Sashe 42
Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ko da yy wannan zuwan kuwa bai kara zuwa ba har da aka 'dauki tsawon wani lokaci, sannan ya nemi inda suke, dan auren ta ya mutu tuntuni sakamakon matsawar dangin miji da tayi ta fuskanta kan rashin haihuwar da basu samu ba, ita har har mijin babu wanda ya tsira, afa'dar su kuma ta kawo musu bare 'dansu nata hidima dashi bazasu iya jure gani ba dole ya sake ta ya 'kara aure, yaso fahimtar da magabatan nasa cewar ko da bai saki Talatun ba zai iya auren sa kamar yadda suke so tunda Allah ya bashi abinda zai iya rike su da shi suka ce sam 'karshe dole sai da aka rabun hankalin kowa ya kwanta.
So da 'kyar Jibrin ya samo inda take bisa jagorancin tsohon mijin nata a lokacin ma already tayi aure na biyu shekarar su biyu suka rabu tana shirye- shiryen yin wani auren ne karo na uku.
Duk wata kulawa ta mahaifi Jibrin bai iya bawa Adam ba, bai iya jansa ajiki ba, idan yazo din ma banda gaisuwa bb abinda yk ha'da su, bb wata sha'kuwa ta 'da da mahaifi babu kyautatawa sam, bai san cin Adam ba balle sutturar sa, bai san lafiyar sa ba ina ya kwana ina ya tashi duk basu dame shi ba, bai san damuwar Adam ba, bai san ilimin sa ba bai san komai da ya danganci Adam ba.
Duk da hk Hajiya Talatu bata ta6a shiga tsakanin sa da yaron ba amma tuni Adam yasan komai game da labarin mahaifiyar sa da irin zaman da tayi da mahaifin sa kuskuren da Hajiya Talatu tayi shine na rashin 6oye masa komai da tayi.
Tun kuma lokacin da Adam yaji labarin mahaifiyar sa har zuwa lokacin da ta rasa ranta yk jin zafin mahaifin sa a ransa har yau kuma hakan bai canza ba.
Jibrin yazo ya auri wata mata amma bata haihu da shiba kasantuwar babbar mace ce ta kuma riga ta gama haihuwar ta kafin suka yi aure.
Ganin yadda yaranta ke zuwa gidan sa suna watayawa son ransu da dukiyar sa ne ya sanya shi fara sha'awar dawo da nasa 'dan shima gaban sa ya kula da shi a kokarin sa na ganin bai zama inuwar giginya ba, a time din kuma Adam har na aji na farko a Jami'a, ba 'karamin mamaki Jibrin yayi ba 'kwarai da gaske, da yaji sau'kar Alkur'anin Adam din har sau biyu har 'kwalla sai da ya zubar domin yaga kokarin Hajiyan sosai take yayi musu alkawarin kujerar Hajji ita har Adam 'din, koda ya bayyana 'kudurin sa Hajiya Talatu bata ce komai ba ta dai ce ya jirayi zuwan yaron yaji ta bakin sa dan ita bata da cewa.
Taso tace wani abu kafin ma zuwan Adam 'din amma gudun yaga kamar tana ziga yaron ne ya sanya taja bakin ta tai shiru, tana kuma da yakinin Adam din da kansa shima bazai amince ba.
Ilai kuwa hkn akayi, dan 'kin amincewa yayi, 'karshe jibrin dole ya koma inda ya fito bayan ya cika Hajiya Talatu da Alkhairi akaro na farko cikin rayuwar sa tun rike masa Adam 'din da tayi.
Alkhairin da ko kallo basu ishi Adam ba, tun ma kafin Jibrin ya bar gidan Adam ya fara masifar ta mayar sa da kudin sa, su basu da bukata, ai ko abaya basu mutu sbd rashin kudin sa ba dan haka a yanzu ma kudin bazasu tare musu komai ba..kuma shi bai ce yana so abiya masa Hajji ba, da kudin sa yake so yaje halak 'din sa gumin sa bada wani ba.
Jibrin murmushi kawai yayi ya juya ya fita yayin da Hajiya Talatu tai shiru tana duban kudin da tunanin yadda zata yi da su.
Dan tasan taurin kai irin na Adam bazai ta6a yadda yy amfani da shi ba kamar kuma yadda yace bai amshi kyautar kujerar Hajjin ba haka 'din bai kar6an ba while a wannan ga6ar tasan yanada bukatan kudi kodan hidimar karatun sa ma...da kyar ta shawo kansa ya dan sauko daga fushin rike kudin da tayi ma amma duk yadda taso ya anshi kudin bai amince da hkn ba...suna cikin rashi a lokacin dan mijin da ta aura ba me karfi bane kamar na baya amma Adam yafi gane yaje yy ko wani irin aiki ne ya samo ku'din sa yy amfani da shi fiye da yayi amfani dana Mahaifin nasa Jibrin...Adam bai ta6a ambatar Jibrin da sunan da kai tsaye zaka fahimci cewa mahaifi yake agare shi ba _Alhaji_ yake kiran sa da shi shima 'din sakamakon arzikin zuwa saudi da ya san samu.
Shi kansa Jibrin ya 'dauki abin wasa sai da lkcn fara shirye- shiryen tafiya yayi Adam ya tire sam shi babu inda zashi.
P.An Jibrin cikin zuciyar sa yace " kaji marar rabo" har ga Allah shi bai ta6a gani ko jin tarihi makamancin wannan ba, abin mamaki...Hajji fa..?amma ana bin sa yana kaucewa.
