← Book details Binteee Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 218

Sashe 53

Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

.......Cigaba tayi da duba sauran sakonnin da suka gama tururuwar shigowa cikin wayar tata.

Wata me suna Ameera ce ta tura mata" _Mrs RM baki yi bacci ba_ ...?"
Bata kula ba sai da ta 'dan 'dauki lokaci cikin wani group bayan ta gama nazartan duk abonda ke wakana cikin group 'din kafin ta fito.
Amsa ta turawa Ameeran da fa'din
".. _Wlh Ameera ban yi ba..ina dai niyya, ya labari_ ..?"
" _Shiru ne fa 'kawata, ya Babyn ki_ ..?"
" _Yana 'kalau, yana can 'dakin sa..."_
Ta bata amsar in I don't care manner.
Idanu Ameerah ta zaro a zahiri ta kuma tura mata emoji exactly yadda tayi da idanun ta sannan ta 'kara da rubuta " ' _kawata 'dakin sa fa kika ce, ke kuma fa_ ..?"
'Dan ha'de rai Amrah tayi tana bawa Ameeran amsa da fa'din.." _Nima nawa 'dakin nake..mun yi fa'da ne..."!_
Dariya Ameeran tayi har a fili daga inda take.
" Shegiya tawan, wayon dai har yau babu, ko waye yace mata ana haka a wannan zamanin oho ...ta furta a fili.
Sai kuma ta tura mata emojin daria.." 😂... _fa'da da Babyn naki mrs Rayyan_ ....?".
" _Ki bari kawai Ameera 'dan yawa ne wlh kina ganin sa, sai uban fushi, rashin ha'kuri da zafin rai..."_
" _Kai.._ 😱
_" Allah kuwa, masife ni yayi fa dan kawai ban yi wanka akan kari ba ko ina ruwan sa oho..._ "
Ta 'karashe da 'kya6e baki.
" _Kai 'kawata ke ma dai yawar gareki wani lokacin yasin.."_
Cewar Ameerah inda ta turo mata tana murmushi.
Tiryan- tiryan ta labarta mata yadda suka yi kaf da Rayyan hadda wanda ba ma ranar ya faru ba, da abinda ma bai kamata ta sani ba duk ta sanar da ita, Ameera nata mata daria da ganin wautar ta, ita bata wani ga abin fushi anan ba ma 'karshe dai haka suka rabu ba tare da wata 'kwakkwarar magana ba a tsakanin su.

Ameera ita har ga Allah abin dadi yai mata...ta jima tana so da begen Rayyan 'din amma ta rasa ko wata iriyar damar ganin sa ma balle magana da shi, ita kuma a yadda take jin zuciyar ta bata da kwarin gwiwar iya fitowa fili ta bayyana masa kudurin ta, baya ga haka ma Amran babbar kawarta ce, kawancen su kuma yafara ne tun suna da 'kananun shekaru bazata iya cin amanar ta ba shiyasa ta hakura kawai ta barwa Allah komai, sai dai daidai da rana guda bata ta6a bata shawara game da zamantakewar auren ta ba, duk da tasan iriyar tarin ta6ara da Amran ke tafkawa amma hakan bai sa ta 'dora ta da hanya ko sau 'daya ba.

Tun fitar Amrah ya ja wata doguwar tsaki kuma har a lokacin bugun zuciyar sa bai dai dai ta ba, Safaa is his lovely sister which atimes take iya zame mishi tamkar aboki, ya shaku da ita fiye da duk sauran sisters 'din sa duk da yake ba mai sakewa bane shi, amma hakan bai hana Safaa shiga jikin sa har suka saba ba, hatta Sultan da yake namiji basu shaku da shi kamar da Safaa ba, she is very friendly with a genuine personality, tana da hakuri sosai gata da fara'a ga mugun 'kaunar ahalin ta da Allah ya 'daura mata nd that's what makes her leave her footprint still in his heart...he adore nd missed her alots...
A fili ya furta Allah ya gafarta miki ya 'kara haskaka kabarin ki...Ameeen..."
Wayar sa ya 'dago ya 'kira Ammi ya sanar da ita yaje ya kuma tarar da su lafiya.

