Sashe 100
Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Allah ya sani yanzu kam zuciyar ta bazata iya 'daukan wani mummunan abu da zai yiwa Zaitun ba..mutun da agaban idanun ta ma bai ji kunyar hantarar ta ba taya zata iya kwantar da hankalin ta alhali tasan 'diyar ta na tare da shi kuma ba imani ne da shi ba.
'kila ma ya kashe min yarinya..wannan tunanin da tayi ne yasa ta tashi a zabure ta zauna, kukan ta sai ya kasa tsayawa, tashi tayi ta koma bakin window ta tsaya ta na 'karewa harabar gidan kallo..tabbas babu motar sa, gate 'din gidan ta kurawa idanu tana addu'ar taga shigowar su cikin gidan yanzun nan.
Ai kam bata bar bakin windown ba har lokacin da taji 'karar horn aka wangale gate ya bude, Motar Rayyan ta shigo...madadin taji sanyi a aranta a a.
Saima sake zare idanu da ta yi tabi motar da idanu har zuwa inda yayi parking.
'Kur take kallon motar bb ko 'kyaftawa ganin fitowar Rayyan rungume da yarinyar ne ya sanya ta sakin ajiyar numfashi me sanyi...sai alokacin ta dan ji hankin ta ya kwanta.
Rayyan kuwa daga asbiti be tsaya ko'ina ba sai Pharmacy ya sayo komai da aka rubuta masa sannan ya kamo hanyar gida har a lokacin kuma Feefy na kwance saman kafa'dar sa.
Zaitoon na jin muryar sa ta taso da sauri ta fito ganin sa rungume da Feefy ya sanya ta kasa barin bakin 'kofar balle ta 'karaso..shi kam duba 'daya kawai yayi mata ya 'dauke kansa bai sake kallon inda take ba sai ma baki daya kya6e domin kallo 'daya idan kayi mata zaka fahimci tsananin damuwa da tashin hankalin da take ciki...cikin zuciyar sa ya furta" kamar akanta aka fara haihuwa.
'karamin tsaki ya saki wanda ya fito fili, maganin hannun sa ya fara sau'kewa hango Ammi na sau'kowa daga saman bene...a hankali taga ya sau'ko da Moopy ma dake saman kafa'dar sa ya kwantar da ita har da gyara mata kwanciyar cike da kulawa wanda hakan yayi dai- dai da isowar Ammi tsakiyar parlorn hango Ammin ya sanya itama Zaitoon jin 'kwarin gwiwar 'karasowa da sauri dan ganin fuskar 'diyar ta, ammavsaivtavkasa 'karasawa, sam ji tayi bata amince da shi ba har cikin zuciyar ta.
Kuma duk wannan tattali da ya nuna wa yarinyar bata sa aka ba dan aganin ta duk na ganin ido ne...dama dai wani daban ne yai mata raunin da zata iya yadda da shi amma fa dakan sa ya fa'dar da Mufee har bakin ta sai da ya fashe taya zata yadda da shi.
Shi kam maganin kawai ya mi'kawa Ammi ya juya ya fice abinsa batare da ya jira ko shi 'din ya furta wani abin ba.
Ammi murmushi tayi kawai dan tasan dalilin sa na yin hakan be wuci yace ta shiga rayuwar sa ta tilasta shi yin abinda bai yi niyya bane kawai.
Zaitoon na 'karasowa ta isa gaban Moopy ta rungume ta tana sakin ajiyan zuciya.
A hankali ta sumbaci goshin ta tana shafa kwantaccan gashin dake goshin nata take murmushi ta furta " Ammi kinga bakin ma kumburin ya fara sau'ka kuma ba wani zazza6i da ya kamata...".
Ta 'karasa maganar tana sakin murmushin da 'karara zaka fahimci na jin da'di ne.
Ammi ma murmushin tayi kawai cikin ranta tace" ya sau'ka dai zazza6in"
Yayin da a fili kuwa cewa tayi" ai ina ga an bata magani ko kuma allura suka yi mata sai Allah"
Tana fa'din hakan ne da shirin zaunawa sai bayan ta zauna sannan ta ciro magungunan daga ledar su tace" Ki barta tayi baccin ta toh idan ta tashi sai kiyi mata wanka sai abata magungunan nata ko.."