Jibrin kuwa cewa yayi shifa idan ya cire kyauta baya maida shi.
Karshe Adam cewa yayi sai dai mijin Hajiyan da ita suje amma shi babu inda zashi.
Aikin carwash, gareji, welding, capentary, leburancin gini, hatta kasadar gyaran wuta sai da yy, ha'kar Soakaway da borehole aikin painti da saka tiles, ha'da satelite bb irin aikin da Adam be yi ba a rayuwar sa, yayi aikin driver a wani gida ma, dan tun yana 6oyewa Hajiyan har tazo ta fahimta tayi masa fa'da amma 'karshe dole ta kyale shi, duk da irin tarin dukiyar da Jibrin ya tara ya kuma kafa tarihin da kowa ya san erh lallai yana da dukiyar amma sam basa gaban Adam tamkar ma bai san da wanzuwar sa ba.
Tun daga lokacin kuma Jibrin yake shiga rayuwar Adam din a hnkl batare da ya sani ba, dan shima ganin shekaru sun tasammasa haikan bashi da wani da zai kira nashi illa Adam 'din yasa ya 'dan fara shiga taitayin sa, duk da yk dama can yana kaunar yaron kawai dai yafi bawa harkokin sa muhimmanci ne fiye da komai, kuma rashin damuwar sa ya ta'allaka ne da tabbaci da yk dashi na cewar Adam din yana hannun da yasan baza'a ta6a barin sa ya koka sbd damuwa ba, zai samu cikakkiyar kulawa tamkar yana hannun mahaifiyar sa shiyasa bai wani damu ba.
Abin mmk duk inda Jibrin ya fahimci Adam na zuwa leburanci sai yaje ya sa an dakatar da shi ya kuma nuna musu cewa 'dan sa ne jinin sa, fushi yy dashi ne shiyasa kawai yake huce takaicin wajen aiki da su, 'karshe sai yy musu alkhairi ya tafi ya bar su da 'dimbin mamakin Adam.
A ganin su taya me uba kamar Jibrin 'Dan Maliki zai na aikin sana'ar leburanci irin wanda su suke yi, bacin irin su tun kafin a haife su aka tara musu dukiya suka tashi cikin sa, wasu na ganin wautar Adam yayin da wasu ke ganin kawai saukin kansa ne yy yawa.
Duk kuwa yadda Jibrin yaso yi masa bazata da aiki amma Adam yaki duban ko'ina, dan acewar sa bai nemi aiki da kowa ba dan hk koda an neme shi da appointment nunawa yk baya bukata dan sarai yasan aikin waye...infact ma shi be gama schl ba balle har ya kaiga neman aikin dan haka duk daraja da girman aikin baya masa gani.sau biyo acewar sa baya bukatar ko guda.
Sosai hakan da yake yi yake 'kona ran Jibrin ya kuma rasa yadda zai yi da shi.
Idan sun ha'du zai gaida shi a mutunce babu rashin da'a amma daga hakan babu wata magana kuma, kuma har yau yaki amincewa da duk wani abinda zai fito daga hannun sa ko ta dalilin sa gaba daya ya rasa me ke damun Adam din.
Da kansa ya budi baki ya bashi hakuri da tunanin ko rashin kulawa da bai bashi bane abaya yk damun sa amma Adam yace hakurin na menene kuma shi bai masa laifin komai ba.
Ba 'karamin azabtar da zuciyar Jibrin yk da irin wannan halayyar tasa ba cikin su kowa na ganin 'dan uwan san baya kyauta masa.
Dan Adam zuciyar sa cike take da haushin abinda yayiwa mahaifiyar sa ne gashi yaki ya dube shi da sunan 'dan sa har sai da yaga ya tasamma shekarun girma sannan yazo yana tarwatsa masa duk wani shirin sa na sana'a da ke yi yayin da Jibrin ke ganin dansa yafi karfin yy irin wannan sana'ar while yana raye a doran 'kasa.
A hk rayuwa ke tafiya musu tsakanin shi da mahaifin nasa, ko da Jibrin yayi fushi baya iya doguwar fushi da Adam 'din dole yake sakkowa amma still Adam ya kasa fahimtar sa.
Time 'din daya gama schl ma kyautar mota ya bashi wacce ya tabbatar samari irin sa ke burin mallaka amma abin mamaki Adam ya ki ansa yace baya bukata, daga can makaranta ma aka bashi appointment da sunan sbd kyan da takaddun sa suka yi ne wannan ma Adam ya rufe idanu yace baya bukata kuma bai bari Hajiyar sa tasan da batun ba.
Su biyu suke zaman su yanzu sakamakon rasuwa da mijin Hajiyar na karshe yayi bayan dawowar su daga Hajji, tun daga nan kuwa Hajiya Talatu ta ha'da duk kudaden wajen ta da mafi yawa daga 'Dan miliki suke ta bude wajen saida abinci, dan acewar ta ta gama aure yanzu, yayin da Adam ya tattara nashi da ya tara da gumin sa ya fara sana'ar sayar da kerosine, engine oil da sauran su a bakin titi, acewar sa ai wannan kam ba karkashin wani bane balle ai masa ma'kar'kashiya.
Da zai tafi service sai da ya 'dora wani akai sannan ya tafi.
Duk da yake Adam baya bada fuska amma sosai yadda 'Dan Malikin ke damuwa da lamarin Adam abin ke mata dadi, aganin ta ko ba komai dai dole Adam watarana za ya nemi uban nasa domin da uba ake ado, kuma ba laifi tana kokarin.yi masa fa'da kawai ya kasa fuskantar ta ne.