Sashe 127
Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Fara'ar da ta karanta saman fuskar ta ya bata mamaki matuka.
" Nadawo...ai hankali na ya kasa kwanciya sai da na 'kira wata 'kawata da muka yi secondary school tare acan Geidam 'din itama take aure, ita ta tabbatar min babu komai, karshe ma ta ha'dani waya dasu mukayi magana, andai sace musu wayoyi amma kowa yana nan lafia kalau duk mun yi magana da su... shiyasa na dawo kawai tunda nima marar lafiyr gare ni zuwa wani lkc naje in dubo su..."
Ammi tayi duk wannan bayanin ne tana mai 'karasawa cikin 'dakin.
" Masha Allah...Allah ya 'kara tsarewa.."
Cewar Zaitoon itama tana mai bin bayan Ammi zuwa ciki.
Kamar zata yi mata albishir 'din tashin san amma ganin yanda ya koma ya sake kwanatawa sai ya fahimtar da ita wani abu."...Ya jikin nasa ne Zaitoon...?"
Ammi ta tambaya tana mai kama hannun sa.
" Alhamdulillah da sauki sosai Ammi...".
Zaitoon ta bata amsa tana murmushi.
Ammi da yake ba duban fuskar ta take ba yasa bata fahimci hakan ba...sai ma.cigaba da tayi da fadin.
" Ni abin ma yanzu ya fara bani tsoro, so nake mu sake magana da Fawwaz, 'dazun ya 'kirani wai zai shiga tiyata da safen nan bazai samu shigowa ba sai zuwa anjima may be zuwa yamma zai shigo, so nake a canza wannan tsarin, in ma asbitin ne gara mu koma abin yana ban tso....."
Bata kai ga rufe baki ba Zaitoon dake cike da tsananin farin ciki ta ce
" Ammi... !"
Sai kuma tayi shiru tana zare idanu.
Kallon inda Rayyan yake kwance tayi tana kikkif da idanu domin bata san me ya kamata tace da Ammin ba kuma.
Duban ta Ammi tayi ta kuma bi inda take kallo da idanu.
" Me ya same shi ne Zaitoon...? Me kike son sanar da ni...? Wani abu ya faru da shine...?"
kai ta girgiza sannan ta 'dora da fa'din.." Ammi wallahi 'dazun naga kamar shi ya fito daga bathroom da 'kafafun sa kuma shi ka'dai..."
A ru'de Ammi ta dube ta da kyau...Zaitoon da rawar muryar ta 'kara da fa'din" Kamar shi Ammi...wallahi shi na gani..."
Inda tayi maganar a 'darare tamkar mai tsoron furtawa hadda 'dan ja baya ganin yadda Ammin ta fuskance ta.
" Zaitoon kin tabbatar abinda kike fada min gaskia ne ko kuwa kina fada ne kawai dan naji dadi...?"
Yanayin da Ammi tayi maganar Zaitoon sai taji ta bata tausayi sosai.
Ita kanta zuciyar ta ya karaya...bata fatan ace ganin san da tayi ace ba gaskia bane...amma tana da tabbacin a zahiri ne ta ganshi bisa 'kafafun nasa tunda har ta6a hannun ta yayi.
Da sauri ta 'dago hannun nata dan sake tabbatarwa sannan tace da Ammi.
" Dagaske nake Ammi, kin ga ma har ya rubuta min abu a hannu na...".
Ta 'karashe maganar da nuna mata hannun ta.
Da sauri Ammi ta kamo hannun Zaitoon tana kallo gami da shafa rubutun, Zaitoon kin tabbatar shine ya rubuta wannan...?"
Da kai ta bawa Ammi amsa tana duban fuskar ta da hawaye gami da murmushi suka lullu6e shi.
Sai dai murmushin ya bayyana cewa na tsantsan farin ciki ne dake tasowa tun daga 'kasan zucia.
