Sashe 144
Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Cak kukan Ammi ya tsaya ta 'dan ja baya ka'dan nan take wani mugun tunani ya 'dar su aranta..kar dai Zaitoon ma irin mutanen nan ne masu 'karya da sunan yaro dan kawai su ci dukiya...tasan akwai mazanbata da yawa akwai macuta, akwai maha'inta amma bata sako Zaitoon cikin su ba.
Zaitoon kam ganin irin kallon da Ammi take yi mata ya sanya ta jinjina mata kai tana share hawaye tace" Ba batun wasa Ammi, kuma kinsan bazan yi mk 'karya ba..."
Hannu Ammi tayi saurin 'daga mata tana.kawar da kai cikin zazzafan yanayi ta daka mata tsawa.
" Ya ishe ni haka nan dan Allah, basai kin bayyana min ba nasan me kk so yanzu, yanzu ne na fahimci asali wacece ke, yanzu ne na fahimci manufar ki na zama tare da mu, yanzu ne na fahimci fuska biyu gare ki Zaitoon..."
Rayyan ne yayi saurin zama gefen Ammi ya 'dan kwantar da kansa saman kafa'dar ta da alamun son kwantar mata da hankali.
Ita kuwa Ammi nuna Zaitoon tayi da har yanzu take goge fuksar ta tace" Rayyan kana jin me wannan yarinyar take fa'da kuwa...".
" Naji Ammi...ki kwantar da hankalin ki..zaki fahimci komai yanzu..."
Zaitoon kam gyara zama tayi sosai tana duban Ammi tace" Ammi yau zan gaya mk abinda zai baki mamaki, yau zan gaya mk asali wace ce ni, yau zan sanar miki asalin labari na da na jima ina 6oye mk Ammi.....
Salmerh😘
[11/12/2022, 4:28 am] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕
*( 'Yata ce)*
*Wattpad@*
_Serlmerh-md_
🅿️ *...81*
........Shigowan Marwa da Anty Marwa ne ya dakatar da maganar da Zaitoon ke yi, sakamakon ji da tayi ko sallaman Marwan an rasa mai amsawa a cikin su sbd yadda suka bada dukkan hankalin su gareta.
Saman la66a ta amsa sallamar tana mai waigawa ta dubi Marwa.
Idanu Marwa ta waro ganin yanayin Zaitoon da hannuwa tayi mata alamun tambaya.." Lafiya..me ya faru kuma...?"
Hankalin Both Ammi da Rayyan ma kanta suka koma sbd ganin Zaitoon ta mayar da hankali wajen ta.
Kafin su 'dauke idanun su daga kan Marwa sai wata sallamar suka sake tsinkaya ciki- ciki da wata sautin muryar da suka tabbatar da cewa ba sabuwa take a wajen su ba.
Kusan dukkan su atare suka raya sunan ta cikin zu'katan su amma ko 'daya babu wanda ya nuna alamun farin ciki da ganin ta har ta 'karaso ciki ta samu waje ta zauna.
Sai lokacin Ammi ta budi baki tace..." Amrah..! daga ina haka...?"
" Daga gida muke Ammi munzo..."
Bata ma bari Amrah ta kai aya ba ta jinjina kai gami da fadin..." Sannun ku toh...ya wajen su Mummyn naki...?"
" Suna nan lafia.."
" Haka ake so...".
Duk wannan maganar Rayyan ko sau 'daya bai dubi inda suke ba balle ya nuna alamun yasan da zuwan su, Marwa kuwa tuni ta 'karasa kusa da Zaitoon 'kasa 'kasa tayi mata ra'da a kunne.." Dan Allah me ya faru..naga fuskar ki da hawaye...?"
Zaitoon bata ce da ita 'kala ba illah juya idanu da tayi ta dubi gaban ta hakan yasa Marwa ma ta kai duban ta wajen.
Dabas ta zauna yanayin na sauyawa izuwa na alhini ta kai hannu ta 'dago hoto 'daya..saman la66a ta furta" Anty Nadia...!"
