Sashe 14
Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ganin mutun tayi ya bayyana ta bayan labilen dakin ta..." Yah Subhanallahi.."
Da sauri ta yunkura gami da bude baki da niyyan sakin ihun neman agaji, kafin ta gai ga hakan ne Bbn Abdul da ya gama fahimtar abinda take shirin yi taku daya tak yayi sai gashi gaban ta ya rufe mata baki ruf da hannun sa daya..." Haba Zaitun ya zakimin haka?
" ba daman nace miki zamu yi magana ba..?"
Kici kicin kwatan jikin ta take yi yayin da ko'ina na jikin ta duk ya dauki rawa.
Duk iya tattaro karfin ta da tayi hakan be sa Bbn Abdul yayi ko gezau ba dan karfin ba 'daya bane.
"..Ki nutsu dan Allah babu abinda zan miki...ni dai dan Allah Zaitun ki taimaka ki amince muyi aure tun kafin shaukin sonki ya kaini ga aikata ba daidai ba tsab sai inyi aika-aika.."
Fadan hakan da taji yayi ya kara mata kaimi wajen son ganin ta kwaci kanta amma inaa..ta kasa cire hannun Bbn Abdul daga bakin ta.
"..Wai ke baki jin tausayi na ne Zaitun?..wlh ina son ki kuma na miki alkawari zan kula Mufeeda tamkar 'yar ciki na, duk abinda zanwa su Siyama nai mk alkawari shi zanwa Mufeeda dan Allah ki amshi soyayya ta..."
Duk maganar nan yayi ta ne batare da ya bawa Zaitun damar kwatan kanta daga hannun sa ba.
Takaicin ta daya ma ko Hijab babu ajikin ta dankwalin ta ma tuni yayi nasa waje sai tsefaffen gashin ta da duk ya barbaje saboda kiciniyar da take yi.
"...Ki nutsu nace ba abinda zan miki...amma kina yin wani kuskuren da ya janyo hankalin mutane har aka shigo cewa zanyi ke ce kika gayyato ni dan ban miki abinda kike so bane kuma yasa kike min ihu..."
Daga fadin hakan ya sake mata baki ya mike tsaye batare da wani 6ata lokaci ba.
Kuka kawai Zaitun ta saki mai cike da takaici, kuka mai tsuma zuciyan duk wanda ya ji.
Jifan sa ta fara yi da duk abinda hannun ta yaci karo da shi.." Mugu! macuci,..wlh ban yafe ta6a jiki na da kayi ba..kuma ka kuskura ka sake shigo min daki sai na illata ka..baza'a aure kan ba, bazan aure ka ba mara imani kawai...".
Ta jero duk wadannan batare da ita kanta tasan me take fadi ba,ta karashe da durkusawa kasa kan gwiwoyin ta kukan takaici na sake kubce mata.
Irin kukan nan da kake yi idan a cuce ka kuma an hanaka daukan fansa.
Shi kansa jikin sa yayi sanyi but he have to do all this ko hakan zai sa ya same ta yadda yake so.
Bbn Abdul bai ce da ita komai ba sai ma hanyar fita da ya dauka bayan gama jin kalaman nata.
Sai da ya sa kai zai fita sannan ya waigo..." Ki sani, bazan sake 6ata lokaci na wajen nuna mk soyayya ta ko kuma rokon ki akan ki aure ni ba daga yau, amma ki shirya tarata daga gobe zuwa kowani lokaci.."
Daga haka ya fice abin sa ya tafi, da gudu Zaitun ta tashi taje ta isa ga kofan sakatan ta saka tana wani irin kuka gwanin tausayi.
Jikin kofan tabi ta sulale ta cigaba da kukan ta, sai da tayi mai isan ta kafin ta tashi ta koma gefen Mufeeda ta kwanta..bacci sam kaurace mata yayi tana ta tunani, meyasa abubuwa ke neman fin karfin ta ne.
Shin cikin kaf din rayuwar ta akwai inda ta kuskure ne da Allah ke hukunta da shi.
Bata da amsoshin duk tambayoyin da ke makare cikin zuciyar ta dan haka dole ta hakura.
Bacci 6arawo ne ya sace ta batare da ta sani ba.
washegari bata bi ta kan kowa na gidan ba tana kammala hidimomin da ke gaban ta ta goye Mufee suka wuce wajen aiki dan aranar ko mutun guda daga cikin gidan ji tayi idanun ta basa kaunar gani.
Idanun ta sam basa ko ganin inda take jefa kafafun ta kadan ya rage ma bata afka wani ramin soak away da aka fara tona bada jimawa ba har sai da wasu 'yan mata biyu dake bayan ta suka ankarar da ita.
Da haka ta samu ta isa wajen aikin, sai ya kasance yau din babu wanda ya riga ta isa cikin ma'aikatan gaba daya….sai dai me? tun kafin ma ta gama shigowa balle akai ga batun gaisuwa Hajia ta fara surfa mata ruwan bala'in tazo mata da goyo bacin ba haka suka yi da ita ba.
Hawaye kawai Zaitun ke sauqewa, ta rasa me ke damun kwakwalwar Hajiyan, shin Mufee kadai take yiwa wannan kiyayyar ko kuma duk har itan take wa kora da hali.
Ta riga da ta saba da duk ayyukan da take yi a wajan kuma tana da tabbacin Mufee baza ta6a yi mata sha maki da ayyukan ta ba...toh ta ina matsalar take?
A tun zuwan da takeyi da Mufee bata ta6a kuskuren da yarinyar tayi ko da 6arna bane balle ace dalilin kena...toh me Hajiya ke nufi da ita?"