Gaban gadon da yake kwance Ammi ta isa ta tsaya tana bin sa da idanu tama kasa fa'din komai.
Zaitun bin su da idanu tayi daga shi har Ammin batare da ta 'daga 'kafafun ta ba.
A hankali ya bu'de idanun sa ya sau'ke su akan fuskar Ammi ya sau'ke su, sai dai bai motsa ko da 'dan yatsan sa ba.
Bai so bayyana kansa cikin gaggawa haka ba amma wannan dakikiyar yarinyar ta riga ta tona shi, sai kace bata ga rubutun da yayi mata ba....sai dai bisa ga rubutun da Zaitoon ta nuna wa Ammin nasa yasan itan zata fahimci manufar sa zaku ma ta rufe sirrin sa.
'Kasa Ammi ta dur'kushe tana sakin hamdala a bayyane...bayan haka ta fara jero masa tambayoyin inda ke masa ciwo Rayyan bai bata amsar ko guda da bakin sa ba...'karshe 'kokari kawai yayi ya mi'ke zaune.
Hakan ya sake ruda hankali da farin cikin Ammi.
Ganin hakan yasa Zaitoon kama hannun 'diyar ta kawai suka yi waje taja musu 'kofar tana sakin murmushi.
Cikin ranta take masa fatan samun lpy ingantacciya.
Salmerh😘
[25/11/2022, 9:25 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕
*( 'Yata ce)*
*Wattpad@*
_Serlmerh-md_
🅿️ *...74*
........Zaitoon kam 'daki ta koma tana sake duban hannun ta...har a lokacin Amrah na zaune tana kallon Zee world...ko inda take bata ma kalla ba haka itama ta wucewar ta bata damu da wanzuwar ta cikin palorn ba....
Hannun ta nada saurin yin zufa hakan yasa tana shiga ta nemi abin rubutu da 'kyar ta samu 'yar takadda wacce ake zubo magani a ciki sai dai babu abin rubutu sam dan bata da shi ba amfani take da shi ba....
Hankalin ta taji ya fara tashi saboda ita kanta tana so ta san manufar rubutun da yai mata a hannun...kuma ita bata iya karatun hausa sosai ba ka'dan- ka'dan ta iya shima 'din Marwa ce ta koya mata duk da haka sai ta nutsu sosai take iya ha'dawa da 'kyar.
Bincike ta hau yi hankalin ta atashe, kamar an ce mata wani abin tashin hankali ne ya rubuta mata, tasan ba hakan bane amma haka kawai taji zuciyar ta ta 'kagu da son sanin abinda ya rubuta 'din dan tasan a halin da yake ciki dole ne ya kasance abu mai muhimmanci ne.
Da 'kyar ta ci karo da brown eyes pencil cikin drawer wanda ake zana gira da shi bata da mu ba ta koma ta zauna....Mufee na 'kananun kuka ma amma bata damu ba da yake tasan wanka take bukata ba komai ba, karo na farko kenan da taji wani abu daban ya 'dauki hankalin ta akan 'yarinyar ta akaf din rayuwar ta.
Jikin ta ta jawo Mufee ta kwantar da kanta saman 'kafa'dar ta...da 'da'd'daya 'da'd'daya ta fara 'dauko rubutun nasa tana ajiye wa saman papern nan...wasu ma har suna fara gogewa saboda yawan zufan dake hannun ta.
" K a r k i f a d i m a w a k!...."
" Subahanallah 'karshen ya goge wallahi".
Ta fa'da cikin ranta tana mai jin babu da'di.
Sam ta kasa gane menene a wurin, duk iya kokarin da tayi wajen ganowa amma ta kasa ganewa haka ta ha'kura da wanda ta samu ganewa.
Tana bubbuga bayan Mufee a hankali take nazartar rubutun...da manyan harruffa ne ma zata fi saurin gane su da kyau amma 'kananun haruffa na bata wahalar ganewa gaskiya, dan bata kai ga bambance su a makaranta ba har ta bar garin nasu...wannan ma bisa taimakon Marwa ne da take 'dan nuna mata wasu abubuwan yasa har ta iya ha'dawa.
