← Book details Binteee Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 156 OF 218

Sashe 156

Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ido na zaro sosai ina kallon ikon Allah wato ruwan dake bin inda matar ke kwance da kuma jinjirin dake kuka a 'kar'kashin ta.

Baya nayi kokarin ja amma hakan ya kasa samuwa gare ni, fizgar hannu na naso nayi da niyyar gudu amma matar nan sam bata da niyyan sake min hannu.

Ba 'karamin tsorata nayi ba, hakika wani tashin hankalin yafi gaban wani, dama haka ake haihuwa ?
Na tambayi kaina da kaina.

Ko kuwa dai ita wannan 'din ce nata yazo ta wannan sigar..ma'ana daban da saura..?

Ina cikin tunani da son tantance gaskiyar lamarin da nake da da bu'katar sani, ji nayi matar nan na sakin hamdala a fili gami da saukar da ajiyar numfashi mai zafi, hakan ma ya sake bani tsoro, still tashi na sake niyyar yi amma dole na koma na zauna sakamakon hannu na da naji cikin na matar har yanzu bata sake ni ba.

Numfashi kawai take sau'kewa sai dai zuwa yanzun ya koma a hankali, banda kallon matar nan da mamaki babu abinda nake yi tunanin nawa ma tuni ya tsaya cak, idan na kalli Babyn sai na kalli matar da har yanzu ta kasa saki na.

Babu wanda ya sake yin wata magana a cikin mu illa ni da ke ta muzurai.

Tsawon mintina sama da biyar muna ahaka sannan naga matar ta fara sake yin wani nishin amma wannan karon babu abinda ya fito...salati ta fara tana kiran sunan Allah da alamu ba 'karamin ciwo take ji ba a yadda naga yanayin ta...

Mun 'dauki tsawon lokaci a hakan sai kuma na rasa takamammai abinda ya kamata na aikata.

Zuwa lokacin na gama fahimtar haihuwa matar tayi, na kuma fahimci irin ciwo da zafin dake cikin haihuwa, ashe mu ganin yara kawai muke muyi farin ciki bamu san wahalar da ake sha kafin a haife su ba, hakika dole mu jinjinawa iyayen mu, dole mu yi musu biyayya muddin ran mu, bamu da komai bamu da wani abinda zamu iya yi ko mu biya su da shi face mu yi biyayya ga duk wani abinda muka san zai sanya su farin ciki.

Na tausaya mata sosai, domin tuni na fara kuka wanda har zuwa lokacin wannan babyn na kwance inda uwar ta haifo ta babu wanda ya ta6a ta har ta yi kukan ta ta gaji tayi shiru.

Da kyar Allah ya taimake ta ta sake haifo wani Babyn wanda hakan shi ya dakatar da nishin da take yi ya kuma dakatar da zafin ciwon da take ciki ta koma sauke wani numfashin tana sakin hamdala cike da galabaita a zahiri.

Shi kam na biyun bai ko motsa ba, kwancen sa yake yadda ya fito kuma ko idanun sa basu motsa ba balle yayi kuka kamar na farkon.

Kallon ta na sake yi na kuma dubi yaran duk biyu ina jan hannu na domin zogi yake min sosai.

Sai da ta dube ni sannan ta saki hannun nawa tana murmushi, da alamu ma mantawa tayi da cewa ta rike min hannu.

" Da na sake ki da tuni kin gudu kin bar ni ko...?"
Matar ta fa'da tana duban fuska ta muryar ta na rarrabewa kuma cike da sanyi.

Sam ban bi ta kan maganar tata ba sai ma idanu na da suka 'kara fitowa waje ina yarfe hannun idanu na akan yaran nace...." Sannu hajiya....".

Inda ta ri'ke 'din har sai daya koma ja saboda ba 'karamin riko tayi min ba.
" Na haifi yaran ka Doctor, sai dai ka yafe min a jeji na haife maka su..."
Abinda naji ta furta kenan madadin amsar sannun da nai mata.

Ido ta lumshe sannan ta sake furta"...Abinda na so yi maka suprise akan su sai gashi Allah bai nufa in haife su a hannun ka ba, Allah bai nufe ka da fara ganin jinin ka a dunia ba, Allah bai sa kaine zaka amshi haihuwar yaran ka da kanka ba...ka yafe min miji na, hkn sam ba daga cikin shirina bane, shirin Allah ne...".

Tayi maganar hawaye na gangaro mata ta gefe da gefen idanun ta.

Ni kam tuni hankali na ya bar kan matar ya koma kan yaran dake gaba na, so nake na 'dauki ko da 'daya ne daga cikin su amma yanayin da naga suke ne ya hana ni..ko ka'dan ban saurari ko kalma guda cikin maganganun matar ba balle na fahimci manufar ta.

Yun'kuri tayi ta tashi zaune, ganin ta zauna ne ya sa hankali na komawa gareta, ina nuna yaran da zararren idanu nace" Hajia har guda biyu fa?"
Murmushi matar tayi min kawai batare da ta bani amsa ba.
Sai na cigaba.
" Hajia na tsorata sosai...dama haka ake haihuwa da wahala..?"

Murmushi kawai tayi min bata furta komai ba har a lokacin....dube dube naga ta fara ni kuwa ban wani kula da hakan ba sai faman rarraba idanu da nake akan yaran wanda 'daya ke motsi 'daya kuma tun fitowar sa bai motsa ba.

Hannu na ta kamo sai na kalle ta da sauri dama a 'darare nake, can inda ta yada jakar ta inda na kamo ta zuwa nan ta nuna min.

Nima sai na kalli wurin da sauri na mi'ke na 'dauko mata.

