← Book details Binteee Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 130 OF 218

Sashe 130

Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali ya cigaba da kulawa da lafiyar sa da taimakon ragowar 'karfin da ya rage masa.
domin a halin yanzu ko Zaitoon ta shigo duba shi ma ko kallon arziki bata samu daga gare shi balle har ta samu damar yi masa wani taimako...kuma da yake tasan ya farka sai bata sakewa kamar baya bata ta6a iya matsawa kusa da shi in dai ba shine ya bu'kaci hkn ba.

Sa6anin hk kuwa ayyukan ta kawai take yi ta ficewar ta.

Shima Rayyan haushin ta yake ji musamman idan ya tuno wai matar sa ce itama, amma duk cikin su ita har Amran babu mai iya yin zaman mintina talatin tare da shi.

Abu guda 'daya ke sashi raga mata shine idan ya tuno Mufeeda.
Mufeeda ta bayyana cewar ita din jinin sa ne, kuma Zaitoon ta kula da ita ta 'kauna ce ta da dukkan 'karfi da zuciyar ta, sannan ga shi shima yaji a bakin da yasan baza su yi masa 'karya ba Zaitoon ta kula da shi, toh idan yayi mata ba'kin rai ai da kansa yasan bai mata adalci ba, yarinyar ta 'karachi ilahirin rayuwar ta ne wajen bauta masa shi da 'diyar sa, bata san da'din rayuwa ba sam burin ta ta sama musu farin ciki ne a koda yaushe.

Duk san da ya tuno wannan abin sai yaji bazai iya yi mata abinda yake jin zuciyar sa na ingiza sa ba, dan sosai yake ji cikin zuciyar sa cewar yayi mata koran kare daga sashin sa gaba 'daya.

Amrah da ta fahimci farkowar sa 'korafi na farko data fara shigar masa shine na auren Zaitoon..Rayyan kasa ma tanka ta yayi.

Tace taya ma Ammi da kanta zata amince ta aura maka wannan 'yar iskar yarinyar, Baby ka manta har yarinya ce da ita marar uba....?"

A hankali idanun sa suka koma suka lumshe da jin wannan furuci na Amrah.

A cikin zuciyar sa yake jin zafin kalmar ta kuma mamayi ilahirin jikin sa amma sam baya da wata kalmar furtawa ga Amrah.

Sam baya 'kaunar ko da ganin fuskar ta ne, bayan cin mutuncin da sukai masa da yake kwance bashi da lafiya mai kuma take sake nema awajen sa...yana wannan tunanin ne daidai lkcn da ya tsinkayi sautin muryar Amrah na fadin" Dan Allah Baby ka sallame ta tun Kafin ta caku'da mana zuria da irin nata iskan yarana..."
" Dan Allah Amrah go to ur room...plz leave me..."
Ya fa'da a'dan tsawace ransa a 6ace sosai tun ma kafin ta dasa ayar maganar ta.

Sum- sum ta fita tana 'ku'k'kunin mutun na jinya ma amma ba'kin hali na nan bai barsa ba.

Amrah ko da ganin sa zaune hakan bai hana ta fita yawon ta yadda taga dama ba, dan tasan babu mai taka mata birki a halin da ake ciki.

Hatta su Ammi sun san yawan fita da Amrah ke yi amma basu ta6a tanka ta ba... ala'kar ta Sultan ne dai basu da masaniya akansa illah Zaitoon kadai ta sani sai kuma shi uban gayyar, itama 'din albarkacin zaman ta sashen yasa ta fahimta...domin wani bin sukan shafe sama da awanni biyu cikin 'dakin Amrah...yayinda wani sa'in sukan shafe tsawon wasu kwanaki a hotel suna hutawa abinsu.

In sun so kuma su shirya wajen ha'duwa ta fice ta tafi wurin sa, suyi yawo daga nan a wuce hotel asha sharholiya sannan a dawo gida..gaba 'daya Sultan ya gama lalata zuciyar Amrah bata gane kalaman kowa sai nasa.

Su Ammi basu ta6a hana ta ko yi mata fa'dan yawan yawon da take yi ba sbd gudun fitina sai suka kyale ta...musamman Ammi da ta bawa abin cewa 'kilan uzuuri gareta dake sata yawan fitan.

Hankalin su duk akan Rayyan ne, burin su suga ya waraware gaba 'daya ya tashi da 'kafafun sa tamkar baya.

Tunda ita bata san ta yiwa kanta fa'da ba a matsayin ta na mata kuma matsayin uwa ba ai sai tayi.

Ganin yadda yk fama da amfani da hannun hagun sa ka'dai dake aiki dole tasa Ammi rokon Zaitun cigaba da kulawa da shi kamar baya da yake kwance...ga kuma yadda matar sa ke nuna masa halin ko in kula da sha'anin sa...dan a lokacin ma ya samu sau'ki ba laifi sai dai hannun sa na dama dake da matsala baya aiki sam, gashi dai tsab zaki ganshi mutum har mutn amma hannun haggun sa ne ka'dai me amfani hakan yasa dole wasu abubuwan sai an taimaka masa, kama daga alwala, yin brush, cin abinci, dressing da sauran su.

To Amrah babuvruwan ta yanzu a bayyane take nuna ita bata son wahala akansa, 'karshe ma Uk ta tafi da 'kawayen ta yawon sha'katawa, shi kuma a lkcn sam bai damu da Zaitoon ba bai 'dauke ta wai matar shi ce dagaske kamar ya samu lbr ba, a hankali kuma sai abubuwa suka fara fin 'karfin sa, gashi sultan baya gari yy masa nisa haka ma Amrah, cikin 'kunci yake jin zuciyar sa sosai amma bai bari kowa ya fahimta ba.

