Sashe 16
Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
*******
Zama yayi kasan Carpet gefen Hajiya da ke zaune bisa kujera mai zaman mutun biyu tana duban sa da mamaki tace.." Miye hakan Shahid naga ka wani Zauna kasa tamkar wani ba'ko ko me neman gafara".
" Hajiya mgana nake so muyi.."
" Shine sai ka zauna a 'kasa.."
" Zan fi jin dadin neman alfarmar ta hakan ne Hajiya..".
Gyara zama tayi tana me maida dukkan hankalin ta gareshi.." Ina jin ka toh meyafaru?".
Shiru ne ya dan biyo baya fargaba yake shin Hajiya zata kar6i maganar da hannu bibbiyu ko akasin hakan, yasan abu ne mai wahala ta kar6a masa cikin sauqi shi kuma amincewar ta kadai yake bukata...gyara zama yi tamkar wani abu na tsungulin sa yayin da Hajiya Talatu ta kasa dauke idanun ta akan sa tana jira taji mecece alfarmar dayake nema din.
Da kyar yayi gathering courage wajen fara harhado abinda ke mintsinan zuciyar sa.
" Hajiya kin kasance min ne tamkar haske a cikin rayuwa ta, kin so ni kin kaunace ni kika nuna min gata, kika zame min mahaifiya a lokacin da na rasa tawa, bani da bakin gode miki illa inta miki addu'a muddin raina..."
Ajiyan numfashi nannauya Hajiya ta sauke ga dukkan alamu maganganun nasa sun ta6o ranta ne. " Allah ya gafartawa Mahaifiyar ka ya jikan dukkan muslumi".
" Amin "yace a hankali.
" Ban fahimci me kake shirin fada min ba Shahid kayi min bayani dalla dalla..Insha Allahu ni mai tsaya maka ce akan komai matukar be fi karfi na ba dan bana da burin da ya wuce ganin ka cikin farin ciki".
" Nagode sosai Hajiya, a yanzu amincewar ki kadai nake bukata ina so a daura min aure ne karshen satin nan..."
" Aure !"
Ta fada cike da mamakin sa.
" Aure Shahid cikin sati guda kamar ta wasan yara..?"
" Hajiya abin ne yazo min nima a bazata, ban ta6a kawo hakan cikin lokacin nan ba.."
Sake gyara zama Hajiya tayi idanun ta kur akan sa, haka kawai sai taji tsoro ya tsarga mata.
Tsoron abinda zuciyar ta ta darsa mata game da maganganun Shahid din taji.
Kuma in ba dai hakan bane dagaske menene dalilin da zai sa ya nemi a daura masa aure cikin kwanakin da suka gaza sati daya tak.
" Dan Allah kai min bayani sosai Shahid kar ka barni cikin duhu na kasa jin kwanciyar hankali, shin iyayen yarinyar ne suka matsa akan sai an yi hakan..?"
" a a Hajiya..?"
" Toh me yasa? Me kake tunani ko tsoro da zai ka tunanin yin aure cikin gaggawa haka? aure fa ba wasa bane Shahid Su waye iyayen yarinyar ina ne gidan su?"
_Tirkashi!..inda gizo ke sakar kenan._
Cewar Adam cikin zuciyar sa, domin bashi da amsoshin dukkan tambayoyin Hajiyan ko 'kwara daya.
Sai dai yana ga a wannan bigiren 6oye-6oye bashi da wani amfani dole ne ya fito fili ya bayyanawa Hajiyan koma menene.
Cikin kwantar da murya cike da fargaban yadda Hajiya zata kar6i zancen ya fara fadin" Hajiya ita bakowa bace ba kuma wata ba, kuma batada wani da zata fito ta nuna da sunan nata ne a yanzu haka...ni dai kawai na tsinci zuciya ta ne cikin tsananin so da kaunar ta..dan Allah Hajiya kar kice a a kar ki hanani damar mallakan ta..."
Bata jira ya karasa maganar ba ma cike da kaguwa tace.." Wacece haka ne Shahid kar ka zauce akan mace har haka mana...fada min wacece?"
" ZAITOON ce!..."
"Zaitun?..wace Zaitun kake nufi?"
Hajiya ta maimaita sunan gami da sake tambayar sa cike da son kore shakkun ta.
" Wacce ke aiki a shagon ki..."
_Tas...tass...tasss_ karan saukar marin da Hajiya ta sauke kan fuskar sa kenan batare ma da ta jira taji karshen zancen nasa ba, a karo na farko tun tasowar sa yau Hajiya ta maresa har mari uku lokaci gada..ko da wasa Hajiya bata ta6a daga masa ko murya ba balle ta kai hannu da sunan dukan sa, sai gashi dalilin soyayyar sa yau ta mare shi.
"..Baka da hankali..!"
Fadin Hajiyar tana me sauke huci da alamu ranta yakai kololuwa ne wajen 6aci.
" Ashe baka da wayo Shaheed bansani ba?..ko kunya ta baka ji? ka dubi tsabar idanu na ka wani ce min Zaitoon? duk duniyan nan baka ga 'yan mata bane sai Zaitun?"
