jin wata kaunar ta zazzafa na ratsashi, yana son Zaitoon har zuciyar sa, yana kuma tsananin kishin ta.
Duk wani tsari da plan na rayuwar sa ta gaba da ita yake tsarawa...amma sai gashi kwatsam rana tsaka ana so a rushe duk wannan shirin nasa da ya jima yana tsarawa.
" Yah Sultan meyafaru, wani abu kake nema ne..?"
Ta sake tambayar sa muryar ta na rarrabewa sbd ganin irin kallon da yake mata.
Idanu ya lumshe ya kuma bu'dewa akan fuskar ta..yana sakin huci mai zafi.
" Babu komai...ba komai Zaitoon sai dai illar da ake so.a yiwa zuciya ta dalilin ki kadai....".
Bata fahimci maganar tasa ba hakan yasa tayi shiru...sai kuma taga yin shirun nata sam bai dace ba, kamar yadda ke6ewar tasu bai kwanta mata a zucia ba.
" Yah Sultan idan wani abu kake so dan.Allah ka fada min sai in kawo maka aima da ba sai ka taho har nan ba da aikawa kayi a kirani kawai sai inzo..."
" Da Allah kimin shiru..."
Ya buga mata tsawa yana jin hucin da zuciyar sa ke fiddawa.
Tuni idanun sa sun rikide zuwa jajaye.
Duk abubuwan da ya aikata abaya baya jin sun kai wani matsayi, baya jin sun kai. girman abinda zai iya aikatawa matukar aka yadda aka shiga tsakanin sa da yarinyar nan.
Abinda zai aikata akan.Zaitoon zai iya bawa kowa mamaki amma ita kanta bata san hakan ba.
Tsawar tashi tuni sake rikita ta..sai ta fara duban hanya ta gama yanke.shawarar ficewa ta bar dakin aganin ta yafiye mata fiye da kasancewa tare da shi a dakin tun kafin akai matsayin da zai make ta duk da yake bata san laifin ta ba har yanzun.
Fahimtar da yayi cewa shirin gudu take ya sa shi saurin tare kofar yana sake bin ta da kallo sai tayi kasada idanun.ta.
Tsawon sakanni masu yawa yana kallon ta gami da tausan zuciyar sa ya kuma sanyaya muryar sa.
" Wai da hankalin ki? Zaitoon da wayon ki zaki amincewa auren wancan dutsen...?"
Salmerh😘
[18/11/2022, 3:08 am] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕
*( 'Yata ce)*
*Wattpad@*
_Serlmerh-md_
🅿️ *...71*
.......'Kan'kance idanu Zaitoon tayi sosai tana duban sa da mamaki..." Yah Sultan Dutse kuma..? waye dutsen...?"
Shima a zuciye ya bata amsa sbd yanayin 6acin ransa ke 'kara hauhawa musamman daya ga yau gashi ga ita wuri guda amma lkc kadan ya rage ta zama mallakin wani ba shi ba.
Ji yake tamkar ya 'dauke ta gaba 'daya ya gudu da ita yaje ya killace akabar sa kowa ma ya daina ganin ta sai shi ka'dai.
" Wancan dake kwance yake irga kwanakin mutuwar san nake nufi..!
Yayi maganar tare da yin nuni da hannun sa idanun sa na sake rinewa
".....me kike tunanin zaki samu tattare da shi? Me kike tunanin zai amfanar miki da shi baya ga bauta da zaki yi ta masa har 'karshen rayuwar sa..."
Baya kadan taja sbd yadda yake.fitar da maganar tasa tamkar zai hadiye ta 'danya.
Tana 'dan yamutsa fuska gami da takure jikin ta waje guda tace.
" Yah Sultan dama ai ba dan in samu wani abu na amince da auren ba face dan inyi bautar ka'dai...".
Sultan ji yake tamkar ya make ta sbd takaicin ta, meyasa ta kasa fahimtar inda ya dosa ne? meyasa sam kwakwalwar ta bata ja koka'dan..shi aganin sa Zaitoon tafi 'karfin tayi wannan bautar har abada sbd itan mallakin sa ce, be san me ya hana Rayyan 'din mutuwa tun a ranar farko ba, bai san me ya tsaya jira ba da har za'a bautar masa da Zaitoon sbd shi.
Ya 'karashe tunanin yana mai watsa hannu alamun dai takaici ke cin sa.
Har ya juya sai kuma yy turus, still dai idanun sa na nan a rine.
Babu komai...a yanzu damar tasa ce gaba 'daya, damar sa ne ya bar Rayyan ya cigaba da rayuwa, damar sa ne kuma ya 'karasar da shi ga hanyar barin.duniyar da ya kamk....amma tabbas bazai bari ba, dole ne sai yayi wani abu guda...wala alla hakan zai iya haifar masa da kwanciyar hankali mai 'dorewa.