Razor blade naga ta ciro cikin 'yar purse 'din ta ta fara 'ko'karin yanka cibin yaran, da sauri na rintse idanu.
Tsananin kamar da ke gare su ne ya sanya cibiyar su ya kasance a ha'de...a fa'dar ta.

Sai da na tabbatar ta gama yankewa kafin na bu'de idanu na..." Dama haka ake yi...?"
Na tambaya ina kallon su, kai kawai ta 'daga min bata ce komai ba har ta kammala abinda zatayi, 'dan kwalin ta ta warware sai kuma ta tsaya kallon yarinyar tana murmushi tace" Allah sarki"
Inda tayi maganar tana shafa cikin yarinyar, da muka ha'da ido sai tayi min murmushi.

A karo na biyu na sake jin sautin muryar ta dake fita da wani salon birgewa.

Cikin raina na ayyana tabbas wannan matar 'yar gayu ce ta 'karshe.
Komai nata gwanin birgewa.

'Dan janye, hannun ta dake kan cikin yarinyar tayi sai lokacin ma na lura da wani ba'kin abu dake a cikin yarinyar, girman sa kamar sulalla kuma ba'ki ne si'dik kamar an sanya gawayi.

Ni kaina nayi mamakin ganin abin dan ban ta6a ganin irin shi jikin duk yaran da nake ,dauka na mutane ba, yayin da na lura ita matar ganin abin farin ciki ya sanya ta.

Nuna min shi tayi tace" Kinga wannan? sak irin na mahaifin ta ne..yarinya ta iya gado"
Ta 'karashe tana murmushin dana tabbatar tun daga zuciyar ta ne.
Duk da nakan lura lkc zuwa lkc takan dan rintse idanu da alamu wani ciwon na dan tsinkulin ta amma bata bayyana shi a fili ba.

Nima murmushi nayi mata dan ban fahimci zancen da kyau ba, hankali na duk na kan yarinyar ne.
Na'de jinjirar tayi tana ta motsi da bakin ta g dukkan alamu abu take so ya shiga bakin ta...sosai naji sun shiga raina, lokaci guda wani so da kaunar su ya ratsa cikin zucia ta gami da tsananin tausayin su gaba 'daya har da mahaifiyar ta su ma, dan yau ne rana na farko a rayuwa ta da naga yanda mata ke shan wahala wurin haihuwa ganin ido na....
" Allah ya baki aljanna Innata".
Shine abinda na fa'da cikin zuciya ta sai dai ga mamakina matar nan 'daga kai tayi ta kalle bi gami da fa'din" Ameen Ameen."
Wannan furucin ne ya sani fahimtar cewa a fili nayi maganar ba a zucia ba.

Ganin tana shirin na'de 'dayan yaron da bai motsi cikin mayafin ta ne ya sanya ni saurin ciro 'dan kwalin da ke kaina na mi'ka mata...

Bata yi musu ba ta amsa bayan ta bini da 'kayataccen murmushi mai nuna alamun godiya.

Kan cinya ta 'dora mai motsin ita kuma ta rungume 'dayan bisa 'kirjin ta...ban sha wahalar daidaita rikon yarinyar ba dan kuwa wannan ba sabon abu bane a wuri na rike jirajirai abu ne da na riga na sabarwa kaina da shi tun ba yau ba.

Hawaye ne ya sau'ko mata a hankali na tausayin yaran ta, baya ga haka ma dauriya kawai take yi amma tsananin ciwon ciki ke damun ta, cikin sanyi ta furta" 'kanwa ta ya sunan ki?"

" Zaituna".
Na bata amsa a takaice ina sake duban fuskar babyn dake hannu na, koka'dan ban ji 'kyankyami ko wani abin ba, sai ma wani 'kaunar babyn dake ratsa ni kusan kowacce da'kika na shiga da fitan numfashi na.

Murmushi matar tayi min tana kallo na tace " ni kuma sunana Nadia...Kano nake zama da miji..."
Shiru tayi batare da ta 'karasa abinda tayi niyyan fa'di ba sai tayi 'kasa da kanta tana cihe la66an ta.

Ita ka'dai tasan me ta ke ji da yasa ta yin hakan amma hakan bai hana ni fahimtar hakin da take ciki ba.

" Sannu Hajiya"
Na furta cike da tausayin matar nan mai suna Nadia.

Indai haka haihuwa yake ai dole aji tausayin mata, balle ita da ta haifi har guda biyu, Ni fa tunda nake 'kwa'kwar zuwa gidan masu jego sau 'daya na ta6a ganin wacce ta haifi biyu lokaci guda shima 'din 'dayan kwanan sa 'daya ya rasu ya bar 'dayan, ban sani ba ko Allah ne kawai bai so nuna min hakan kafin yau 'din ba.

Ina cikin tunanin naji matar na fa'din" Daga Damaturu nake zamu wuce maiduguri daga can kuma zan hau jirgin da zai kaini zuwa kano sai kuma cikin rashin sa'a muka yi katari da tashin hankalin nan....".
Shiru ta sake yi tayi 'kasa da kanta, yayin da na tsura mata ido zucia ta cike fal da tausayin ta, gami da mamakin ta, ashe har jirgi ma take hawa...na ayyana cikin raina.

Yaron dake 'kirjin ta ta rungume da 'karfi hatta hannayen ta ma da na lura sai naga rawa suke tamkar mai jin sanyi.

Hakan sai yaso bani tsoro, baya ga haka ma fa da kyar take ta rattafo min wannan bayanin muryar ta na rarrabewa.
Chapter 156 · 0% Book details