← Book details Binteee Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 154 OF 218

Sashe 154

Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zuwa lokacin na jima da fara jin zuciya ta na tashi hararwa nake son yi amma ya gagare ni gaba 'daya bana jin da'din komai tattare da jiki na.

Kusan ko 'ina na ciwo yake min ji nake kamar a bu'de ciki na akwashe min abinda ke ciki ko zanji da'din jiki na.

Idanu na duk sun yi luhu- luhu ba 'karamin galabaita nayi ba amma hakan bai hana ni fitowa ba lokacin da na tsinkayo muryar Addah ta tazo gidan ba.

Haka na fito cike da 'karfin hali ina 'ka'kalo murmushi na sanyawa fuska ta.

Shigowan ta kenan ko zama bata yi ba na fito lokacin suna tsokanan juna da Azeemah matar Hamma Bukar dake zaune kan tabarma gefen 'dakin Iyami.

Maraba nayi mata sannan na zaga bayan ta ina 'ko'karin kar6ar goyon yaron dake bayan ta duk a kokari na na gudun kar nayi wani laifi.

" Dama nasan abinda ya fito dake kenan".
Tayi maganar tana kunce 'daurin goyon da tayi fuskar ta babu yabo ba fallasa.

'Yar murmsuhi nayi ban kuma fasa kar6ar goyon ba.

Azeemah ce ta kya6e baki sannan taja 'kafar ta ta gyara tace" Ai kuwa dai..ku masu abinda za'a fito domin sa ba, kinga ni ai duk jimawa ta azaune anan banga idanun ta ba saboda bani da jinjiri a hannu na da za'a kar6a...".
" Kema kinsan halin Zaituna ai..sai a hankali in dai akan yara ne.."
Cewar Yaagana.

Daga haka Yaagana bata sake bi ta kan zancen ba zama kawai tayi suka cigaba da hira har Iyami ma tafito suka gaisa tana banka min uwar harara...da alamu tun abinda ya faru da safen nan bai bar zuciyar ta.

Ni kam ban damu ba nayi 'kasa da kaina ina gyarawa yaron rigar jikin sa, watannin sa fa hu'du ne da wasu kwanaki amma idan ka ganshi sai kayi zaton watan sa biyu ne kacan saboda rashin girman jiki.

Yaagana ce ke faman fifita da maficin dake hannun ta ta waigo inda nake tace" gaskiya yau garin 'daure yake akwai zafi, Zaituna cire masa rigar jikin sa ya sha iska da Allah.."
" Toh..." Kawai nace mata sai ta cigaba da fa'din" Ke kam da alamu baki jin zafin nan, cikin gidan ma bazaki daina zama da hijabin nan ba sai kace wata matar limami..ai ni bazan iya ba wallahi?"
Ta 'karashe maganar tana kya6e bakin ta gefe.

Iyami ce tayi saurin kar6e maganar da fa'din" ai in dai wannan ce ko cikin 'dakin ma ba cire hijabi take ba yadda kika san haihuwar ta akayi da su..."

Azeema kuwa cewa tayi Allah dai yasa na gaskiya ne bana munafurci ba..."
Tayi maganar tana kawar da kanta gefe.

Daga nan suka cigaba da hirar su...ni kaina 'karfin hali kawai nayi na zauna a wurin amma wani uban gumi nake ji yana karyo min cikin jiki na, wanda na tabbatar na abu biyu ne, na ciwon dake damu na da kuma zafin da ake zabgawa ni kuma gani da hijabi amma sam banji zan iya cirewa ba sbd sabo.

Salmerh😘
[29/12/2022, 7:48 am] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕
*( 'Yata ce)*

*Wattpad@*
_Serlmerh-md_

🅿️ *...87*

.......Cikin sa'a zuwa yammaci ma sai naji 'kirjin nawa ya sake ni sai dai ciki na dake min mur'da haka kuma na kwana ina fama da shi, da 'kyar ma na 'dan samu na saka wani abu a baki na lokacin sahur sanin da nayi cewar banci wani abin kirki lokacin bu'de baki ba gudun kar azumin ya wahal da ni.

