Sashe 139
Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Har wani 'kiran ya sake shigo masa ma duk bai lura ba da yake wayar ba 'kara take ba..wa'dancan da ya bawa umarnin bin diddigin sune suka 'kira sun sake 'kira still bai 'daga ba yana can yana tunani.
Shikenan sun kashe min ita.
Shikenan itama ta tafi ta barni.
Abinda ya fara zuwa maza cikin brain kenan bayan ya dawo daga duniyar da ya lula.
Baya yayi ya jingina bayan sa da jikin kujera yana tunani, jikin sa duk yy sanyi, shi kansa bai san meyasa ya za6i uwar ba...bai san yaushe kuma a wani dalili ya za6i Zaitoon kan gudan jinin sa ba.
*Afuwan pls...nasan nayi laifi* 🙏
*Zagi is allowed but HAKURI da UZURI over everything please..* 👌
~Ina son ku...~ 👍
Salmerh ce😘
[9/12/2022, 4:55 am] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕
*( 'Yata ce)*
*Wattpad@*
_Serlmerh-md_
🅿️ *...79*
........" Anty Wlh hankali na ya kasa kwanciya da rashin Zaitoon a gidan nan, Anty tsoro nake ji kar a cutar da su..."
Marwa ta fada tana mai 'ko'karin share hawaye.
Duban ta Anty Madeena take cike da tausayin ta, a hakan ma dan bata san 'ka'k'karfar ala'kar da ke tsakanin ta da Mufeeda ba kenan.."
Anty Madeena ta ayyana hakan cikin ranta.
A fili kuwa ajiyar numfashi tayi tana mai gyara zama tace..." Nima kaina Marwa hankali na ba kwance yake ba, babu mamaki ma.yafi naki hankalin tashi, ina matu'kar fargaban abinda zai biyo bayan wannan tafiya ta Zaitoon...cikin rashin sani tayi tafiyar bayan ta riga ta bar cibiyar 'diyar ta anan ta kuma bar zuciyar ta ita kanta ma anan 'din...ina fargabar inda Zaitoon zata shiga da auren Rayyan akanta...amma babu komai, Insha Allah babu.abinda zai faru, zamu ji alkhairi madadin sharrin da muke gudu bi'iznillah..."
" Allah yasa Anty, Allah yasa muji Alkhairi ba sharri ba..."
" Ameen Ameen..."
Cewar Anty Madeena tana mikewa dan komawa babban palor.
Can 6angaren kuwa tunda suka ga yadda Zaitoon ta sume sai suka she'ke da dariyar mugunta gaba 'daya illah mutum 'daya, babban su ne yace" Ni dai ina da shawara..."
Damar magana aka bashi ya kuwa furta abinda ke ransa.
" A gani na bai kamata ace an kashe ko guda ba aciki ba, domin alamu sun nuna duk suna da muhimmanci a wajan sa, kunga shi uwar ya za6a ita kuma ta bada ranta wa 'yar da alamu ko nawa aka tatsi shegen zai fitar..."
Da wannan shawarar suka rufe zancen nasu, nan suka bar Zaitoon da Mufee cikin mugun yanayi abin tausayi.
Mufeeda kam kuka sosai take tana shiga jikin Zaitoon dake sume dan itama 'karar bindigan ya firgita ta sosai, wani ne ya dawo hannun sa dauke da goran ruwa nan ya bude ya she'ka mata ruwan mai azabar sanyi, a gigice ta farka zata saki kuka taji kukan Mufeeda gefen ta hakan yasa ta waiga gareta da sauri ta janyo ta rungume abar ta tana sakin kukan farin cikin ashe tana raye basu kashe mata ita itaba.
Kuka take tamkar ranta zai fita...haka suka cigaba da zama cikin 'dakin har zuwa yammacin ranar, duk sanda taji an bu'de 'kofa razana take yi da tunanin lokacin raba ta da Feefy ne yazo dan ita bata san da wancan shawarar tasu ba...sai dai kuma ga mamakin ta abinci ka'dai suke basu da ruwa su koma har aka sake yin kwana biyu.