" _K...kar..kak...kar ki..fa' dima k..."_
Abin sai ya kasa bata ma'ana guda 'kwa'k'kwara.
Ta maimaita fin sau bakwai kafin ta fahimci ka'dan ahakan ma " Kar ki fa'dima ko..."
Shiru tayi ta shiga nazarin rubutun sosai..sam ta kasa 'karasawa, a cewar ta sai take ganin kamar sunan mutum ne ya rubuta amma duk gidan batasan wani da sunan shi ya fara da kalmar _ko_ ba.
Har taje tayiwa Mufee wanka itama tayo nata ta fito abin na ranta kuma ta kasa fahimtar in da maganar ta dosa.
Tana shirya Mufeeda tana sake duba rubutun nata.
Ganin bata da masalaha yasa ta kawai ta 'karasa da kanta, in dai har zaice kar ta gayawa wani to ai akwai dalilin sa na fa'din hakan, dan haka kawai gara ta 'karasa da "kowa.."
Kenan kawai inja baki na inyi shiru yake nufi in dai na fahimta dai- dai.
Cikin.ranta take ta zancen zucin ita kadai...ta sa'ka wannan ta kwance wannan har dai ta gama yanke shawarar da taga shine mata dai- dai.
Baki ta kya6e tana tura bakin ta gaba, a fili na furta ai na riga na fa'dawa Ammi toh kaima meyasa baka sanar da ni tunda wuri ba....."
" Toh ai kuma Ammi ce, ya ma ya isa yace har ita kar in fa'dawa ne, bayan yasan tafi kowa damuwa da rashin lafiyar tasa.
Yanke wannan hukuncin ne ya sani ta shi da rubutun nata ta wuce bayi, mitsi-mitsi tayi da shi ta kora shi a rariya.
Luf kuwa taji hankalin ta ya kwanta, sai dai wani 6oyayyan farin cikin da ta san duk na taya Ammi murnar tashin 'dan ta ne...matar na matu'kar bata tausayi musamnan idan taga tana zubda hawaye akansa, haka take zama ta tayata kukan itama tana sake rungumar Mufeeda a kirjin ta da tunanin idan akace ita ce a wannan halin ni ya zanji.
Duk lokacin da tayi wannan tunanin bugun zuciyar ta canzawa yake yi, har ga Allah bazata iya juran ganin Feefy cikin wani hali ba sam...ta kan furta a fili cewar..." _Yah Allah ka tsare min ita, Yah Allah ka kare mu, ka bamu kariya, Yah Allah ka jikan iyayena ka tsare min su a duk inda suke, Yah Allah 'daura mu akan makiyan mu ka rabamu da mummunan 'kaddara ka bamu dacewa dunia da lahira..._ "
Addu'ar ta kenan kusan kowani lkc indai akan kanta ne.
Parlor ta dawo dan lokacin ha'dawa Amrah breakfast yayi, tana fitowa tagan ta har yanzu ta maida hankali kan kallon ta tamkar ance mata nan aljannar ta take.
Baki ta kya6e tana girgiza kanta a 6oye...wannan hala bata ga isowar Ammi bane ko mene, ko kuwa tsabar iskanci ne da nuna isa ke damun ta, tunda abu ne mawuyaci tasan mutun ya wuce ta nan parlorn batare da ka ganshi ba tunda ba girma ne da 6angaren wani na sosai ba.
Da ganin Zaitoon Amra sai ta 'dan yi mi'ka tana gyara zama tace " Ke ha'do min tea dan Allah kafin kije gyaran dakin nasa bana so wannan series 'din ya wuce ni ne, sai na gama zan shiga na duba shi naga ma Ammin tasa ta fita..."
Tayi duk wannan dogon bayanin ne batare da ta dubi inda Zaitoon take ba.