" Toh Ammi"
Ta furta tana mi'kewa tsaye tace" bari in kaita ciki.."
" A a barta anan kar kuma yawan jagwalgwalon ya yanke mata baccin ta.."
Zaitun bata yi musu ba ta koma ta zauna tana sake gyara rigar dake jikin Zaitoon wanda yake 'ko'karin rufe mata fuska, duk rigar ta 6aci da jini da kuma yawun kukan ta tasha hatta jikin Rayyan ma taga yayi stained da jirwayin jinin wanda take kyautata zaton abinda ya sake hassala shi kenan ya fice da hanzari.
Ita kam lokaci- lokaci take juyawa ta kalli Feefy, Allah- Allah take yarinyar ta tashi domin sam rigar dake jikin tan ya tsaye mata arai, bata barin yarinyar ta cikin datti ko 'kazanta ko da wasa shiyasa hankalin ta ya kasa barin kanta.
Zaune take daga gefen ta zuba mata idanu Ammi kuwa hankalin ta na kan T.V komin 'kan'kantan abu ya zo jikin Moopyn da sauri zaki ga ta ka'de shi ko kuma ta hure shi... a kullum 'kaunar 'diyar ta sake ninkuwa mata yake cikin zuciyar ta...Allah ya sani dai- dai da 'kwayar zarra bata 'kaunar abinda zai raba ta da ita shiyasa ko a wancan lokacin ma bata bari rabuwar su ta ci galaba akanta ba, duk yadda aka so raba su sam Zaitoon taki bada damar haka.
Tun a wancan lokacin ta hana wa'dannan mutanen ganin ta, lokacin da jami'an tsaro suka zo ma tana gefe can 6oye tana duban su amma sai ta kasa 'daga 'kafafun ta ta bayyana gaban su gani take tamkar 'kwace mata 'diyar da uwar ta tayi mata kyautan ta zasu yi...tana da komai da zai iya sada ta da asalin dangin Moopy amma tun ranar da mahifiyar ta ta bata abubuwan har yau bata ta6a ko tunanin 'dago su ta duba ba balle har ta yi wani yun'kuri akai...'ji take tamkar da 'kaunar Moopy aka 'dura mata jinin jikin ta..bata ta6a 'kaunar wani abu irin hakan ba...shiyasa duk wanda ya dube su baya ta6a yin tunanin ba itace mahaifiyar Feefyn ba ita kuwa ko ajikin ta..abu 'daya ne bata jura idan akace mata shegiya mara asali..takan yi iya yinta wurin 'kure masifar ta wajen 'kwatar wa 'diyar ta 'yanci ta kuma 'karyata duk wanda ya furta hakan.
Tana kuka zaki ji tana fa'din " ni yarinya ta ba shegiya bace..tana da gatan ta.
Hatta Rayyan dake aibanta ta da wannan sunan wasu lokutan ji take tamkar ta shake masa wuya sbd takaicin sa..a 'kira ta 'yar iska, mara tarbiya mai yawon banza, a 'kira 'diyar ta shegiya 'yar gaba da fatiha duk wa'dannan zagin ba ba'kinta bane in da sabo ma ta riga ta saba, sam nata zagin baya yi mata ciwo saboda tasan bata aikata ba, amma na Mufeedan idan akayi ji take tamkar ta ciro zuciyar ta daga 'kirjin ta saboda azalzalar da yake yi mata.
Salmerh😘
[25/10/2022, 11:35 am] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕
*( 'Yata ce)*
Wattpad@
Serlmerh-md
🅿️ *...59*
........Koda ranar Monday tayi ba'a samu damar mi'ka Mufeeda skul 'din ba kamar yadda suka tsara sbd yanayin jikin ta, hakan yasa Ammi tace abari sai ranar Tuesday kawai akaita that's washegari kenan.
