← Book details Binteee Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 218

Sashe 11

Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tsaye cak Zaitun ta mike tare da sake rungumo yarinyar sosai bisa kirjin ta tana jin tamkar zuciyar ta zata fado saboda bugu, bata jin a duniya kaf akwai wata halitta baya ga mahaifan ta da zata so kwatankwacin yarinyar nan, dan a ganin ta idan kwana zata yi tana yiwa Mmn Abdul bayanin irin tarin kaunar da take yiwa Mufee ba zata fahimce ta ba, kuma bakomai ne cikin labarin rayuwar ta ba illah Mufeedah kadai, dan haka gara kawai abar wasu abubuwan a yadda idanu kadai ne ke iya ganin su.

_Salmerh_😘
[20/9/2022, 12:32 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE* 💕
*(' Yata ce)*

*Salmerh MD*

🅿️ *...7*

....Sai da ta koma daki sai taji kuka ya kufce mata, kukan da ita kanta bata san dalilin yin sa ba, sai kuma taji nawin da zuciyar ta yayi mata ya dan sauka, bayan wani dan lokaci da ta nutsu sannan sai ta ji kamar kuma bata yiwa Mmn Abdul adalci ba, baiwar Allahn bata san wace ita ba amma ta kar6e ta hakanan, bata san daga inda ta fito bata san meke 6oye cikin rayuwar ta ba amma a hakan ta nuna mata kauna ita da 'yar ta, tai musu halacci ta bada gudunmmawa cikin rayuwar su gwargwadon iyawar ta, bata ta6a kyarar su ba bata ta6a kyamatar su ba iya zaman su, meyasa kuma ita bazata bude mata zuciyar ta ba.

A daren ranar ta yanke shawaran washe gari zata bawa Mmn Abdul amsan tambayar da tai mata game da tarihin rayuwar ta, sai dai kuma kaf din daren kasa tsaida hawayen ta tayi haka ta kwana kuka bacci ma kauracewa idanun ta yayi, Mufeeda na kwance kan cikin ta tana shafa bayan ta duk wani motsin yarinyar tana lura da shi.

Abubuwa ne masu yawa suke yawo cikin zuciyar ta da ta jima tana danne su, ba karamin kokari tayi ba iya tsawon lokacin nan tana hana kanta tuno su, karfi da yaji ta hana kanta samun lokacin da zata ware domin tunawa da su.
Amma a yau hakan ya gagare ta, yau din ji take tamkar zuciyar ta zata fashe ne, sosai take jin kewa, tana jin dana sani na son taso mata, zafi take ji cikin kirjin ta sosai...zafi na rashin madafa rashin sanin tudun dafawa.

Washegari cikin rashin sa'a sai ta tashi da zazzafan zazza6in da take kyautata zaton matsantawa kanta da tayi da tunani ne ya haifar da shi.

Da kyar ta lalla6a ta yi wanka ta yiwa Mufee ma, Tea ta hada musu suka sha da guntun bread din da Adam ya kawo musu tun shekaran jiya da yazo, wanda a jiya da safe wata 'yar tafiya ta kama shi da take kyautata zaton har a yanzu ma bai dawo ba.

Kayan Mufeeda set biyu da suka yi datti tayi zaman wankewa su cike da karfin hali, dan gabobin ta duk ba karfi take jin su, hatta hannun ta ma ji take nan da wani dan lokaci tamkar bazasu iya amfanuwa ba saboda zafin zazza6in.

So take tayi ta kammala ta lalla6a wajen Mmn Abdul ta bata hakurin abinda tai mata jiya...dan tasan dole ne zata ji babu dadi.

_"...Salam Alaikum..."!_
Tajiyo tashin sallamar da tun ma kafin me rero sallamar ta bayyana Zaitun ta fahimci wace ita.

Amsa sallamar tayi tana mai kakalo murmushi ta dorawa fuskar ta na karfin hali.
"...Yau Anty Rauda ce da sassafe haka..."
"...ai dai ba yawon bariki naje ba balle ace na aikata ba daidai ba.."
Ta fada tana wani yatsina cike da kallon raini take watsawa Zaitun da ke Zaune har yanzun bakin kofar ta.

Sanye take da dan Hijab din ta da ta riga ta sabawa kanta dashi matukar zata fito harabar gidan.
"...Barka da zuwa Anty Rauda fatan an iso lpy..."
Ta sake fada duk da tasan cewa abu ne mai wahala ta samu kyakykyawar amsa daga Raudan..ga mamakin ta kuwa hakan ne.
" Da ba lafiyar ba ai baza'a ganni gidan 'yar uwa ta ba a wannan lokacin...kuma zikau aka ganni babu 'yar jagora balle tukuicin bariki..."

Wannan karon kam Zaitun bata sake tanka ta ba dan batun yau ba in da sabo yaci ace ta saba da halayyar Raudan da a kullun indai tazo gidan sai ta yada mata magana makamancin wannan, wani bin sosai take mamakin Raudan, yadda take daukan zafi akan Zaitunan kai kace akwai wata mummunar gaba da ya ta6a hada su, amma ba komai ne ya kawo hakan ba face zaman Mufee tare da su Siyama da suka kasance 'ya'yan yar ta kasantuwar ita din kanwa ce ga Mmn Abdul uwa daya uba daya sai dai akwai banbancin halayya karara.