Muryar Amrah ne ya hana Marwa cigaba da magana jin tana mi'kawa Rayyan gaisuwa hadda mikewa ta isa wajen sa tana mai mi'ka masa yaron dake hannun ta.
Rayyan sam bai iya bude baki ya amsa gaisuwar da take yi masan ba sbd tsananin mamakin ta.
Wai yau Amrah haka ko kuwa idanun sa ke yi masa gizo.
Sai yanzu ne ta san da cewar yana da muhimman ci? Bayan sun gama lalaceqar su da Sultan hadda binsa tafia wata 'kasa ta barshi kwance cikin jinya..bata damu ba, bata damu da ko ya mutu ko ya rayu ba sai yanzun da ta tabbatar ya warke shine ya zama mutun ko...?"
Kallon ta yayi ya kuma duban yaron, jikin su fresh sun yi kyau sosai amma kokadan bai ji dai dai da kwayar zarra na kewar su ko farin ciki da zuwan su ba.
Kan yaron ya tsayar da duban sa take yaji wani murmushi na shirin 'kwace masa, bai kuma hana faruwar hakan ba, domin bai ga aibun sa ba idan yayin...cikin ransa ya jinjina wannan iko na rabbiz izzati, yaron bai bar komai na Sultan ba sai ma kamannin su da ya 'kara fitowa.
Alamu yayi wa Amrah da cewar hannun sa baya aiki balle ya kar6e shi sai ta 'dan nuna jimami saman fuskar ta tana shirin magana tajiyo hayaniya na tunkaro palorn saman Ammin da 'dan gudu gudu.
Badi'a ce ta shigo, bayan ta Mufeeda ce sai Imran daga 'karshe.
Yayin da sautin muryar Anty Madeena daga bayan su tana tahowa take yi musu masifar rashin natsuwa.." Ke de Badi'a ban san lkcn da zaki girma ba wlh...".
" Wallahi Anty itama rigima gareta wai fa sai na goya ta kuma nawi gare ta yanzu...".
Badi'an ta fa'da tana mai 'kara hanzari zuwa saman...tace" Mutum sai shegen son jikin tsiya..."
Anty Madeena ce tace" Daina zagar min ita..ai duk laifin ki ne, ba ke kk koya mata ba kuma sai yanzu ki wani ce zaki guje mata...?"
Sallamar da Badi'a tayi ya hana ta sake tanka maganar kasantuwar itace a farko, Imran yayi jin haka yasa Mufeeda ma yin sallamar.
Ba su dake zaune cikin 'dakin ba hatta da Anty Madeena dake bayan su sai da ta murmusa da jin muryar Mufeeda na sallama...in ka 'dauke Amra kadai da tun farko ta tsani yarinyar.
Yanzu ma abinda ya dawo da ita gida shine kan batun auren su, so take ya sawwakewa Zaitoon tunda ya samu sau'ki domin ita bazata iya cigaba da ha'da miji da 'yar aikin ta ba.
Murmushin Zaitoon yafi na kowa fa'da'da jin muryar sahibar ta da sauri ta waigo suka ha'de idanu.
" Mammi...."!
Mufeeda tace tana mai tahowa wajen ta da gudu.
Zaitoon kuwa ta bu'de mata hannuwa tana murmushi hawayen da bata san na menene ba yana sakko mata.
Da gudu Mufee ta fada jikin ta suka rungume juna.
Dai dai da 'karasowar Anty Madeena ciki.
Idanun ta cak akan su a fili ta furta" rai yaga rai kenan.."
Sannan ta 'dora da sallama.
Maganar farko da tayin da kuma sallamar da Mufeeda tayi 'dazun shi yasa fuskar kowa ta kasance cikin fara'a da annashuwa.
Har aka gama gaishe gaishe...Anty Madeena ke zolayar Badi'a da fa'din" Kina mata rowar hawa bayan ki..toh yau ga ta ga wacce bata gajia da goya ta ko da kuwa yini zata yi bayan ta..."
