Sashe 77
Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sunan ta da Ammi ta ambata yasa da sauri ta 'dago da kanta, tuni idanun ya rine jajajir..." Zaitoon zan tambaye ki ki tabbatar kin sanar dani gaskia, dan ko baki fada min ba Allah ya gani kuma kinsan sai ya miki hukunci kan hakan..."
" Kin dau ki sarkar Amrah ko.baki dauka ba...?"
Kai ta fara girgizawa" Wallahi Ammi ban ta6a sha'awar 'daukan abin.kowa ba, ban ta6a ganin abinda ba nawa ba ne nayi sha'awar 'dauka kuma har abada bana fatan hakan ya faru dani, sarkar ta kuma ban ma san ya kalar ta take ba balle in dauka...."
Tana maganar ne hawaye na sauko mata da gudun su.
Ammi bata jira taji karshen maganar Zaitun ba ta maida duban ta ga Amrah domin ta riga ta samu amsar da take bu'kata..." duk zaman da zakiyi da mutum Amrah ki tabbatar baki zalunce shi daidai da 'kwayar zarra cikin zaman ku ba domin Allah baya barin azzalumi da maha'inci, sannan ki tabbatar kina da hujja kwakkwara kafin ki yanke hukunci gudun abinda zai je ya dawo, dukkan ku tamkar 'ya'yana nake jinku so bazan bari 'daya ya cutar da wanin sa ba...ba kuma nufi na in 6atawa kowa daga cikin ku ba amma gaskia ce a duk yanayin da tazo dole zan fade ta hakan shine dai-dai...
" Kafin Zaitun ta fara yi miki aiki ta min aiki na tsawon lokaci kuma nasha bar mata bedroom 'dina ta gyara ta share min lungu da sa'ko na dakin, ko wani 6angare ban mata shamaki da shi ba..daidai da allura ban ta6a nema na rasa ba har kawo yau 'din nan kuma bata fasa ba, me yasa sai a wajen ki zata 'dauki abu? Me Zaitun zata yi da sarkar ki...? Ku ji tsoron Allah ku kyautatawa 'yan uwan ku zato ku kuma kyautata mu'amala da kowa da ke rayuwa kusa da ku 'daya daga cikin halayyar mutumin kirki kenan...."
" Zaitoon zo mu wuce ".
Ta fa'da tana duban 6angaren da Zaitun take.
Sai kuma ta sake dawowa ga Amrah" In kuma aikin da take yi mk ne baki so daga yau an daina kiji dadin ki, sai ku nemo mai muku hidimar sashen ku daga yanzu, sarkar taki kuma idan baki samu ba ki rubuto min adadin kudin ta zan bayar aka kawo miki sai ki sayi wata..."
Daga haka Ammi ta ja hannun Zaitun suka yi gaba.
Amrah kuka kawai ta sanya ta zube a kasa tana fa'din an ci mata mutunci, an muzantata, yau an wulakantata gaban 'yar aikin ta.
Rayyan kuwa ficewa yayi ya bar gidan kawai bai dawo ba kuwa sai yamma.
Shikan sa yana bayan maganar Ammi, dan bai ta6a jin anyi complain da 6atan komai a wancan 6angaren ba...kawai dai Amrah wani abin take nufi ko kuma inma gaskiya ne bata ga sar'kar ba to ba mamaki Amran manta inda ta ajiye sarkar tayi ko kuma bata nutsu ta duba da kyau ba...amma bari idan ya koma zai tayata su sake dubawa ko za'a dace.
Ko da ya koma gidan bai tarar da Amrah ba, bai kuma neme ta ba dan yana kyautata zaton gidan su tai tafiyar ta.
Har washegari Amrah bata dawo ba, bai sanar da Ammi bata nan ba haka kuma har a lokacin bai nemi numbern wayar ta ba.
'Bangaren Zaitun kuwa daren ranar kuka tasha sosai ta 'koshi, ji take tun da take aduniya ba'a ta6a ci mata mutunci irin ranar nan ba, sata fa, tayi me da kayan sata...?"
Tun daren ta yanke shawarar barin gidan, ta sha yanke irin shawarar nan akaro babu adadi amma wannan karon tana jin babu abinda zai dakatar da ita.
Washegari da ya tashi wajen aiki gidan su Amrah ya nufa ya nemi ganin ta amma mahaifiyar ta taki bashi dama, haka ta 'dime ta zayyana masa sharu'd'da kafin ta sake bashi dama akan Amran, ranshi ya 6aci sosai da jin kalaman mahaifiyar Amrah.
Tun anan yaga gazawar ta wajen mutuntaka, kuma ya tabbatar dan mahaifin ta baya gari ne amma da baza'ayi hakan ba.
Taya zata ce sai an sallami mai aiki a gidan kafin Amrah ta dawo, ba fa shi ya kawo yarinyar ba..mahaifiyar sa ce, so take ya yi iko da Ammin nasa ko kuwa me take nufi...?"
Duk yadda yaso fahimtar da Mummyn Amrah gagara fahimtar sa tayi.
Cike da haushi ya bar gidan cikin ransa yake fa'din ta ji'ka Amran ta shanye idan wata tsiya ce..".
*Drop ur Comment pls*
Salmerh😘
[11/10/2022, 6:10 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕
*( 'Yata ce)*
*Wattpad@*
_Serlmerh-md_
🅿️ *...48*
.......A hanyar sa ta komawa gida ne ya fara hango wata kamar Zaitun kamar kuma ba ita ba...hakan yasa ya rage speed ya fara tafiyar a hankali sosai tamkar bai so yayi.
Tafiya take tunani kala- kala na zuwan mata.