Ai kuwa washegarin gudun karya manta ma Ammi da kanta ta 'kira wayar shi da sassafe ta tunatas da shi.
Sam ba haka yaso ba amma da yake Ammi ta dage sai shi da kansa zai kai yarinyar ya sanya shi amincewa domin bashi hujja ko ikon yin jayayya da ita.
7:02am ya fito cikin shirin sa, sai da ya duba Amrah ya tabbatar babu wata matsala kafin ya fito zuwa sashen Ammi.
Shirye ya tadda su duk a Palorn 'kasa, Ammi da Mufee zaune gefen ta tasha wanka cikin wata ha'daddiyar shiga sai Zaitun dake daura da su fuskar ta babu yabo babu fallasa.
Ammi ce ta amsa sallamar tashi yayin da Zaitoon ta amsa ciki- ciki ahakan ma sbd kawai sau'ke nauyin addini ne amma ko kallo bai ishe ta ba har a zuciyar ta.
Taso kawar da kai daga kallon sa amma tuna cewa a yau shi ke da ragamar rayuwar su ya sanya ta dole maido da hankalin ta gare shi.
Gaishe shi tayi a takaice Rayyan kam bai ma amsa ba illah kallon ta da yayi ya kuma 'dauke kansa, tasan amsar kenan matukar baiyi niyyan yin magana da bakin sa ba.
" Shikenan kuje toh.. idan yaso duk abinda ake ciki naji labari daga bakin Zaitoon idan ta dawo..."
Ammi ce ta fa'di hakan bayan sun gama gaisawa da shi.
Har ya mi'ke sai kuma ya dubi Ammi cikin hanzari, yana ha'de gira yace..." Wace Zaitoon kuma Ammi...?"
" ina nufin uwar Mufeeda, idan baka santa ba gata nan gefe na toh 'dan nema kawai...".
Cewar Ammi a 'dan kufule.
Sau 'daya ya kalle ta ya wani 'dauke kansa yana sake ha'de rai sosai" wai Ammi hadda ita za'a ne? Gaskia ni bazan kuma dawowa gida dan kawai in sau'ke ta ba tayi zaman ta tunda ba cinye mata 'diyar zanyi ba..."
Ya fa'da ransa 6acin rai na son taso masa yana me kama hannun Mufeeda dake gaban Ammi.
Mufeeda bata yi gardamar binsa ba dan Ammi ta gama lalla6an ta tun 'dazun akan zasu je da Mammyn ta da Uncle Rayyan skul a siya mata kayan wasa.
Sai da Mufeeda taga suna shirin barin Palorn ne kafin ta dan waigo ganin Zaitoon a zaune yasa ta fara 'kiran sunan ta tana shirin kya6e baki.
Fahimtar hakan da Rayyan yayi ya sashi 'dago ta cak zuwa gefen kafa'dar sa ya rungume ta yana fa'din " shiii"...suka cigaba da tafiyar.
Zaitoon kam mutuwar zaune tayi, kamar wasa kamar gaske take ganin fitar Rayyan da Mufeeda su ka'dai daga gida, motsin kirki ma kasawa tayi sbd al'ajab 'din maganar sa.
Rayyan kuwa bai zame ko'ina ba sai motar sa da aka ware masa zai fita da ita, ciki ya sanya Mufeeda sai dai yana ajiye ta tana sake 'kan'kame shi da sakin kukan da bai fito mata tun 'dazun ba...tana 'kiran" Mammi.."
Rasa yadda zai yi da ita ma yayi.
Da farko iska ya hura abakin sa yana jin tamkar ya maida musu yarinyar ciki, shi bazai iya raino haka nan kawai babu gaira ba dalili ba.
Haushin wannan lamari duk ya tsaye masa a zuci, meyasa Ammi zata tilasta lallai sai shi bacin ga mutane da yawa da zasu iya sada yarinyar da skul ba lallai sai shi da kansa ba.
Idan kuma tafiso na gida ya kaita ina laifin Sultan toh amma wai sai shi...abinda ko Marwa ma aka bawa dama zata iya mi'ka ta.