Kusan kwana nayi idanu na biyu, ina jin babu da'di sosai cikin raina, na kan kuma yawaita jin fa'duwar gaba duk da dama ba yau na fara fuskantar irin hakan ba, da jimawa na ta6a yiwa Hamma na maganar yace in rin'ka maimaita _La'ilaha illalallahu wahdahu laa sharikalahu yuhyi wa yumit, wa huwa ala kulli shai'in qadeer.._ a lokacin ban ta6a mantawa ba na kan yawaita yin sa kuma Alhamdulillah na samu sassaucin jin yawan fargabar at times ma sai inji kamar ana bin bayana idan ina tafiya amma yanzu duk hakan babu su, sai dai a yau 'din a yadda na lura fargabar tawa kusan duk bayan wasu mintina 'kara tsanani take yi.

Sosai jiki nake jin raina babu dadi, gashi har a lkcn banajin dadin yanayin ciki na dan bai sake ni gaba 'daya ba....

Ban 'dora duk wannan matsalolin kan komai ba face Dambu da naci, na kuma 'dauki al'kawari cikin zucia ta kan cewa da iznin Allah.. bazan 'kara cin dambu ba koda kuwa shine ka'dai abinda ya rage da zanci a gidan matu'kar ba shine abu na 'karshe da zanci ya min sanadin aljanna ba, ya wahal da ni kuma yana kan wahal da ni 'din ba da wasa ba.

Komin kadan din sa naci baya bari na yin rayuwa cikin natsuwa ta.

Yanzu haka fa zawo nake yi zaryar yi, daga lokacin sahur zuwa yanzu na shiga bayi fin sau hu'du...ka'dan-ka'dan nake ji kamar zazza6i na shirin kamani, ga uban fargaba ga mur'dawar ciki dake 'karuwa min, gefe guda kuma zaryar zuwa bayi gashi banda wani da zai tsaya akaina ya kula ni ko in samu arzikin samun magani sai dai Hamma Bukar ka'dai.

A hakan a daddafe ina yi ina hutawa na samu na kammala ayyuka na na cikin gida da wuri dan nasan yau kam ciro ganyen Iyami babu fashi ne sai dai in gangan jiki na baya tare da numfashi.

Sai dai na kammala komai kafin rana yayi zafi na shirya tafiya jejin da 'yar ledan buhu na da na saba 'debo mata a ciki.

Ina ninke ledar nake ce da Iyami " Iyami na tafi jejin..".

" Adawo lafiya...kuma a tsinko min masu yawa dan kinga ko dabbobi na ma tun jiyan basu samu ciyawa sun ci ba..kuma ki dawo da wuri babu mamaki Goni shigar safia zai yi..."

Da sauri na waigo..." Iyami Goni zai dawo ne dama yau...".
Na tambaya cike da jin dadi duk da cewa ba wani shirin kirki ke tsakani na da shi ba...amma 'dan uwa yafi gaban wasa..kuma ba shakka nayi kewar 'dan uwa na sosai...tunda yasa kai ya tafi can kudancin 'kasa ban 'kara jin ko da labarin sa ba sai yanzun da Iyami tace zai dawo.

Iyami harara ta 6alla min batare da ta bani amsa ba.
Ina 'karasa ninke ledan hannu nake fadin" Allah ya dawo da shi lafia..Allah ya sa ya kawo mana tsarabar kankana..."
" Da yake 'kanin ubanki ne ai dole kice haka..."

Yadda naji suka da 'dacin wannan zagi na Iyami bazan iya kwatantashi ba.
Sosai abin ya min ciwo.

Shin menene laifin magana ta..?
Ko kuwa laifi ne dan furta hakan ga 'dan uwa na jini na wanda muke uba 'daya da shi.

