← Book details Binteee Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 218

Sashe 6

Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai dai me ita Hajiyar a kullun gani take kamar muhimmancin da ta bawa yarinyar ya fi wanda ta bawa aikin ta, shiyasa ta kafa mata dokar sai dai fa ta nemi wurin saka yarinyar in har aikin zata yi dagaske in kuwa ba haka ba ta hakura da aikin ita zata iya neman wata daban... ba karamin tashi hankalin Zaitun yayi ba, tana matukar kaunar 'yar ta kamar yadda take tsananin son aikin nan na ta domin shine rufin asirin ta, wannan dalilin ya sanya ta nemi shawarar Maman Abdul kan batun, nan take kuwa Maman Abdul tace mata kar ta damu ita zata rika kula mata da yarinyar har taje ta dawo.
"..um um Maman Siyama abin ai sai yayi miki yawa, ga yaran ki ga kuma Muphy?
Kuma ma ai kinga yini nake yi kullun.."
" kar ki damu Zaitun Insha Allahu hakan bazai zaman min matsala ba.."
Maman Abdul bata kai ga rufe bakin ta ba suka tsinkayi muryar Hajja na fadin.." Allah ya sawwaka a cakuda min jikoki na da irin layi..."
Maman Abdul ce tayi saurin cewa " Haba Hajja wallahi abin nan da kike yi babu dadi sam..."
"..Toh ba sai ki fada min abinda ya kamata inyin ba Rahama..."
Tayi maganar tana bankawa Maman Abdul uwar harara...Dukkan su shiru sukayi illah Zaitun dake dan sheshsheka a hankali, dan zuwa yanzun tunanin.ya fara cunkushewa, tana tsoron ta isa ga6ar da shekarun ta zasu gaza cigaba da daukan wasu abubuwan.

Gyara tsayuwa Hajja tayi tana cigaba da fadin..." Ni dai na gama magana babu wanda ya isa ya caku'da min jikoki da 'ya'yan shegu in rainon take so ta kawo ni nan zan mata ta rika biya na..."
Ta kai karshen maganar ne tana me ballan goron dake hannun ta.

Ido sosai Mmn Abdul ta bude tana duban Hajjan da kyau wai ita zata yi raino a biya ta..bacin ko kadan bata taba nuna fuskar rahama ga yarinyar ba dai dai da rana guda, taya Zaitun zata iya sakin ranta ta bar mata rainon 'yar ta...tana cikin tunanin ta tsinkayi muryar Zaitun cikin kuka tana fadin
"....Ni dai Hajjah dan girman Allah ki daina sheganta min yarinya, wlh yarinya ta 'yar halak ce ba shegiya ba...zan fi jin dadi ni ki dinga zagina akan yarinyar nan...".

" Wannan kuma sai ki fadawa wanda bai san dan yau ba, ni din Zaituna ba ta yau bace halin 'ya 'yan zamani kuwa jimla jimla babu wanda ban sani ba, ban mayi shahada bane dana ce zan miki rainon inda ke wata ce gode min ya kamata kiyi ba kuka ba...mthew ta karashe da jan tsaki tana komawa dakin ta.

Maman Abdul ce ta kwantar mata da hankali tare da nuna mata cewa kar ta wani damu tunda tana gida ga kuma Siyama tunda anyi hutun makaranta tayi mata alkawarin bada dukkan kulawar ta ga yarinyar koda kuwa tana wajen Hajjan kamar tana wajen tane.

Da kyar Zaitun ta yadda ta amince da batun sai dai tana ji cikin ranta cewa daidai da rana guda idan taga rainon bai mata ba zata bar aikin ne kawau gaba daya ta cigaba da kula da 'yar ta inyaso tai ta yawon neman aikatau din goye da 'yar ta duk da tasan hakan yafi wahala amma gwamma hakan da ta zuba idanu tana gani ana cin zarafin yarinyar nan.

Maman Abdul ce tace mata kuma kar ta daga hankalin ita Hajjan yawan kudi bai damin ta ko dubu guda ta bata idan lokaci yayi bazata raina ba.

Sai da ta koma daki tayi zaman lissafi, kenan idan ta bada dubu daya na rainon Mufeeda dubu biyar ne zai rage mata sam bata damu ba duk da raguwar adadin kudin dan matukar zai ishe ta hidimar yarinyar aganin ta shikenan ita kam me zata saie nema, Mufee ne kadai damuwar ta kuma ta tabbatar dubu biyar zai ishe ta tayi mata duk abinda ya dace da shi kowani wata.

Da haka ta amince ta fara barin Mufee a gida, amma tana wajen aikin hankalin ta a rarrabe da kyar ta fara sabawa da rashin Mufee kusa da ita...kullum idan ta dawo da dare sai tayi wanki saboda kayan ta ba yawa ne da su ba...itama Mufeen tana so ta kara mata wasu kayan sawan amma bata da sukunin yin hakan saboda karancin kudaden ta.

Fara barin Mufee a gida da kwanaki goma sha daya Baban su Siyama ya dawo daga tafiyar da yayi ya dawo ne cikin dare bayan har Zaitun sun yi bacci, dan ita har ga Allah bama tasan da dawowar shin ba kasantuwar bacci da yake mata nawi musamman saboda gajiyar take yini kwasowa wajen aiki kuma Alhamdulillah tunda ta fara barin yarinyar bata ta6a zuwa ta same ta cikin yanayin da zai sosa ranta ba kamar dai yadda Maman Abdul tai mata alkawari.

Tun wayewar gari da taci karo da mutumin ta fahimci cewa ba mutumin kirki bane shi musamman saboda yadda yake binta da wani irin kallo.

