Sashe 43
Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tsundum Jibrin ya fa'da harkar siyasa ya kuma yi nasarar da duk wani makusanta da masoyan sa suka taya shi farin ciki, yayin da 6angaren Adam abin ba haka yake ba dan ko a jikin sa ma, ko yaji cewa abin ya masa aran sa ma bai ji ba, aganin sa tunda ya kasa kula da lafiya da farin cikin mahaifiyar sa ya kuma kasa sauke hakkin sa dake kansa matsayin sa na uba toh meze dame sa da shi.
Adam kyakkyawan saurayi ne fari mai matsakaicin tsayi, tsabta da nutsuwa kusan sune suka karbi gaba wajen bayyanar da asalin kyawun da yake da shi gashi da kyakkyawar mu'amala.
Ba karamin buri Hajiya take ci akan saba kwatsam sai Zaitun ta fa'do cikin rayuwar sa batare da Hajiyan ta farga ba, bata yi kasa a gwaiba wajen shiga tsakanin su da nuna mata nisan tazara dake tsakanin Adam da ita, ta kuma yi nasara sakamakon sanin da Zaitun ta yiwa sunan 'Dan Maliki badan tasan shi a fuska ba amma tasan babba ne shi a 'kasan nan, ta kuma san waye mahaifin ta tasan gaskiyar Hajiyan ne akwai tazara tsakanin su duk da Adam bai ta6a gwada mata hakan ba.
Kwatsam alhini da jimamin rashin Zaitun bai bar zuciyar sa ba labari ya isko shi cewar wata babbar mota tayi fatali da kayan sana'ar sa na bakin titi komai ya lalace, yaron ma Allah ka'dai ya sa ya tsira da kadan motar ta bi kansa, hankalin Adam ya tashi sosai dan har kwalla sai da ya zubar da jin wannan labari amma daga baya da ya tsaida tunanin sa sai zuciyar sa ta sanar da shi waye sanadi bai kuma yi mamaki ba dan yasan fiye da hakan ma zai iya aikatawa dan ganin ya durkusar da shi ta yadda dole sai ya ja hankalin sa ya fito duniya ya nuna cewar shi 'din 'da ne agare shi shi kuma bai ji zai iya hakan ba.
Salmerh😘
[20/9/2022, 12:34 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕
*( 'Yata ce)*
*Wattpad@*
*Serlmerh-md*
🅿️ *...27*
......Haushin fatali da 6arnatar masa dukiya da akai batare da wata 'kwak'kwarar dalili ba ya sashi yanke shawarar zuwa ga 'Dan Maliki suyi magana ta fuska da fuska, yana so ya fito masa a mutun ya nuna masa gaskiyar cewa ya gaji ya kuma kai 'karshen bango, yana so a sarara masa haka nan, kuma inda hali baya so ya 'kara shiga sabgar rayuwar sa, shike da ikon za6arwa kansa duk irin sana'ar da yake so ya kuma ga ta kwanta masa dan haka ya 'kyale shi, ko kwasar kwata zai yi babu ruwan kowa da shi.
Sun tattauna da Hafeez kan hakan lokacin da yazo yi masa jajen lamarin ya kuma so dakatar da Adam 'din kan cewa da yayi zai sami 'Dan Malikin tunda a zahiri babu wata alama da ta bayyana da sa hannun sa ciki.
Amma Adam sam ya ki amincewa da batun Hafeez domin acewar sa shi ya san waye 'Dan Malikin da duk shirin sa, dan haka in zai raka shi toh bismillah in kuwa baza shi ba ma duk ba matsala bace agare shi zai iya zuwa shi ka'dai.
Da wannan tunanin ya ringa kwana yana tashi har zuwa ranar da ya samu lkcn zuwa ga 'Dan Maliki domin ganawar bisa tursasawar sa ga Hafeez dole sai da ya raka shi.
Unfortunately sai basu je kan sa'a ba sakamakon katari da mugun gani da suka yi shi har Hafeez 'din babu wanda bai tsinci kansa cikin tashin hankali ba.
Duk wa'danda ke aiki tare da mahaifin nasa zuwa lokacin sun riga da sun san kakkarfar alaka da ke tsakanin sa da Adam dan haka koda ya nemi ganin sa bai samu wata matsala ba, sai dai cikin rashin sa'a sun same shi ne tare da wasu watsatstsun 'yan mata, ba sai an fa'da masa ba domin a yanayin da ya gansu amsar shi ta riga ta bayyana a fili karara, ya kuma san already matar da yake aure tana can Abuja da zama kuma ita babbar macece ba kamar 'yan matan da ya gani tare da shi ba, wa'danda yana da tabbaci ba dan ku'di da suke samu daga 'Dan Malikin ba da bb abinda zai sa su saurare shi ma sbd shekaru da suka bayyana gareshi 'karara.
Fa'din halin da Adam ya tsinci zuciyar sa a wannan ranar ma 6ata lkc ne, abin ya matukar ka'da shi, sosai yayi masa ciwo a zuci, yayi ba'kin ciki irin wanda ya jima bai yi irin sa ba, haka ya fito batare da ya tsaya bi takan hatta Hafeez ba ma balle ya jira su yi maganar da ta kaishi da Alhajin, tafiyar ma yin ta kawai yk amma dishi dishi yk gani, baya so ya 'kara koda minti guda cikin gidan baya ga haka da babu abinda zai hana shi samawa kansa hutu, sai dai yafi bukatar barin gidan akan hutun da yake ji kamar yana da bukata saboda tsananin yadda bugun zuciyar ya karu yake kuma masa barazanar 'dauke masa numfashi.