Ranar da zasu koma asbiti da 'kyar ya shirya kansa yanayi yana tasbihi ga ubangiji da ya halicce shi.mutum cikakke, ha'kika nakasta jarabta ce.

Duk yadda yayi 'kokarin shirya kansan amma saka ma6allai da 'daura necktied sun gagare shi...gashi ba'kin halin sa yasa ya hana Zaitoon sakewa a 6angaren nashi ma balle taimaka masa.

Dole ya 'kira Ammi akan ta taya shi saka ma6allan.
Ammi bata yi musu ba tazo ta 'daura masa amma tana yi tana masa fa'da ha'di da nasiha cikin natsuwa, ta yadda zai fahimce ta da kyau, nan ta nuna masa muhimman cin Zaitun a kusa da shi..
Rayyan shiru yayi bai ce uffan ba...kamar 'karamin yaro a gaban Ammin kawai ya 'dan ha'de ransa yana sauararen ta.

Ammi bata yadda tabar gidan ba sai da ta tabbatar ta sake bawa Zaitoon hakuri gami da rokon ta alfarma akaro na kusan uku kenan yanzu akan sa, kuma ba akan komai ba sai dan ta ringa kulawa da shi kamar yadda ta saba dan ba komai ne yake iya yiwa kansa ba.

Zaitoon bata ji shakkan sanar da Ammi cewa shine yace bai son taimakon ta ba...
Ammi tace 'kyale shi, bazai sake fa'din hakan ba Insha Allahu.
Zaitoon shiru tayi, bata so ta ringa jan musu da Ammin ko kuma 'karyata ta amma ita tasan ba'kin halin Rayyan a gidan nan, bacin da kansa yace ta daina zuwan masa 'daki.

'Karshe basu rabu rabu da Ammi ba sai da tasa Zaitoon yi mata al'kawarin zata bashi kulawa, tace mata yanzu ba Mufee bace ka'dai nauyin da Allah ya 'daura mata tace shine babban nauyin da ke kanta wanda har zai iya sadata da aljanna.

Har Ammi ta bar 'dakin nata bata 'kara iya magana ko kallon inda take ba.

Tunani take ta yadda Ammi zata fahimce ta amma bata ga alamun hakan ba.

Yini tayi tunanin mafita amma bata hango ko guda ba.
Bata kuma.samu damar zuwa 'bangaren ba har sai da yammaci lkcn da ta tabbatar duk inda yake ya dawo saboda Ammi ta jima da dawowa.

Zaune ta same shi kan sofa da hannun sa 'daya mai cikakken lafiyar yake shafa saman dantsen hannun sa 'dayan da ke ciwo...da alamu sabon 'dauri akayi masa a hannun, jikin sa babu riga illa dogon wando ka'dai, kallo.'daya tayi masa ta 'dauke kanta.

Yanayin da ya amsa sallamar ta tasan ko ta gaida shi abu ne me wahala ya amsa ta..ilai kuwa hakan ne sai dai sam bata damu ba, ai inda sabo ta riga ta saba da wannan halayyar tasa.
" Ya jiki...?"
Ta 'kara tambaya tana mai kawar da kanta izuwa gefen gadon sa.
'Dagowa yayi ya dubi bayan ta dayake already ta juya.

Bai amsa ba kamar yadda bai sake kallon inda take ba, ya mike yayi kwanciyar sa yana lumshe idanu.

Sai da ta gyara masa gadon da ta tabbatar yana da bukatan gyaran kafin ta nufi bayi ma ta tsabtace shi duk da babu wata alama ta kazanta dake bayin illa kayan sa da ya cire da safe sai da ta wanke su kafin ta fito..bata sake duban inda yake ba tayi waje abinta.

Bayan maghrib ita ta gabatar masa da abinci amma bai ci ba yace Coffee mai zafi kawai yake so...Rayyan bai sake korar ta ko yi mata ba'kin rai ba sai dai babu wata doguwar magana tsakanin su.

Duk kuma abinda tasan nawin sa yin sa na kanta ne takan yi 'kokarin aikata shi tun ma kafin ya bu'kaci hakan.

Hutun ta ka'dai idan su Ammi ko Anty Madeena sunzo ne sai kuma Marwa da ke 'dan tallafa mata da sauran aikace- aikace.

Wannan dalilin ne ya kawo 'yar kusanci tsakanin su, ya kan yi mata wayo ya hanata tafiya 'dakin ta da dare ko kuma idan tana yi masa addu'ah yayi ta kallon ta tun yana mamakin abinda take yi masa a hannun sa har yazo ya saba ma, ko magani zata shafa masa ya dinga kallon cikin idanun ta kenan, musamman idan tayi 'kasa da idanun ta sosai yake 'daukan hankalin sa.
Haka in zata bashi abinci ko taya shi dressing amma maganar kirki babu a tsakanin su har lokacin sai dai ta idanu kadai.

Sosai yake yawaita jin abinda bai saba ji ba akan sauran matan sa dan shi be kasance mutum mai tsananin bu'kata ba amma akan yarinyar sai yake ji daban.

Haka kawai ganin idanun sa sai yaga ta rame masa bai kuma san dalili ba, amma da ya zurfafa tunani sai yga kamar hidimar sa ce tayi mata yawa ga kuma ta Mufeeda.

Yaso ya ce da Anty Madeena ta 'dauke yarinyar a wurin ta amma shi kansa baya so tayi masa nisa.
Kuma ko ya hana ta yin wasu aikin ba ji take ba, yayin da 6angaren ta take ganin idan bata yi ba wa zai musu toh..tunda alhakin komai na wuyan ta ne a yanzu.
Har mantawa yake da wata wai Amrah sbd tuntuni halayyar ta yasa ta fita ransa kwata- kwata.
Chapter 130 · 0% Book details