Rayyan da tun da yaji karan harbin nan ya tabbatar na kisan diyar sa ne komai ya kwance masa, bai sake bi ta kan komai ba hatta wayar sa kuwa, da kiraye kiraye suka dame shi ma sai kaseh wayoyin sa yayi baki 'daya.
Bai kuma sanar da kowa ba sai da Ammi ta matsa ne ma da ganin canjin nasa sannan yayi mata bayani atakaice.
Hankalin Ammi tashi yayi sosai, nan ta fara yi masa fada meyasa yayi saurin bada za6in sa, atace ai da rokon su yayi su basu ku'di ko zasu sake su, amma yanzu idan Zaitoon ta tabbatar da cewar da bakin sa aka kashe mata 'diya tasan har abada bazata ta6a yafe masa ba balle ta kwantar da hankali tayi bautar auren ta.
Rayyan dai bai ce da Ammi komai ba yayi shiru dafe da kansa.
Cikin lokaci 'kankani yayi busu busu da shi ya tattara gashi a fuskar sa.
Banda jinin sa dake shirin hawa sama.
Akan wayoyin sa ma sai da Ammi tayi dagaske kafin ya bude su.
Awanni ka'dan bayan bu'dewar wani abu ya fado ransa, da sauri ya janyo waya daya ya fara lalu6o wata number, nan ma yaga ashe sun tara masa missedcall tun ma kafin lkcn da ya kashe wayar.
Bayanin da akai masa kan bin diddigin da ya sa ayi ba 'karamin tayar masa da hankali yayi ba.
Sake jinjinawa yake cikin ransa..nan yasa aka shirya masa troop daga headquater...sai nan ne ma ya dan ji kwarin gwiwa sai dai wani tunani ke sake kashe masa gwiwar nan take.
Har gida suka biyo suka dauke suka wuce.
Traicer ke nuna musu hanyar da ya bada umarnin abi masa kiran da akai masa a wancan lkcn.
Cikin kowani dakika fargabar sa karuwa take, sosai yake kokari wajen ganin ya 6oye abinda ke masa kai kawo a zuci...meyasa sai nan unguwar toh...?"
Ya tambayi kansa.
Bai sake tsinkewa da lamarin ba har sai da yaga motocin sun tsaya gaban wani guest house din Abban su.
Ido ya lumshevya kuma bu'dewa domin tabbatarwa amma still nan din dai yake gani ba wani waje daban ba.
Zaitoon na nan yashe duk ta galabaita, rabon ta da ganin wani halitta a gidan har awanni talatin da hu'du kenan yanzu.
Ta gane hakan ne ta agogon bangon dake manne saman 'dakin da aka ajiye su.
Bata san me ya faru ba, bata kuma san ya suka 'kare da shi ba balle tasan dalilin da yasa ta daina ganin su.
Ashe ya fahimci kutsen da akai masa ne ya sa shi basu umarnin barin gidan cikin gaggawa, yaso su fito gaba 'daya har su Zaitoon amma sai yaran nasa suka yi kuskure basu fito da su Mufeedan ba sai ma sake kullesu da suka yi suka fice daga gidan.
Lokacin da ya fahimci wautar da suka yi ba karamin haushi yaji ba bashi kuma da damar saka su su koma gudun kar ayi ram da su...dole ya hakura bai koma gidan ba kamar yadda bai bada umarnin wani ya koma ba.
Sai dai yasan dole hakan sai yayi wa sirrin sa gi6i.
Gudun kar a zarge shi ya sa cikin lkc kankani ya nemi ticket ya sake komawa can 'kasar da ya fito..can gidan su kuwa babu wanda ma yasan ya dawo Nja ciki kuwa hadda matar sa Marwa.
Kamar cikin mafarki Rayyan ke ganin lamarin, fita suka duk 'karasa jikin gate din da kafafun su.