Yana jin yadda 'Dan Malikin ke kwala kiran sunan sa da nufin dakatar da shi amma bai ko waigo ba bai ma nuna alamun yaji kiran ba, kuma baya da niyyan tsayawa kamar yadda bashi da burin sake ganin fuskar 'Dan Malikin gaban idanun sa.
Kallo 'daya zakai masa ka tabbatar ba cikin hayyacin sa yake ba, tafiya kawai yake bama ya sanin ina yk jefa kafar sa balle yasan inda ya dosa, haka kawai sai yaga kamar harabar gidan ya 'kara fa'di da tsayi ne, duk 'ko'karin da yake wajen ganin ya fitar da kansa cikin gidan amma abin ya faskara, bai ta6a fahimtar girman da gidan ke dashi ba sai a wannan lokaci.
Gaba 'daya fuskar sa da idanun sa sun koma jajaye, jijiyoyin kansa da gashin jikin sa sun mimmike, banda wani dun'kulallen abu da ya tokare masa kirji yai masa nauyi sosai...cikin ransa yk ji tamkar ba zai yi tsawon rayuwa ba aduniyan nan, kuma shi akaran kansa ma yafi son hakan da ya cigaba da rayuwa yana cin karo da irin wagga lamari daga mahaifin sa gara ace bashi ma a duniyar yafi a ganin sa kenan.
" Har sai yaushe? sai yaushe ne zai canza? Duk da wannan shekarun amma har yanzu bb abinda ya canza game da shi? Sai yaushe zai samu cikakken farin ciki daga mahaifin nasa? sai yaushe zai fuskanci rayuwa ya san cewa annabi ya kafu, sai yaushe tsoron Allah zai dasu masa a zuciya? sai da wani lokaci zai san cewa shi 'din yanzu ba yaro bane shekarun sa sun ja sosai, sai yaushe ne shi kansa zai samu cikakkiyar adalci daga mahaifin nasa? tun yana cikin mahaifiyar sa bai samu kula da adalci daga gareshi yadda ya kamata ba sai yaushe ne zai samu hakan wai? Yaushe wannan mutumin zai bari ta6on da ya dade cikin zuciyar sa ya warke gaba 'daya?"
Duk yadda 'Dan Maliki yaso dakatar da shi 'kin tsayawa yayi za'a iya cewa ma bai san yanayi ba, tunani ne da tarin tambayoyi fal kirjin sa.
Sai dai kafin ya kai ga isa gate 'din da zai fitar da shi daga gidan tuni 'Dan Maliki ya bada umarnin adawo masa da shi, haka securites 'din sa suka cicci6o Adam suka dawo dashi gaban sa bayan sun sha fama da shi, uku daga cikin su sai da suka amshi lafiyayyyun mari daga gareshi amma bai dame su ba, burin su kawai su cika umarnin shugaban su ne, da yake ance sarkin yawa yafi sarkin karfi haka badan yaso ba bisa dole suka dawo dashi gaban 'Dan Malikin suka juya suka fita.
Kallon kallo suka tsaya yi tsakanin sa da 'Dan Malikin bai kuma sake ganin 'yan mata guda biyu daya gani 'dazun tare da shi suna yi masa tausa cikin mummunar shiga kuma mafi munin ma a nan palor ba, bai kuma ga Hafeez ba.
Bai san takamamme me yk ji game da 'Dan Maliki ba amma daga jiki har zuciyar sa yk jin baya bu'katar ganin mutumin kwata- kwata, yana ji da ace yana da iko da tuni ya saka almakashi ya datse duk wata alakar dake tsakanin sa da shi, duk da baya so ya tabbatar wa zuciyar sa hakan amma can 'kasan ransa yake jin tsana mafi muni na ginuwa masa kan mutumin, ba 'karamin jinjinawa 'karfin hali irin nasa yayi ba da har ya iya tsayawa ya dubi cikin idanun sa ma bayan duk wannan abin da shi idanun sa suka gane masa...shi da kansa kunyar kansa da kansa Adam yake yi amma me yasa 'Dan Malikin bai ji kunyar abinda ya aikata ba?
Idanun sa yayi 'ko'karin kawar wa ga barin duban mahaifin nasa a daidai kuma lokacin da sautin muryar sa ya kara'de kunnuwan Adam.
" Dan Allah ka gafarce ni Adam, kayi hakuri..."!
Shine abinda ya fito bakin 'Dan Maliki yana mai lumshe idanu gami da juyawa Adam baya.
Bai tanka ba bai kuma yi niyyar tankawan ba dan bashi da kalma ko guda cikin kirjin sa da harshen sa zai iya furta ga 'Dan Maliki a wannan ga6ar.
Fahimtar cewa bazai tankan bane ya sanya 'Dan Maliki cigaba da magana batare da ya sake duban idanun Adam 'din ba, ba 'karya tsananin kunya da nauyin yaron nasa yake ji ba tun yau ba ba kuma yanzu ba, kawai dannewa yake a 'ko'karin sa na ganin ya dake gudun kar ya raunata tunanin Adam 'din gaba 'daya, balle abinda ya faru yau din dole matsayin sa na uba yaji kunyar sa koda kuwa ace ba 'dan sa na cikin sa da ya haifa bane da kunya balle ya sani sarai shi din gudan jinin sa ne cikakken mahaifi yake agare shi da babu madadin sa a kaf fa'din duniyar nan.
" Nasan ban kyauta maka ba kuma har a yanzun bana kyauta maka nasani dan girman Allah Adam kayi hakuri...".