" Ta66in...da wannan nawin nata, ai banajin ko Anrmty Zaitoon din ma zata iya kamar da..yarinya duk ta zama 'katuwa da ita...".
" Tabarakallah masha Allah..."
Anty Madeena tace cike da jin da'di.
Amrah dai sai rarraba idanuwa take, sai taji zaman ya gundure ta anan, ko da ta mike dan wucewa sashen ta kuwa Ammi ta dakatar da ita da fa'din ta zauna magana zasu yi.
A kunne Zaitoon ta ra'dawa yarinyar.." Baki gaida Ammi da Abty Marwa ba, ga can Abba ma yana kallon ki wai gaida shi ba..."
Duban Abban Mufee tayi suka ha'de idanu tana no'ke kafa'da gami da ha'de ranta.
Duk da bai san dalili ba amma sai da yayi murmushi ya kuma kasa 'dauke idanu akanta, da gaske wannan 'diyar sa ce ko kuwa akwai sauran bayani agaba.
Baya fatan jin wani bayani sa6anin wanda ya fara tararwa wajen binciken sa ya bayyana, abinda kawai yake son ji yanzu daga bakin Zaitoon ne ka'dai.
Cikin ransa yake raya abinda Zaitoon tace da yarinyar da har ta dube shi...amma ya kasa samun abinda zai cike masa gurbin maganar ta su...kowanne ya kiyasta sai yaga bai hau dai dai ba.
" Kishiya ta babu gaisuwa ne...?"
Ammi tace tana mi'kawa Mufeeda hannuwa.
Tayi kyau sosai cikin shigan ta akayi mata kamar wata 'diyar 'yan gayu..dama Mufee ba dai kyau ba aka kuma dace da samun kula sosai kyanta ya kara fitowa jikin ta ya murje sosai.
Abin da yasa kenan Zaitoon bata ta6a bakin ciki ko.da Mufee zata yi fin sati gidan Anty Madeena domin tasan ana bata kula yadda ya dace, ba wani ke sanar da ita ba face tsabar saka idanu da kulawa da take bata ya sa take fahimta daga yanayin yarinyar idan ta dawo.
Sai da Zaitoon ta lalla6a ta kafin ta tafi wajen Ammi dan ta ki barin jikin ta tunda suka shigo.
Saman cinya Ammi ta 'daura ta tana yi mata wasa.
Abin ya sosa ran Amra sosai, domin ita tun shigiwar ta babu wanda ya ko.nuna alamun yana son 'daukan Arfan balle har a 'dauke san..ban dama wata bakar harara kasa kasa da take fuskan ta daga wasun su da nuna halin ko in kula da akayi da su.
Amma fa ji wannan, ko da yake ta san Arfan da jinin.su bane amma ai tunda ba sanin gaskiyar zancen suka yi ba bai kamata su yi banza da shi har haka.
Shiyasa tun farko ta zige Rayyan dan ganin an kawar da su a gidan amma hakan bai samu ba, ta zige mahaifiyar ta ta kuma yi barazana da auren ta duk dan sun bar gidan amma a banza.
'Karshe Sultan ta hurawa wuta akan su, sai dai shima 'din bata ga abin kirki da ya tsinana ba tunda har yanzun dai gasu nan duk araye cikin gidan kuma cikin 'koshin lafiyar su.
Baki ta tura ta wani ha'de rai sosai bata sake yadda ta dubi inda suke ba sbd takaici.
Cikin.ranta ta ayyana cewar tunda sun kasa da kaina zan dauki mataki, bazai yiyu in zauna wata banza ta kwace matsayin da ya dace 'dana ne ya kasance akan ta ba sam.
Sai da Ammi ta gama yiwa Mufeeda wasa tana 'yar daria ta mikawa Marwa ita tana mai mayar da duban ta ga Zaitoon tace..." Zaitoon bismillah muna sauraren ki..."!