A yanzu babu abinda tafi tsoro irin masu hannu da shunin nan, duk kan su kusan iri 'daya suke, kowa da nashi kalar sharrin yake tafe, bazata ta6a mantawa da zancen Hajia Talatu ba, a maganganun ta 'karara ta nuna mata bayyanannar tazara dake tsakanin ta da su, a yanzu kuwa ta sake tabbatar da hakan, ta sake tabbatar da cewa su 'din rayuwar su kal dabn take da ita koda kuwa aiki kake karkashin su kawai dole sai sun nuna maka bambanci.
Shiyasa Hajiya Talatu ta tabbtar mata da bambancin dake tsakanin ta da Adam Shaheed abaya, ta nuna mata cewa Adam ba sa'anta bane ta kowace fanni, a lokacin bata yi mamaki ba, sai ma mamakin yadda Adam bai ta6a sanar da ita hakan ba da tayi, bai ta6a nuna mata wata alama da zata sa ta gane cewa mahaifin sa wani babba ne a'kasar nan ba.
Sai dai maganganun Hajiya Talatu ba 'karamin tasiri sukai mata a zuciya ba, dagaske har zuciyar ta ba taji son Adam ba, bata ji tana 'kaunar sa ba, bata kuma ji cewa ta shirya aure a lokacin ba, ko dan bata taba yin so bane oho, dan dama tun asali ita zancen so baya gaban ta kokadan...kyautatawar sa dama agareta ne kadai yasa taji erh zata iya amincewa ta aure shin, ko ba komai shidin me 'kaunar ta ne tunda yana 'kaunar Moopy gami da bata kulawa, kuma ance zuciya na son me kyautata mata ne.
Sai dai bisa shara'di da kashedin Hajiya Talatu dole ta barshi, kuma bata yi ba'kin ciki da hakan ba ba balle ta matsawa zuciyar ta da tunani, jin babu da'di ko tausayin sa, dan tasan ita din ba kowan kowa bace, ba komai bace cikin tarin kyawawan mata da Allah ya azurta duniya da su, mata masu aji da ilimi da tunkaho da dukiya da karfin mulkin iyayen su wadanda suka fi dacewa da shi tamkar yadda Hajiyar sa tafiso, tasan Cikin lkc kalilin Adam zai samu wacce ta fita ta maye masa gurbin ta, shiyasa bata damu ba sam, musamman da tasani kuma ta aminta da cewa lalle dagaske ita din ba tsarar sa ba ce..dama can ta saba da wahalar rayuwar ta, ta saba da fadi tashin ta ita ka'dai, so ba sabon abu bane yanzu gareta...hakan yasa ta saki ranta ta cigaba da rayuwar ta tamkar yadda ta saba can baya kafin zuwan kaddarar ha'duwa da Dr Rasheed ta same ta.
Sai dai daga ranar da ta ji sunan mahaifin sa cikin case 'din su, komai ya kwance mata, tausayin Adam ya tsarga mata sosai, tasan zaiji babu da'di, zai kuma ji nawin cigaba da walwalar sa kamar baya yadda ya saba.
Zaitun tayi duk wannan tunanin ne lkcn da take tafiya bayan ta bar gidan Ammi...gidan da taji fit ya fice mata aka, bazata ta6a iya rayuwa a inda ake binta da sharrin sata ba...yinin ranar kaf jin ta take tamkar akan 'kaya take, ko lkcn da take kulle a prison bata ji matsuwar barin sa kamar wannan gidan ba, kuma tana fita daga cikin sa taji wata natsuwa ta sau'kar mata..har da sakin ajiyar zuciya.
Tun kafin ta bar layin gidan ta fara hango mota na tahowa ya kuma haske ta sosai duk da duhun ba mamayi garin sosai ba amma sai aka wani haske ta da fitilar motar, bata san waye haka cikin motar ba amma yadda ya rage gudun motar ya kuma haske ta ya sanya tsoro sake tsirga mata,
Cikin ko wani da'ki'ka rayuwar ta na baya ke sake dawo mata.
Tsoro da fargaba cika mata zuciya suke akai akai...tsoron abinda ya ta6a faruwa da ita ya sake maimaita kansa.
Tun ba ta yi nisa ba taji jikin ta yayi sanyi.
Bata ta6a sanin zama cikin gidan babban garkuwa ne agareta ba sai yanzun da ta tsinci kanta bisa titi ga hasken da ya dallare ta.
Bata san inda zata nufa a cikin gari irin kano ba, bata san gabas ba balle yamma.
Tun fitowar ta taji kanta gaba 'daya ya juye mata wani 6angare na daban.
Daf da ita motar tazo ta faka sai dai ba'a bude ba, sai anan ma ta fahimci ashe 'daya daga cikin motocin gidan Ammi ne sai dai bata san waye a ciki ba duk da tasan waye ya fiye amfani da wannan motar kasantuwar windown 'dakin ta dake saitin babban wajen parking din gidan.
Tana iya jin yadda idanu ke mata yawo ajiki ta tabbata ita ake 'karewa kallo hakan ne yasa tsoron ta 'kara karfi, shirin gudu ta fara sai kuma akayi rashin sa'a dai dai zata gota motar taga anbude ta.
Taku baifi hudu yayi ba ya cimma ta yana dawo da ita baya fuskar sa babu yabo babu fallasa yace" Sai ina kuma? Ko dai yawon bai 'kare bane har yanzu...?"
Ya tambaya yana duban 'kwayar idanun ta.
" Cika min hannu na malam".
Ta fa'da cike da karfin gwiwa da zafin masifa da ya taso mata nan take, dukkan su ahalin gidan haushin su take ji in ka 'dauke Ammi ka'dai.
Gire ya 'dage yana kallon fuskar ta yace
" Toh fa..wannan irin masifa haka, ko dai nima marin zansha kamar yadda aka yiwa Amrah kwanaki..?"