← Book details Binteee Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 118 OF 218

Sashe 118

Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wannan maganar sosai ya yiwa Anty Madeena ciwo haka ma Ammi da ta samu labari bayan tafiyar su..hatta Raihana itama abin ya 'kona ta.

Salmerh 😘
[13/11/2022, 2:59 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕
*( 'Yata ce)*

*Wattpad@*
_Serlmerh-md_

🅿️ *...68*

........Sosai Anty Madeena take masifa Raihana na tayata, duk da yake ita din ba mai magana bace amma yanayin da lamarin ya kasance sai da yasa fusata ta 'ka'kalo masifa 'karfi da yaji take.taya Anty Madeena dan sosai ransu ya 6aci a ganin su abinda mahaifiyar Amran tayi ba komai bane face cin zarafin su.
Marwa dai na gefe bata ce komai ba.

Da 'kyar Ammi ta samu da ban baki Anty Madeena ta sarara suka yi shiru amma maganar ta kasa barin ransu, wannan kam hatta da Ammin ma 6angaren ta abin haka ne.
Da za'a tona ranta ma tafi su shiga tashin hankali sai dai kawai tana dannewa ne.

Ko da dare kusan kwana tayi tana tunani bata yi bacci ba, musamman idan ta tuna Rayyan ta tuna yanayin rayuwar sa amma yau rana tsaka ake gudun sa sbd lalura ta same shi sosai abin ke yi mata ciwo.
Rayyan dai Rayyan dai.
Ganin baccin ba zuwa mata zai yi ba ya sa ta dauro alwala ta ringa sallah tana nema masa afuwa wurin mahalicci.
Ha'ki'ka 'dan Adam ba'a bakin komai yake ba, duk yadda kake jin kanka kake ji cewa kai wani ne bisa tsari da yaddar ubangiji kake komai, cikin yan kalilan din sakanni zai iya canza maka rayuwa ta inda yaga dama.

Bayan kwanaki biyu.
Ammi ba 'karamin tausayin tilon 'dan nata take ji ba, sosai ta damu da wannan rashin lafiyar tasa, kwana take ta tashi cikin rashin sukuni da fargabar kar ta wayi gari ace mata shima babu shi.

Bata san halin da zata iya shiga ba matukar ta rasa shi duka tasan kadan.ne daga hukuncin Ubangiji amma tasan dole rashin sa sai ya jijjiga ta, yanzu da yake kwance take ganin nasa ma ya takare, abinci wannan sai an tuna mata cin sa kafin take samu tayi aqueezing lkc taci shima ba wani ba mai yawa ba sbd tsantsan damuwa.
Har a lkcn ko dan yatsansa bai motsa ba, yana nan ne tamkar gawa amma an tabbatar mata da cewa da rai tattare da shi....amma ace yana cikin irin wannan mawuyacin halin amma matar sa ta guje shi, duk da tasan yes ba laifin Amrah bane amma sam abin ya matukar bata mamaki, bata ta6a zaton hauka da rashin hankalin mahaifiyar Amrah ya kai har hakan ba.

Sai dai duk ba wannan ne damuwar ta ayanzu ba, burinta Rayyan ne, burin ta taga ya tsaya da kafafun sa tamkar baya, bata da wani aiki a yanzu illa yi masa addu'a ba dare ba rana.

Duk da kusan raba dare da tayi tana tunani hakan bai sa ta kasa tashi sallar asuba akan lkc kamar yadda ta saba ba...domin 'kage take ta taje taga Rayyan ko an samu wani cigaba a lafiyar sa.
Baya ga haka akwai wani abu aranta data idda yanke shawarar aikatawa kuma da shi ta kwana cikin ranta.

Tun kafin gari ya gama yin haske ta kira Fawwaz ta sanar da shi halin da ake ciki, ta kuma nemi shawarar sa kan hukuncin da ta yanke na cewar ko za'a mayar da Rayyan din karkashin kulawar asbiti hankalin ta zai fi kwantawa fiye da zaman sa a gidan alhali babu takamamman me kula mata da shi illah Fawwaz din...Fawwaz yace hakan ma ai karkashin kulawar tasu yake tunda 'dakin da yake a gidan baya da bambanci da na asbitin, duk wasu na'ura da ya kamata su tallafawa lafiyar sa an samar da su suna kuma amfani.

Fawwaz yace tayi hakuri, ta kuma kara akan wanda take yi, dan yasan dole ne ta damu shi kansa karfin hali kawai yake amma sanin da yayi babu yadda zasu yi yasa shi dangana ya mi'kawa Allah komai.

Batun Amrah ma duk ta cire shi a ranta yace a samu wani amintacce inma biyan sa ne a ri'ka yi Ammi sai yana kulawa da Rayyan din.

Ammi da hanzari ta katse shi..dan sam bata jin ta yadda da kowa a wannan halin balle har ta iya bashi ragamar kulawa da Rayyan bazata iya ba.

She wish da namiji ce ita da ta tabbatar babu abinda zai mata shamaki da kulawa da gudan jinin ta musamman a yanzu da yafi bu'katar taimakon wani nashi makusanchi.

Fawwaz ne yace toh sai ayi magana da Sultan yana zuwa yana masa wani abin kafin aga yadda hali zai yi, idan anyi sa'a ma ya tashi nan kusa ai shikenan...dan a binciken su da suka gudanar sun fahimci cewa yana iya farkawa a ko wani lkc ma.

