Sashe 70
Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Tana kwance a 'daki da wani yammaci da bama tasan wace rana bace ma tana sharar kwalla da tunanin mafita sai ji tayi ana mata sallama wai ana kiranta a Parlor.
Tayi niyyan barin yarinyar amma sai taji tsoron barin ta ita ka'dai, gani take kafin taje ta dawo Moopyn zata iya tafia ta barta saboda yadda zafin jikin ta yayi tsanani.
Jikin ta na 6ari ta fito idanun ta duk sun fito sbd yawan damuwar da take ciki.
Tana fitowa Rayyan bai ma bari ta gama 'karasowa ba ya fara fa'din" kin kuwa san aikin ki anya a gidan nan?"
Da jin hakan tasan mene laifin ta hakan yasa taja ta tsaya tayi 'kasa da idanun ta tana addu'ar Allah yasa yayi mata uzuri.
Cike da marairaita tace" Dan Allah kayi ha'kuri wallahi yarinya ta ce bata ....."
Bai bari takai aya ba ya tare ta da 'daga mata hannu, dama yasan a kullum excuse dinta kenan.
Ya gaji da wannan kalmar akoda yaushe, komai yarinyar ta yarinyar ta yarinyar ta, shi me ruwan sa da wani batun yarinyar ta, aiki aka 'dauke ta kuma ta yadda zata yi meyasa zata bar masa muhalli da kazanta kusan kwanaki uku yanzu, ko ina yayi 'kura babu kyan gani.
Kici kicin yayi da fuska yace
" Akan wata 'diyar ki ne bazaki je ki tsabtace min muhalli ba...?"
Yatsa ya 'daga ya nuna mata yana daga tsayen yace.." Wallahi idan kk kuskura kk kaini bango bazaki ji dadin hukunci na ba, bana son iskanci da rainin wayo, kullum da an ta6a ki yarinya, yarinya, ke ko kunyar fa'di bakiji? akanki aka fara haihuwa ne ko me...?"
Ammi ce da ke tsaye bakin 'kofar shigowa tayi saurin dakatar da shi da fa'din " Rayyaan...?"
Ransa a matu'kar 6ace ya waigo jin muryar mahaifiyar sa da be yi zato ba...'dan lumshe idanu yayi sannan ya juya ya isa gareta cikin natsuwa.
Handbag dake hannun ta ya kai hannu ya kar6a batare da ya yadda sun ha'de ido ba yace" Welcome Ammi".
Duk yadda Ammi ke kallon sa da 'ko'karin son ganin 'kwayar idanun sa sam ya'ki amincewa...ko wlcm da yy mata ma 'kin amsawa tayi.
Ganin hakan ya sashi fahimtar ranta ya 6aci ne da kalaman sa.
Bai yi mamaki ba bcuz shi da kansa ba ze iya fa'din tsawon lokacin da take tsaye a wurin ba.
Zaitun kam goge hawayen ta tayi da tun 'dazun ke gangaro mata tana sake ta6a fuskar Moopy dake rungune saman kafa'dar ta tana mai jin 'dumin jikin ta na sake ratsa nata jikin..tsananin tausayin Moopy ne ya cika mata zuciya banda wannan ba'kin suna da ake bi mata yarinya da shi, duk duniya zata iya ha'kuri da komai amma bazata ta6a iya jure zagin Moopy da sunan shege ba..domin ta fahimci duk kalaman sa jurwaye yai mata, bai fito fili ya fadi kalmar ba amma duk dai hakan yake nufi while ita 'diyar ta ba shegiya bace kamar yadda suke tunani.
Hannun sa da hannun Ammi duk ri'ke da jakar amma ta'ki sake masa sai ma sake ha'de rai da tayi...a hankali ya 'dago nasa jajayen idanun ya zuba kan fuskar ta suka ha'de idanu.." am so sorry Ammi...ban sakewa".
Yayi maganar ta yadda ita ka'dai dake kusa da shi ne zata iya jin sa.
Sake masa jakar tayi da jin abinda ya fa'di sannan ta kawar da idanun ta daga gare shi.
Murmushi ta sakar mata tana me takowa izuwa cikin parlorn idanun ta na kan Moopy da taga ya langa6e a jikin Zaitun.
Zaitun murmushin 'karfin hali ta 'kakalo tana duban Ammi tace" Ammi barka da hanya.."
" Yauwa Zaitun...fatan kuna lafiya".
Ammi ta fa'di tana me 'ko'karin zama bisa kujera tare da cire gilashin idanun ta.
Zaitun na amsa mata tana shirin kwantar da Moopy kan 'daya daga cikin kujerun domin kawo wa Ammi ruwa.
Ammin ce tayi saurin fa'din bani ita nagan ta ne ma wata iri..."
Bata tanka ba kawai ta juya bayan mikawa Ammin ita sakamakon jiyo takun haurawar Rayyan da tayi zuwa saman Ammi wanda ya kai handbag da 'dan trolley na kayan Ammin da aka shigo da shi ne sama.
Kitchen ta wuce ta ha'dowa Ammi abubuwan sha masu sau'kin sanyi ta fito dai- dai lokacin da shima yake saukowa daga stairs 'din stairs ta gefen sa ta wuce batare da ta dubi ko inda yake ba ta isa gaban Ammi wanda tun ma kafin ta kai ga ajiye abin hannun ta Ammi dake rungume da Moopy ta jefa mata tambayar abinda ke damun yarinyar.