Adam dake zaune har yanzun motsin kirki ya kasa iyawa hatta marin da Hajiya ta sauqe masa bai ko daga hannu yakai wajen ba balle ya nuna alamun sun ratsa shi.
Ciwo da tsoron da suka taru suka haifar wa zuciyar sa gudu mai cike da razani shine agaban sa..tsoron sa daya kar Hajiya ta kafe kan bakan ta na kin auren sa da Zaitun, bai ta6a tunani ko jin tsoron rasa abu a duniya ba sai yanzu akan Zaitun yake kuma zaune gaban Hajiya tana sauke masa ruwan bala'i..da gaske Hajiya bazata bar sa ya auri Zaitun ba kenan duba da irin muggan kalaman da take furtawa.
Bai 'dago ya kalle ta ba dan baya kaunar ganin 6acin ran Hajiya dai-dai da kwayar zarra, amma dole ne a yau ya nuna mata tsananin bukatar sa ga auren yarinyar.
"..Haji..ya dan girman Allah kar ki ce a a wlh ina kaunar Zaitun ina kuma tausaya mata, Hajiya kowa fa da kalan tashi kaddarar kowa da hanyar da Allah yake jarabtan sa, Zaitun a zahiri kamilalliya ce ba ta da wani aibu ko mummunan halin da zaisa ki qi kar6an ta matsayin matar 'danki, wlh Hajiya ban duban wata mace da suna soyayya ba sai Zaitun ita kadai nake so nake kuma da burin karasa rayuwa ta da ita...."
" Kayi min shiru dan Allah, kayi min shiru Shahid..."
Ta daka masa tsawan da ya tilasta shi yin shiru batare da ya shirya ba kamar yadda Hajiya ta bukata.
" Zaitun dai! Zaitun dai!!, ko ba Zaitun dana sani me min aiki ba? Zaitun wacce ke goyon yarinyar da babu wanda yasan waye ubanta, Zaitun da kowa ya riga yasan ba yarinyar kirki ba ce? Zaitun da ke rayuwa ita kadai babu dangin iya babu na baba duk kuwa da karancin shekarun ta? Zaitun da ta shafe kwanaki da dama tana kwanan layi tamkar mahaukaciya, Zaitun dai da tazo min shago kamar almajira..saboda tausayin ta na bata aiki?..ita ce Shahid? Itace kai Shahid Adam Jibrin 'dana dana raina da hannu na zaka dube ni batare da ko 'dar ba kace min ita kake so in aura maka? Mata sun kare ne a duniya Shahid?"
Hajiya ta karasa maganar tana kwalalo idanu akan Adam dake zaune gaban ta.
Shikan sa jikin sanyi ya karayi, ta ya zai iya kare Zaitun wajen Hajiyan bayan duk wadannan bayan da suka kasance akan ta daba bakin Hajiyar.
Hannun ta duka biyu takai bayan ta tana sakin huci me zafi gami da juya masa baya tana girgiza kai tace..." bana tunanin haka nan ta barka Shahid bazan ga laifin ka ba, tashi ka ban wuri".
" Hajiya...!"
" tashi ka fice min nace".
Ta daka masa tsawan da yasa gaba daya 'dakin amsawa.
Haka nan ya tashi ya fice yana jin kafafun sa tamkar bazasu iya daukan sa ba.
Ranar haka ya yini ya kwana bai ko sake leko waje ba wanda hakan yayi daidai da cikan kwanaki hudu kenan rabon da Zaitun ta sashi a idanun ta.
_Salmerh_ 😘
[20/9/2022, 12:32 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE* 💕
*( 'Yata ce)*
*Salmerh MD*
🅿️ *...10*
_"...Assalamu Alaikum"_
Zaitun dake zaune tana kokarin juye musu taliyar da ta tafasa a kettle kunnuwan ta suka jiyo tashin sallamar da ya taho mata da bugun zuciya...dan tana jiyo sallamar gaban ta ya fa'di sai kuma ta kasa amsawa duk da bata san da wacce Hajiyan tazo ba da yake gidan mallakin ta ne, gashi kuma itan ma'aikaciyar ta ne, duk da haka sai taji ta kasa natsuwa da zuwan Hajiyan tuni ma cire batun aiki a lissafin ta mafitar da Adam yace zai nemo musu shine kullun cikin zuciyar ta dama.
Hajja ce ta fito jin sallamar Hajiyan inda ta amsa cike da fara'a mai tafe da fadanci tana kokarin bawa Hajiyan wajen zama.
Kokadan bazaka dubi fuskan Hajiyan kayi tunanin akwai wani abu cikin ranta ba...ganin da tayi Hajja na shirin bata wajen zama ne yasa tai saurin dakatar da ita da fadin " a a Hajja dama nazo wajen Zaitun ne".
" aww inajin tana ciki ai ki shiga mana..."
Cewar Hajja tana me kokarin komawa dakin ta da fatan Allah yasa kudin haya Zaitun ta kasa biya aka kawo mata Notice har gida.