Bansan meyasa naji ciki na ya mur'da daidai da wanzuwar 6acin da naji zucia ta tayi ba.

Ledar nayi saurin ajiyewa na 'dauki buta da sauri na nufi bayi domin hakan nafi bukata a dai- dai wannan lokaci.

Inaso ina kuka, amma sam ya kasa samuwa gare ni, hawaye nake so in fidda ko zai tafi min da ba'kin cikin da ke cikin zucia ta amma ya gagare ni.

Hakan yasa nake jin wani 'daci da bugawar zucia na daban ba irin wanda nake ji a safiyar ranar ba.

Bayan wani 'dan lokaci na fito daga bayin...Iyami baki ta kya6e ta kawar da kanta gefe tamkar bata fahimci halin da nake ciki ba.

Gaban ta na nufa ina 'dan ciccije baki na saboda mur'dawar da ciki na ke min...yau ko Hamma bamu gaisa ba saboda har yanzun bai shigo gidan namu ba, Abban mu kuwa tuni ya bar gida...

" Iyami dan Allah ko Flagyl babu a dakin ki ne insha wlh ciki na yaki daina ciwo har yanzu, wanda Hamma ya sai min jiyan kuma duk na shanye..."

" Nima bani da shi..."
Ta bani amsar da bazan iya ce ga gaskiyar ta.

Tsaye na mike ina yamitsa fuska ta nace..." Toh shi kenan zan wuce jejin.."
" Ki dai tabbatar kin ciro min mai kyau kuma da yawa nake so dan nasan halin muguntar ki yanzu sai ki kwaso 'dan ka'dan..dayawa zaki 'debo ina sake gaya miki"

" Toh Iyami" nace ina juyawa.

Khausar dake can tana wasa na kalla nace" Khausar dan Allah ki 'dan raka ni mana...?"
Kafa'da ta noke tana mai cigaba da wasan ta tamkar wata 'yar goye.
Yayin da Iyami ta banka min uwar harara sannan tace " Bata zuwa!..salon kije ki mammake min ita ko...munafuka ai duk nasan halin muguntar ki...maza kama hanya ki wuce kafin in sa6a mk..shegiya dangin mayu..".

'Kasa nayi da kaina na kama hanyar fita zucia ta cike da wasi- wasi, wani abu nace min inje jejin yayin da wata zuciyar nace min kawai inje in 'debo mata rayuwa ce ai.

Tafiya nake amma sai nake ji kamar ana 'da'd'daure ni, hatta 'kafafuna rawa suke min saboda tsananin fargabar dana ke ciki ga kuma ciki na da ya 'ki sarara min.

A haka na tunkari jejin..idan na 'dan yi tafiya sai in samu wuri in zauna dan hutawa, a hankali nake sau'ke numfashi, da ace inada gata nasan da baza'a ta6a tura ni jejin nan ba musamman saboda halin da nake ciki, kulawa nake da bu'kata amma nasan banda Hamma na babu mai bani wannan kulawar a yanzu, sosai nake ji da ganin 'kokarin sa kuwa, shiyasa ma ba ko wani lokaci nake kai masa 'korafin damuwa ta ba saboda kar 'dawainiyar tayi masa yawa, ga ta gidan sa ga ta Iyami ga kuma tawa, Hamma na ba 'karamin 'kokari yake yi ba wajen sau'ke nauyin ahalin sa ba...dan haka akan wannan ciwon cikin bazan 'daga hankalin sa ba.

Lokaci sosai na 6ata a hanya domin kafin ma na isa rana ya fito sosai ya haske ko'ina...da yake lokaci ne na Ramadan hakan yasa harkoki da dama suka ragu musamman da safiya ko kasuwanci ma sai da rana aka fiye fara shi zuwa yammaci har izuwa dare...dalilin kenan da ya sanya 'dai'daikun mutane ne zaka ga gani suke gilmawa, garin shiru babu wani hayaniya da zai 'daga maka hankali.
Chapter 154 · 0% Book details