Murmushi Ammi tayi ba tare da wani jin nauyi ba tace da shi " Thank u..."
Bata tsawaita ba, domin daga jin yanayin muryar sa tasan a dame yake duk da bata san dalili ba amma tana kyautata zaton akan aikan da tai mishi ne...ko ma ba itan bace kuwa tasan ba lallai ne ya fa'da mata ba ko da ta tambaye shi dan tasan halin sa sarai da za6an ri'ke komin sa a zuciyar sa, bai fiye son yana tarayya kan wani abu nasa da ya shafe shi da wani ba, mugun son privacy ne da shi hatta ita da ta haife shi bakomai yake iya tattaunawa da ita ba, abubuwa da yawa sai dai ya aikata abinsa batare da tasani ba, wanda Allah yasa taji labari shi take ji wanda bata ji ba kuwa ya wuce ta kenan, tasan wannan halayyar a wajen ta da ma mahaifin sa ya 'debo shiyasa abin ya.kama.zuciyar sa sosai, domin ita har mahaifinsa kusan duk suna da wannan 'dabi'ar amma zuwa yanzu ta fahimci Rayyan ya ninka nata halayyar sau babu adadi.

Yayin da daga 6angaren Rayyan har ga Allah aiken Ammi bai 6ata ransa kamar yadda Amrah ta 6ata masa ba...

Ita kanta Ammi tasan tsakanin su dama bb wata doguwar hira shiyasa bata tsawaita ba, ranar da yaso da kansa yake mata hirar ranar da kuwa bai ga dama ba maganar bakin sa ma sai yaso ake ji.

Sai dai duk da haka sosai yake son mahaifiyar sa da duk 'yan uwan sa sbd sune ka'dai yake da su...ko miye kuwa da Ammi ta bashi umarni tace masa abu kaza zakayi koda baya son abin bazaka ta6a ji ko ganin yayi musu ba, in ya ga dama ko a fuska bazaka ga alamun rashin amincewar zuciyar sa ga abin ba, sai dai wani lokaci yabi Ammin da kallo bacin hkn kuma amincewar sa ne zai biyo baya.

Bai ta6a yi mata musu ba, da kanta take fahimtar komin sa daga cikin idanun sa, wanda idan ta fahimci kamar zata cutar da shine ma sai ita ta janye nata kudurin in kuwa tasan ba ze cutar da shi ba hk take barin sa kawai daga 'karshe kuma alfanun abin zai gani da farin ciki yake 'karewa.

Ko lokacin da zai fara Degree 'din sa, ABU Zaria ya so yi har ransa amma Ammi tace sam karatun likitanci take so yayi kuma ma a wajen 'kasar nan, har ga Allah baya ra'ayi, ya so ya karanci fannin business ne kawai tunda a ciki suka taso suka ga mahaifin su har ya bar dunia kuma sana'ar sa kenan.
Sau 'daya kawai Rayyan ya dube ta ba tare da musun komai ba kawai ya amince...amma cikin wannan kallon ta fahimci ba ya ra'ayi basarwa tayi amma sarai tasan ba ra'ayin sa kenan ba biyayya ce kawai yy mata, ba burinta ta kuntatawa 'diyoyin ta ba, bata fatan dai dai da rana guda ta tauye hakkin wani daga cikin su amma wannan karan bata jin zata iya janyewa daga kudurin ta, sai tayi fatan Allah yasa ya kasance shine hanyar alkhairin sa a rayuwa.