Tun da jimawa farkon zuwan Zaitun gidan da Rauda tazo Hajja ta fesa mata karya da gaskiya shikenan tun daga ranar ta dauki karan tsana ta dora musu.
Mmn Abdul ke taka mata birki wani bin dan matukar taji ko ganin Raudan tayi mata ba dai dai ba takan tsawatar mata..wana Zaitun din ke kyautata zaton ko na yau din ma da ace taji bazata ta6a yin shiru ba.

Zaitun bata sake bi ta kansu ba bayan ta shanya kayan wankin nata daki ta koma ta cigaba da kwanciya zazza6in kuwa kamar jira yake yace Salamu Alaikum, dan sosai take rawar sanyi, Mufee dake can gefe tana ta wasa da kayan wasan da Adam ya siya mata Zaitun ita Zaitun ta kurawa idanu, yanzu idan Allah ya kar6i rayuwar ta cikin wannan halin waye zai maye gurbin ta wajen Mufeen?, waye zai kala da ita? meyasa ma ta baro gida ne? Anya kuwa ta yiwa kanta adalci, ta yiwa mahaifa da 'yan uwan ta adalci..?"
Ta jima da fara tunanin waiwayar gida amma tsoro take ji dan zaman ta da Mufee ba zai ta6a yiyuwa a gidan mahaifin ta ba haka ma ga mahaifiyar ta..shiyasa ta yanke shawaran bari idan Mufeedan ta dan kara wayo sannan su koma aga yadda hali zai yi ko zasu kar6e su su yadda da tata salon kaddarar rayuwar.

Kara karaf-karaf dake tasowa daga 6bangaren Mmn Abdul shine ya maida hankalin Zaitun a can, tasan dai a wannan lokacin Abdul da Siyama na makaranta balle tace sune suke yi, sai daga ma fahimci ashe _kwalema_ su Mmn Abdul din keyi wanda shine ma dalilin zuwan Raudan gidan da farar safiya.

Taso ta fita ko zata iya saka musu hannu amma ko data gwada mikewa sai taji jiri na shirin kayar da ita dole ba dan taso ba ta hakura kawai ta cigaba da kwanciyar ta har kusan sallar azahar sannan da Mmn Abdul taji shirun yayi yawa ne ta lekota nan taga ashe Zaitun din bata ji dadi bane shiyasa.

" Subhanallahi.."
Ta furta cike da kulawa.
" Toh kin sha magani ne..?"
Ta tambayi Zaitun din tana me ta6a wuyan ta.
" a a zansha anjima kadan"
" Ki daure kisha dai Zaitun inda hali ma da chemist kika leka a duba ki acan, ni kwa dai nayi mamaki, tun dazun naji shiru nake tambayar kaina ko me ya faru ashe zazzai ne ya rike ki anan, toh Allah ya sawwaka ya sa kaffara ne, bari Siyama ta karaso sai ta rakaki kuje chemist din ko.?"
" Toh Mmn Abdul nagode sosai.."
" 'yan mata yau Mammi na gida an mance da ni ko.?..".
Ta karasar da maganar tana mai sauke idanun ta kan Mufee dake kwance gefe da Zaitun din ta wani rungume mata hannu.

Yinin ranar kaf babu inda ta je ban da wajen mai chemist da Mmn Abdul ta matsa akan sai taje aka duba ta gami da bata magani ta biya kudin.

Da yake yanzu tana dan ajiye canji cikin albashin ta saboda nawin abubuwa da dama da Adam ya dauke mata.

A hanyar su ta dawowa ne suka hadu da Hajja ta sauka adaidaita tun a farkon layi.

Ganin ta da Siyama tayi yasa ta tafi da gudu tana murnar ganin ta ta rungume ta.(Siyaman ce ta raka Zaitun chemist din.)

Zaitun bata san meyasa ba amma sam ganin Hajjan be mata dadi ba har a zuciyar ta, tun barin Hajja gidan tashin hankalin ta ya ragu, damuwar ta ta zabge, yawan tunani yai mata kaura dan dama sau tari maganganun Hajja ke sawa tana yawan tuna baya...tuna bayan kuma shi ke yawan sata zubda kwallan da bata iya hana su sauka.

Kawar da duk wannan tunanin Zaitun tayi cike da karfin hali ta nufi Hajjan itama tana mata barka da zuwa gami da mika hannu da niyyar kar6a buhun bagco da Hajjan tazo da shi amma ga mamakin ta sai Hajjan tayi saurin janye abinta alamu karara na nuni ga cewa bata bukatan tallafi daga Zaitun din sai ma tayi gaba batare da ko sannun da Zaitun tayi mata ta ansa ba.

A hankali Zaitun ta bisu abaya gudun kar jiri ya kwashe ta dama ba wani karfin dauka ke gareta ba kawai itama dauriya tayi sai kuma aka yi sa'a Hajja tai bore.

A yanayin da take tafiyar ne ya sanya kunnuwan ta jiyo hirar wasu matasa dake zaman majalisar bayan azahar.
"...Rayuwa wallahi yanzu duk ta lalace Sabi'u, dubi wancan 'yar yarinyar idan akace maka zaman kanta take zaka yadda...?"
" ahh haba dai ni da zan ma ce maka tayi min ka binciko min gidan su tunda kai dan unguwa ne..."
"...Allah ya tsare ka da wannan...in gaya maka har shegiyar yarinya take da shi mara uba...'yar iska ce wannan ta karshe...."

Maganar tasa dakatawa yayi ganin yadda Zaitun ta waigo tana duban sa duba irin na tuhuma dama kadan ta gita su so taku kadan tayi ta dawo baya gaban su.
Chapter 11 · 0% Book details