Yadda Fawwaz ya bawa Ammi shawara haka tayi Sultan ne ya fara taimakawa Rayyan 'din da tsaftace jikin sa, a lokacin kuwa sosai 'yan uwa, Neighbours da abokan arziki dama ma'aikatan sa ke zuwa gaida shi, kowa yazo kuwa sai ya tausaya masa matu'ka, masu raunin zuciya kuwa har na zuvda kwalla, ana kuma yabawa sosai da 'ko'karin Sultan akansa shi kansa Sultan 'din yadda ake yaba masan na yi masa dadi dan babu wanda ko alama zai iya zargin sa akan lamarin, sai dai ba'ayi kwanaki uku cikakku ba ya fara jan baya har sai an 'kira shi a waya an tunasar da shi kafin yake tuna cewa ashe Rayyan na kwance.

Anty Madeena da dama ba wani shiri ne sosai tsakanin su ba sai haushi duk ya 'kara cikata, dan ita indai akan alhalin yayantan nan ne toh bata saka kowa sama da su.
Bata dai tanka ba but cikin ranat take jin bb dadi da halin ko'in kula da Sultan ya fara nunawa.
Karyar yau daban ta gobe daban a duk lokacin da yasan bai kyauta ba, ko kuma aka kira shi kafin yazo...galibi ma Marwa ce, idan taji su Anty na mitar rashin zuwan nasa sai ta koma gefe batare da sanin su ta kira shi dan ita kanta bata jin dadin abinda yake yi din, ko bakomai Rayyan ai jinin ta ne, Company, kullum aka tuhume shi sai batun Company ko waye ya fa'da masa cewar Company ne ya dame su a halin yanzu?
Babu wani abinda suke nema a halin yanzu illah lafiyar Rayyan kadai.

Abin mamaki Sultan sai ma ya tsiri tafiya zuwa Lagos batare da sanin Ammi ko Marwa ba, har sai da ma ya sau'ka kafin ya kira ya sanar da Marwa anan su Ammi suka ji labarin tafitar tasa.

Washegari da safe kuwa suka rasa yadda zasu yi da Rayyan.

Dole Anty Madeena da Raihana sai da suka sake 'dago maganar Amrah duk da Ammi ta hana su amma a ganin su yazam dole ne su jimanta a wannan ga6ar sbd kowa na da ranar sa, kowa kagani cikin duniyar nan yana da amfanin da Allah kadai ne ya barwa kansa sanin sa kafin ya bayyana ta ga bayin sa.
A yau ga ranar Amrah, ga bu'katar Amrah nan ya taso musu amma kuma tai musu nisa.

A zahiri mahaifiyar Amrah ta nuna cewa ba 'kauna irin wacce Allah da manzon sa suka koyar da mu suke yiwa Rayyan ba, tunda sun guje shi ne a lokacin da larura ta same shi da har suke tunanin mawuyaci ne ma ya tashi kamar baya, ta mance cewa mutuwa da rayuwa duk na Allah ne.

Ammi shiru tayi tama jinsu, ita kanta abin ya dame ta sosai, tasan ba wai rasa wa'danda zata biya kula mata da shi tayi ba, ba wai ku'din biyan ta rasa ba tsoron ta kawai kar ta 'dauko wanda zasu zame mata ajalin 'daa da kudin ta ne ...baya ga haka ma ga su Huzaifa dake nan kusa amma sam bata ji zata iya basu wannan yadda da amincewar a halin yanzu.

Fawwaz ne da ya zo duba shi shi ya tsaftace masa jikin sa bayan yayi masa duk wani abinda ya san aikin sane hadda ma wanda ba nashin ba sannan ya tafi.

Zugum suka yi a parlourn dake 6angaren Rayyan 'din hirar kirki ma rabon da suyi ta yadda ya kamata har sun manta.
Kowa yayi shiru tunanin da ke kai kawo cikin zukatan su daban.
" Ni wallahi Ammi dama nema masa wata matar akayi aka yi musu aure da sai hankalin mu yafi kwanciya..."

Cike da mamaki gaba daya suke waigo suna duban Raihana da ta fadi maganar da iya gaskiyar ta...

Ganin kallon da Ammi ke yi mata ne yasa ta cigaba da fadin..." Erh mana Ammi, ki duba kiga yadda duk kuka rame kuka canza duk sbd damuwa Ammi, kuma na tabbata rashin Amrah na daya daga cikin abinda ya sake zurfafa abin sbd muna ganin tamkar tunda Amrah ta juya masa baya kowa ma na iya juya masa duk na nasan ba haka bane, amma bazamu ta6a gane gaskiyar ba har sai mun gwada sa'ar mu...a samu wata a aura masa na tabbata baza'a rasa na Allah ba, dan ba duk aka hadu aka zam 'daya ba, a duk lkcn da wani ya kika ya guje ka ya nuna maka kai ba komai bane ma'ana baka da muhimmanci cikin rayuwar sa a daidai lkcn zaka samu wani kuma wutan kaunar ka ke sake ruruwa masa a zuciya...Insha Allah bazamu rasa wacce zata kaunaci Yah Rayyan ahakan sa ba, ta kuma zauna da shi ta kula mana da shi har zuwa lkcn da zai samu lafia, nasan kuma ko shi yaji abinda ya faru da yadda Amrah ta guje shi da kuma yadda matar ta kula da shi bazai ce a a ba, Anty Madeena ko ba gaskia na fada ba....."
Ta karasar da maganar da waigawa ta dubi Anty Madeena.

Wani banzan kallo Ammi ta jefa mata, Raihana da ta fahimci manufar Ammi sai ta kasa da idanu tana jin babu dadi cikin ranta.

Yayin da Anty Madeena ta taji tamkar ta rungume ta sbd yadda shawarar tata ya shige ranta.
Chapter 118 · 0% Book details