Sai da aka 6alle gate din kafin suka samu damar shiga dan ko mai maigadin ma bayanan tuni an sallame shi batare da Rayyan yama sani ba, bai san tsawon wani lkc ya bar aikin ba kamar yadda ba'a fasa tura masa kudin albashin sa duk 'karshen wata tare da sayran ma'aikatan sa ba.
Kallo 'daya yayi wa harabar gidan ya tabbatar 'kafa bai jima da 'daukewa cikin ta...sunan da yake ta so ya kawar din kasa tafiya yayi, dole batare da ya shirya ba yahi la66an sa sun motsa wajen furta sunan..." _SULTAAN_ ..."!
Bincike sosai suka yi kafin suka gano dagaske su Zaitoon na cikin gidan nan, sai dai ko alama 'yan iskan basu bar wata kafa da za'a gane su da shi ba.
Sun galabaita sosai dan hatta hannu babu mai iya 'dagawa tsakanin Zaitoon da Mufeeda, yunwa da ishirwa duk sun galabaitar da su.
Wata kakkarfar ajiyar zuciya Rayyan ya sauke da ganin Mufeeda araye ba kamar yadda ya zata ba.
Ganin tan kuma shi ya kara masa karsashi da kuzarin jikin sa.
Zaitoon dai taga mutane amma koka'dan bata gane ko su waye bane balle tasan manufar zuwan su...domin dishi- dishi take gani..cikin zuciyar take iya ayyana abinda take so bakin ta ya furta amma tsabar galabaita bakin nata bazai iya furtawa ba...hakan yasa ta koma ta kwantar da kanta tana jiran 'karasowar mutuwar da ta tabbatar shine ya tunkaro ta a halin yanzu.
'Karshe sai bu'de idanu tayi taci karo da farin POP flat saman kanta sa6anin na can gidan da aka kaisu da yake designed ne.
Rufe ido tayi ta sake budewa dai- dai da tsinkewar da zuciyar ta tayi..." Mufeedah.."!
Ta furta a hankali dan muryar ta baya fita sosai.
" Mufee na..!!
Ta sake maimaitawa.
'Karfin halin mi'kewa zaune tayi duk da yanda take jin hannun ta a 'da'ddaure amma hajan bai rage komai daga niyyar ta ba...fahumtar da tayi cewar zata iya 'dage hannun ya sa ta 'dagowa ta kalla, nan ta fahimci ruwa ake 'kara mata.
Zaune tayi kokarin mikewa tana mai jin ga6o6in jikin ta babu 'karfi sam.
Da Shi ta ci karo zaune ya tsura mata idanu kawai yana duban ta amma bai ce da ita uffan ba....hannun nata ta kalla tana 'ko'karin fizge abin hannun nata, sai anan yayi magana inda yace..." Ki nutsu.."
" Ba dai yanzu ba.."
Ta bashi amsa batare da ta dube shi ba.
" Kina hauka ne?"
" Babu mama ki".
" Baki ganin halin da kk ciki ne..?"
Yayi maganar yana ri'ko hannun nata.
Kuka ta sanya tana mai fizge hannun tace" Wannan ni bai dame ni ba..Yarinya ta ina kuka kaimin ita inaso in ganta yanzu...sake rushewa tayi da kuka tana fa'din wannan wani irin rashin imani ne fisabilillahi? me yarinya ta tai muku? me Mufeeda ta tsare muku ne duk a duniyan nan?..na zauna da ku tsakani na da Allah na na bauta muku batare da na nemi komai daga wajen ku ba amma sakayyar da zaku yi min kenan? Sai ku kashe min yarinya ta? Bacin baku san ta yadda na same ta ba, amana ce fa a waje na, amanar ta aka bani, yarinyar nan marainiya ce, me kuke so in fa'da wa Ubangiji na idan ya tambaye ni akanta...?"
Kuka sosai ta rushe da shi tana mai kifa kanta da ga gwiwoyin ga.