Bata tanka Hajiyan ba a zahiri amma gaba daya taji aranta aikin ma ya isheta kwatakwata.
Sai da Hajiyab tayi mata tatas tayi mai isar ta kafin ta barta ta kama aikin ta...abu guda ke mata yawo cikin zuciya kashedin Hajiyan na cewa alfarmar yau kawai tayi mata daga yau din kuma bazata sake tolerating irin hakan ba...toh in ba aikin take so ta bari me take so?
bata jin zata sake iya barin yarinyar ta wajen koma waye ne.
Tayi aikin ranar ne duk cikin rashin natsuwa sai dai ko kadan bata yadda tayi kuskuren da za'a kamata da laifin sa ba balle a 'dora alhakin kan zuwan da tayi da Mufee.
Da misalin karfe uku ya tashi a aiki, sai da ya wuce gida yayi wanka ya fito fes da shi.
Masallaci ya tsaya ya sallaci sallar la'asar kafin ya karasa wajen Hajiyar tasa.
Tun isowan shi wajen idanun sa ya sauka akanta, wanda kallo 'daya yai mata ya fahimci akwai abinda ke damun ta.
Gaishe da Hajiyan yayi yana me 'dan yatsina fuskar sa.
Hajiyan da tasan halin kayan ta sai cewa tayi bari a ha'do maka abinci nasan matsalar kenan ai"
Inda tayi maganar tana murmushi da yake tasan Adam ba me wasa da cikin sa bane.
"..Yanzu Adam wannan aikin kake ganin yafi dacewa kayi da gatan ka da komai?"
" Hajiya nafi san in nemi halak dina ne da kaina..dan Allah ki samin albarka kawai shi nafi bukata".
" Toh Allah yasa hakan shine mafi alkhairi".
Hajiya Talatu ta fada tana me bada umarnin a ha'do masa abinci, cikin sa'a kuwa sai abin ya fada kan Zaitun.
Shamsiyya da a kullun Adam din ke kara tafiya da imanin ta ta idan yazo ta dinga binsa da kallo kenan a 6oye.
" 'Karasa aikin ki bari ni zan ha'da masa"
Tace da Zaitun tana mai basarwa tamkar babu wani abu cikin ranta.
Zaitun kam bata kawo komai aranta ba ta bar mata ta cigaba da sabgar ta.
'Bangaren Adam kuwa gani da yayi Hajiyan wa Zaitun ta bawa umarnin kawo masa abincin yasa shi neman hanyar komawa gefe dan nesa kadan da Hajiyan ta inda baza ta hangoshi ba koda zai yi magana da Zaitun din.
Dan tunda yaga yanayin fuskar ta lokacin da ya shigo gaba daya ya rasa natsuwar sa, ji yayi hankalin sa bai kwanta ba, 'kage yake da son jin damuwar ta a yanzun.
Unfortunately sai kuma yaga ba Zaitun ce ta kawo abincin ba, sai dai bai yi azar6a6in tambayan Shamsiyya dalili ba dan har yau babu wanda yasan alakar da ke tsakanin sa da Zaitun din kaf shagon Hajiyan, sosai suka iya takun su dan duk din su daga shi har Zaitun din ba masu rawar kai bane sam.
Duk da yunwan dake kwakulan ma ciki amma haka yaji abincin ya kasa yi masa dadi, dagaske fa damuwar Zaitun din kawai ke gaban sa a yanzu.
Gudun kar Hajiya ta zargi wani abu yasa shi daurewa ya dan ci abincin kafin ya tashi.
" Ga Hajiyan ya dawo yana me yawo da idanun sa cikin babban shagon yake fadin Hajiya zan dan fita yanzun akwai wani uzuri dake gabana amma ba mamaki kafin maghrib in dawo ko zuwa bayan Isha".
" Sai ka dawo Allah ya tsare min kai..."
" Ameen Ameeen Hajiya ta ni kadai..."
" Yauwa mun yi magana da Alhajin ku dazun yace idan akwai wata damuwa ayi masa magana".
Bai ma juyo ya dubi Hajiyar ba yace..." Ni bani da damuwar komai Hajiya.".
Daga haka ya kama hanya ya fice a wajen zuciyar sa taf wasi wasi.
Ko da ya fita ji yayi tamkar bazai iya barin wajen ba har sai yaji menene matsalar tan, cak ya tsaya ya waigo da tunanin ko zai hango ta amma bai ganta ba.
Kai tsaye zuciyar sa ta bashi umarnin toh shin wa kake tsoro ka koma mana ka tambaye ta ko dan kwanciyar hankalin ka ma har zai bi umarnin zuciyar tasa amma sai wani 6arin zuciyar ya hana shi.
" Kai Adam..kabi a hankali dai sannu sannu bata hana zuwa sai dai a dade ba'a je ba...".
Da wannan shawarar ya samu kwarin gwiwar barin wajen sai dai bai iya yaje inda asali yayi niyya ba wajen wani abokin sa dake can wajen gari shima wani gidan mai yake aiki wanda shine ma yayi wa Adam hanyar samin nasa aikin a inda yake.
Adam Hustler ne baya zama sam, dan bayan gidan mai da yake aiki yana da wajen san'ar sa nashi na kashin kansa inda yake saida su Kerosine, Petrol, da engine oil kuma Alhamdulillah ba karamin alkhairi yake samu ba, hakan ma ba shike zama da kansa ba saboda aikin da yake zuwa ya sanya shi dora yaro akan wannan sai dai ya kan kai masa ziyara duk lokacin da yake da lokaci watarana ma yakan zauna ya ringa siyar da mai din da kansa ba tare da girman kai ba.