..Shi kuwa ta 6angaren ta tun ganin sa da ita na farko yaji yarinyar tai masa a ransa, sai dai da yake tun da safe da yaje gaida Hajja tayi masa bayanin Zaitun din a yadda ita ta fahimta yasa tunanin sa canza wa...kamar an tambayi Hajjan ko kuma ance tai masa bayanin ta.

...Ashe matsala guda tak da Maman Abdul din ke fuskanta daga maigidan nata kenan saboda muguwar halayyar sa ta neman mata, wanda akansa ne kadai suke yawan samun matsala da shi.

Ko lokacin zuwan Zaitun gidan ashe Maman Abdul bata dade da dawowa daga gidan su ba in da ta tafi ta barwa Hajja yaran saboda takaicin halayyar Mijin nata, kwanaki kalilan da dawowar ta Hajja ma tace zata je wajen 'yan uwan ta huta saboda bar mata yaran da Maman Abdul tayi ba karamin jinjiki tayi ba kafin ta dawo acewar ta dole itama taje ta huta, shiyasa ko lokacin zuwan Zaitun din ta samo kofan Hajjan a garkame, bayan tafiyar Hajja washe gari shima Baban Abdul ya tafi shine sai jiya ya dawo.

Sosai Maman su Abdul ta tsani wannan halayyar tasa gefe guda kuma tana tsoron ya debo mata wata cuta...duba da irin zamanin da ake ciki yanzu.

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya wa Zaitun wani iri, sosai mutumin nan ya matsa mata ya sa ta gaba da kallo da shishshgi wataran har dakin ta yake shiga wai ya siyowa Feefy biskit Zaitun kamar tayi ihu take ji dan haushi amma haka ta basar.

Sam mutumin bai mata ba, sosai ta tsani ganin sa har Allah Allah take yi ta bar gidan saboda shi.

...Mufee na shan wahala a wurin su Siyama dan karfi da yaji rainon ta ya dawo hannun su musamman da yake yanzun su ke yini da ita a gida.

Kwatsam sai aka wayi gari kanin Maman Abdul ya rasu ta shirya ta tafi gidan nasu...bata dawo ba kuwa har kusan kimanin sati uku...aka barwa Hajja su Abdul da Siyama ga kuma yarinyar Zaitun itama.

Yarinyar har 'yar rama tayi dan bata samun kula yanda ya dace kamar yadda take samu a baya, Ceralac din ma sai lokacin da aka ga dama ake bata...a hakan ma wani sa'in sai su Abdul suzo su shanye mata sai daga baya ne Hajjan tayi dabarar ajiyewa saman wardrop ganin kamar Zaitun din bata jin dadin yanda yake karewa cikin kwanaki kalilan.

Har targade su Siyama suka yiwa hannun Mufee ranar Zaitun tasha kuka kamar ranta zai fita, ranar Hajjan da kanta ta kai ta wajen gyarawa bisa jagorancin Baban Abdul Zaitun sai da tai kwana uku bata leka wajen aikin ta ba, ranar da ta tashi komawan ma da Feefyn taje goye abayan ta nan matar ta tuhume ta, Zaitun dalili ta sanar da ita sai tace ai shikenan amma yanzun ma har ta riga ta nemi wata mai wanke wanken ita kuma sai dai ta koma kitchen sannan aikin cikin kitchen bazai yiyu tana tare da yarinya ba.

Haka dole washegari ta baro Feefyn agida jikin ta sanyi qalau, sai da ma tayi mata addu'o'i kafin ta baro ta.
Hankalin ta baya ta6a kwanciya kuwa har sai taga ta dawo gida.

Amma daga ranar da Maman Abdul ta dawo gidan ne fargaban Zaitun ya kare kaf.
Sai dai kuma wata sabuwar fitina da Baban Abdul din ya tsiro da shi ne yake damin ta, ko kunya baya ji ballantana tsoron Allah, dan har wajen aikin ta yake binta idan ya daidaici lokacin tashin su ya kusa sai ya jira har ta fito dan komawa gida anan ne zai ta mata maganganun banza...har zuwa inda suka rabu sai ya dau wata hanyar ita kuma tayi gida, bata ta6a tanka masa ba, kamar yadda bata ta6a gigin sanar da kowa ba, dan Maman Abdul tai mata halacci arayuwar ta, halaccin da bai kamata ace taji wannan irin maganar daga gareta ba.

Kuma wani sa'in bata ganin laifin sa domin ba shine mutun na farko da ya fara yi mata kallon marar kamun kai ba amma tuntuni ta kar6i hakan ta kuma shiryawa wanda zai biyo bayan wannan din ma ko da ace munin sa ya zarta hakan ne, in dai akan Mufeeda ne zata iya juran komai da za'a mata a shirye take ta fuskanci koma wani irin kalubale matukar abin ita kadai zai shafa batare da yarinyar ba.

Zuwa yanzun ta gama fahimtar inda mutumin ya dosa amma bata ta6a tankashi ba, in dama Allah ya taimake ta ba yinin gida take yi ba in kuwa ta dawo gidan bata ta6a gangancin barin kofar ta abude gudun kar ya shigo mata..komin zafi haka zata rufe musu kofa kirib gashi su ba fanka ne da su ba..haka zata hana idanun ta bacci tayi ta wa yarinyar fifita da wani dan kwali da ta yago kwanaki.

Farin ciki take ji idan taga yarinyar ma bacci cikin kwanciyar hankali.
Burin ta a yanzu bai wuce taga Baban su Abdul ya koma inda ya fito ba.
Chapter 6 · 0% Book details