Jin hakan ya sanya ta zama gefen Ammin tayi rau-rau da idanu gami da fa'din" Zazza6i ne Ammi, tun shekaran jiya yafara mata jikin sai dau zafi sosai kuma bata iya cin abinci kwata- kwata..."
Tana kaiwa nan sai hawayen ta take ta rikewa ya 'karasa gangarowa...
Rayyan dake tsaye ciki-ciki yayi tsaki ganin akan wata 'diyar ta ne take yiwa Ammi kuka..." who cares?"
Waje yayi kawai ya ma fasa zama ko gaisuwa ba suyi da Ammin ba..bai ko sake kallon inda suke ba dan sosai ta bashi haushi yau din...ko Ammin ma bai tanka mata ba yayi wucewar sa ya bar part 'din kawai sai ta bishi da idanu har ya fice bata hana shi tafiya ba.
" Kin bata magani ne toh?"
Ammi ta jefa mata tambayar bayan ta 'dauke idanun ta daga hanyar da Rayyan ya bi.
Kai ta 'daga mata alamar " Erh...sannan ta 'karasa da na bata panadol syrup ma amma jikin har yanzu da zafi".
" Rayyan bai duba ta ba?"
Ammi ta tambaya tana duban Zaitun.
Yadda Zaitun tayi da fuska cike da mamakin jin furucin Ammin yasa Ammin cigaba da fa'din" Ai da kin fa'da masa ma da ko bai duba ta ba zai mika ku asbiti a duba ta sbd asbitin zai fi amma dubi yadda yarinya duk tayi laushi haka kina gani Zaitun...?"
Hawayen ta share batare da furta komai ba kawai ta janyo tiren da ta kawo, glass cup ta tsayar ta cika shi da juice 'din exotic me sanyi ta mi'kawa Ammin gami da fa'din" kisha ruwa Ammi". Cikin zuciyar ta tace" Allah ya sawwake..salon ya 'karasamin yarinya a banza.."
'Dan yatsina fuska Ammi tayi tace" bani ruwa kawai Zaitun.."
Maida shi ta ijiye sannan ta sake 'daga wani cup ta cika shi da ruwa ta mika mata.
Ammi ko hutawa bata yi ba tace suje asbiti aduba Moopy.
Ran Zaitun fari tas domin kuwa babu abinda yafi mata hakan farin ciki..lafiyar 'yar ta shine farin cikin ta a duniyar nan...amma koda yake hakan shine mura'din ta bata 'kaunar ya kasance ta hannun Rayyan ne.
Zazza6in ya riga ya shiga jikin ta dan haka sai da aka basu gado aka 'daura mata drip sannan...Zaitun ce ta ro'ki Ammi da ta koma gida ta huta kawai ita ka'dai ma zata iya kulawa da ita.
Ammi bata yi musu ba dan 'karfin hali kawai take sbd ganin yanayin yarinyar da kuma damuwa da ta fahimci ita Zaitun 'din ta shiga amma da kanta ma tasan tana bu'katar hutun.
Da yake ma an tabbatar mata da cewa drip 'din be kawai kuma da zarar ya 'kare zasu koma gida so tasan ba wata matsala ba jimawa zasu yi ba.
Sallama tayi mata da al'kawarin zata turo a maida su gida.
'Karfe biyar da 'yan mintina ya shigo part 'din har a lokacin fuskar sa a ha'de take..yana shigowa sai yaci karo da Ammi zaune a parlorn ta na sama, a hankali ya 'karaso gareta ya zauna ganin ita ka'daice babu wa'dancan tarkacen.
Zama yayi gefen Ammin yana sakin ajiyan zuciyan numfashi ya jingina kansa da kafa'dun ta yana lumshe idanu.
Murmushi Ammi tayi itam ta dube shi sannan tace" Ka daina fushi da ni 'din ne tun yanzu?"
Idanu ya bu'de batare da ya tanka mata ba sai da yayi baya ya gyara zaman sa ya jingina da jikin kujrea sannan ya gaida ta gami da yi mata ya gajiyar tafiya...Ammi ta amsa cikin sakin fuska.
Duban ta ya sake yi yana me baza kunnuwan sa sosai domin tsintan zuciyar sa yayi da son jin motsin su kamar yadda ya saba ji amma har yanzun shiru, kawar da wancan tunanin yayi yace da ita" Ammi da alamu yanzu kin daina son ganin farin ciki na gaba 'daya?"
Ido ta zuba masa da alamar tambaya saman fuskar ta, duk dama tasan zancen ba zai wuce na batun dawowar ta bane..amma sai bata nuna masa cewa tasan abinda yake nufi ba...shiru tayi kawai tana sauraran sa yayin da Rayyan a hankali ya cigaba da magana cikin nuna rashin jinda'din sa 'karara yake fa'din" Ammi bana so wallahi...kullum idan kinyi tafiya baki son sanar dani in zaki dawo sam na rasa dalilin hakan...Ammi bazan ta6a yafewa kaina ba idan wani abu ya same ki batare da na sani ba kin sani, dan Allah Ammi ki tausaya min ki daina sanya zuciya ta cikin ru'dani, kuma da dawowar ki ma ko gaisuwan kirki bamu yi ba na dawo ban same ki gidan ba Ammi me yasa baki son hutu ne plss....".
Ya 'karashe maganar fuskar sa cike da tsananin damuwa yana duban ta.