Da wannan tunanin tayi ta sa masa albarka tare da nuna tsantsar farin cikin ta da amincewar san gami da alfahari da shi...ta kuma gode Allah dan tasan ba kowa ke dacen samun 'da irin sa ba...' da mai biyayya da juriya da jajircewa wanda baya ta6a son ganin 6acin rai saman fuskar mahaifan sa.

Cikin sa'a kuma tunda ya fara karatun bai samu matsalar komai ba, ya kuma bada hankali yayi karatun sa fiye ma da yadda ita tayi tsammani, daga 'karashe da riba biyu ya fita kowa na taya sa farin ciki..shikan sa farin cikin yayi.

Tsaki yaja a bayyane ganin yadda Amrah ta bar masa gadon sa a hargitse tayi ficewar ta, ya rasa wace iriyar mutun ce Amrah a duniyan nan.
Ace komai ita sai an mata shi, ko an saka tayi sannan zata yi.
Da kansa ya gyara komai sannan ya koma bathroom ya 'dauro alwala bayan ya gama uzurin sa ya fito sai da yayi shafa'i da wutri kafin yabi lafiyar gado, zuciyar sa cike taf da tunani kala- kala.

'Bangaren Zaitun ma kusan haka ne, tamkar dai Rayyan, tunani ne fal a zuciyar ta, bata kuma san cewa an shigo 'dakin bama balle tayi tunanin waye wanda ya shigo, da nisa can ta bayar da hankali ga mahalicci dan neman cikar burin ta, sai da ta idar ta shafa addu'ar ta kafin ta fahimci ba'kon 'kamshi ya gama mamayar 'dakin.

Dube- dube ta 'danyi cike da firgici lokaci guda abinda ya ta6a faruwa tsakanin ta baban Abdul ya dawo mata, sa6anin wancan wannan karan bata ga alamun tunanin ta zai.iya zama.gaskia ba, musamman da yake wannan labilen a sakale yake jikin wani karfe ba ta yadda za'a yi mutun ya 6oye batare da ta ga mai shi ba, sannan 'kofa a rufe yake.kamar yadda ta bar shi.

Bata tsawaita tunanin ba kawai ta basar da tunanin ba mamaki hancin tane kawai ya jiyo mata kamshin.

Mufee ta gyarawa kwanciya sannan tayi mata addu'a ta shafe ta daga baya tayi nata ta shafa itama ta kwanta da niyyan bacci amma sam baccin ya gagare ta.
Tunani kala- kala ke dawo mata, a shekara guda 'daya baya idan ance mata zata tsinci kanta cikin irin rayuwar da take yanzu tsab zata karyata, sai gashi kamar wasa kamar cikin mafarki ta shiga yanayi mabanbanta da bata ta6a tsammanin tsintan kanta cikin su ba, fatan ta Allah ya bata ikon jurewa, ya kara mata karfin gwiwa.

Sai bayan kwanaki biyar da zuwan su gidan kafin hajiyar gidan ta dawo daga Abuja wajen taron da taje, Zaitun bata ma sani ba ni..dan bata fitowa daga 'dakin su tsabar yadda take shiga damuwa da son kusanta kanta ga Allah har sallar walaha ta fara cikin 'yan kwanakin,..ko ruwa take so a bathroom take dibar musu susha sam bata damu da fita cikin gidan ba.
Tana so ta fita ta danyi wani aikin amma rasa 'kwarin gwiwar hakan take yi kusan kowani lokaci.

Tana zaune kan daddumar da take salla akai sai taji ana kwankwasa kofa ta tasan bb mmk Raleeya ce ta miko musu abinci hakan yasa tayi saurin mikewa ta bude kofar...sa6anin Raleeya yau Hajja ladi na gani tsaye amma babu komai a hannun ga dukkan alamu ba abincin ta kawo ba sannan fuskar ta kamar kullun babu wata walwala.
"...Ammi na kiran ki a babban parlour...".
Daga haka ta juya sai kuma ta dawo da baya" kiyi maza in raka ki".
Chapter 53 · 0% Book details