← Book details Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 99 OF 337

Sashe 99

Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Umma yau na ganshi ido da ido wallahi wanan mutumin lalai mugune mugune na karshe umma yau na fara ganin a yau din kuma ya nuna min koshi waye.
Wa kika gani kika shigo min haka a razane umma wanan Alh daya kashe min mahaifina shina gani asibitin.
Farine ba sosai ba dogo mai karfi da da dan gemu ga jajayen idanu maicin mutunci da zarafin mutane ko a gaban kowa.
Yaci muna mutunci ya tozarta mu yau a gaban kowa umma akan abincin da mommy ta aike mu mukai yace mu dawo dashi mu fadawa daddy shi Nuhu yace daddy baiyi abincin da zai aika masa ba.
Fa,izace ta shigo take fadin ana kirana a falon Daddy kallon umma nayi inda take zaune ta kura min ido kafin in mike umma ke fadin.
Ina fatan ba rashin mutunci kikaiwa yayyun mahaifin ki a fitan ku ba da yarbanci babaren data fada shine yasa Faiza dan kallon mu kaina kada nabi bayan Fa,iza din muka fita.
Suna zaune a falon har mommy din muka shigo wuri Fa,iza ta samu ta zauna na duka a gefen ta tare da dukar da kaina a kasa shima daddy din kanshi na kasa yana dan bubuga kafan shi a kasa.
Kafin ya dago yana fadin ungo Sahiba waitin dat man talk at d hospital ?
Nan na fara korawa daddy komai tun shigowan mu asibitin har fitowan mu nakare da fadin that,s all i know daddy.
Ya nisa tare da fadin fine kinyi kokarin fada min komai saidai ku meya sa zaku boye min koda yake ba laifin ku bane laifin uwarkune gata zaune.
Amma ina son ki sani duk da sudin yan uwanki ne na jini saidai a bangaren su yanzun ba haka suka daukeki ba su a wurin su don yanzu Nuhu da yan uwansa sun bata komai a yanzu.
Saidai ina son don Allah ki nisanta yaran nan da shiga harkan wanan mutumin da baida tauhidi a zuciyar shi kada ya taba min yayana don wanan kam bazan kyaleshi ba idan nayi hakkuri akan komai.
Allah sarki mai uwa da uba raye a duniya ya godewa Allah na fada a zuciyana ga Daddy duk abinda Alh yake masa bai ji bacin rai ba, sai yau da yakai ga yayan shi ranshi ya baci haka dasu.
Saidai dama idan yana da wata manufa a kaina don kai abinci yau aka saba kaiwa harshi abinci asibiti idan ya kwanta.
Eh mommy haushin bai samu kashe daddy da sukai niyar yi ranan ba ya komawa dan uwan shi shine yake jiwa haushi a yanzu.
What daddy ya fada karfi.
Nace a rude yes dad they atterm to murder you on that day.
How do you know all dis ?
Ya tambaya yana tsure ni da idanu hannu na ware tare da fadin i dont know .
Amma dai haka din ne daddy i know haka din ne sunyi plain su kashe ka a ranan sai ya juya masu akan kanin shi yayi arziki bai mutu ba.
Ke kinji hjy kinji wanan maganan kuma da yarinyar nan ke fada yanzu na sake fadin yes dad abinda suka shirya ma ke nan.
Innalillahi suke maimaitawa a lokaci daya mommy na fadin dama akan ka Alh aikai wanan aiken kai ku bar saurin yarda da orin zancen nan balle a bakin yarinya karama irin Sahiba.
Ya dago kai ya dan kura min ido na dan lokaci na wani huro iska a bakina tare da hade yatsun hannuna a wuri daya kamar ina wasa dasu suna dan bada sauti kas kas.
Tashi kije Sahiba daddy ya fada ban jira komai ba na mike na fita daga dakin daddy ya kallo sauran yaran dake wuein yana sauke numfashi tare da fadin.
Ku saurari abinda zan fada maku yanzu kuji kada inji wanan zancen ko a cikin gidan nan balle wani waje da fatan kunji abinda na fada suka amsa da eh daddy.
Suka mike suka fice daga dakin suna jin wani iri a zuciyoyin su , don haka ba wanda ya iya magana a lokacin ga baki dayan su.
Shiru dakin yayi na dan lokaci kafin hauwa tace waiko yarinyar nan dai yar securo ce ko me dai don nifa abin Sahiba ya fara ban tsoro.
Meye na tsoro a nan kawai dai wani bauwane na daban Allah yai mata kila ba,a sani ba amma ai zamu gane hakan udan zancen cikin anty ya fito gaskiya lalai Sahiba watace na daban a cikin mu.
Tsoro nake ji idan ba yar wani cult bane fa don kusan wanan haline na diyan kabilun nan su ba su daukeshi a komai ba kamar ma ado yake a garesu.
Don Allah hauwa ki bar wanan zancen don ni kin fara ban tsoro akan yarinyar nan wallahi wanan maganan da kikeyi ya fara firgitani da ita yanzu.
Kai don Allah ku bari da muguwace ai a kaina zata fara nunawa ni dake tare da ita akoda yaushe kuma ai da yar cult ce da ba zatayi ibada haka ba don sahiba badai a tuna mata lokacin sallah ba dai.
Shine kuma fa gaskya ba cult takeyi ba kawai dai wata kila iskokai ne a kanta suke mata hakan .
Chapter 99 · 0% Book details