← Book details Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 262 OF 337

Sashe 262

Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kira bisa kira haka muke samun kira a lokacin saidai amsa dayane shine bamu san wanan zancen bamu don haka dole mutum ya kyale mu. Karshe ma kashe layukan wayan mu nayi sai can dare nake kunnawa in shiga median naga sakonin da suka shigo min a yinin ranan. A irin hakane har ya Abubakar ya samu ganina a online yai min magana na bashi amsa da muna kalau ga dalilin kashe wayan namu a lokaci. Yake fadin cewa hankalin shi ya tashi kwarai da rashin jin layukan mu a kunne sun dauka wani abun kuma ya faru damu don shi a yanzu hankalin shi baya kwanci. Muna kalau na bashi amsa tare da tambayan shi iyalan shi dasu Faiza ya amsa a gundure da alaman akwai abinda yake cin zuciyan shi a lokacin. Yake tambayana wanan din ya kara dawowa ban san wa yake magana a kaiba yasa na tambaye shi yace wanan dai da umma tace yaron baffah marigayine shi daya bullo yanzu a kan case din ku. Banda time din wanan a yanzu don ban san meya kawoshi gare mu ba a yanzu din don haka bai a gabana na bashi amsa. Cikin mamaki yace dani sister kin san ko waye wanan mutumin a yanzu kuwa duk da mahaifin kune ya dagashi a baya har ya zama haka a yanzu . To shidin shine mai ma,adanai fiya da lissafin a cikin kan nan shine Mukhatar usman marwa da kike ji nima cikin mamaki din nace shine wanan din yace kwarai kuwa mahaifin kune ya dagashi har ya zama haka a yanzu din. Ashine dalilin shi na son shiga zancen ku a yanzu din a iya binckena a kanshi na gano bada wata manufa yazo gareku yanzu ba. Illa son da yake ya rama alherin mahaifin ku a gareku yanzu din sai dai ya dauki zancen kashin baffa da akayi da zafi don haka yake son a gano kaomai daga wanda ya hada plan cewa a kashe shidin yake son sani yanzu. Sai naji yayi shiru na sake fadin hello yace ina jinki sai dai ni jikina na bani cewa daddy a wanan katon ba zai iya tsalake wanan sharian ba shima idan ya tsalake na kaduna. Brother ban gane may kake nufi ba yanzu yace eh wanan karon kinsan tunda case din yakai su Abuja shariace za ayi sosai ba irin na kaduna ba. Wanda a karshe zai iya shafan kowa gaba daya nasan zasu durkushe ba zasu rage dako allura ba a hannun su. Wait a minutes nifa zan kirashi in fada mai wanan abin ya isa haka a yanzu sunan family din mune zaici gaba da baci ko yaushe a karshe kuda ke tasowa daga baya mutane zasu zo basu yarda da kuba ma. Kai ya gyada min yace masha Allah da kike da wanan fahintan haka kike da tunane irin na maza kike da tausayi da jin kai irin na mahaifin ki. Duk wanda ya kashe wani zaisu hadu a gaban Allah wata rana don shima bazai zauna gadin duniya ba ai dole yaje inda ya tura dan uwan shi. Yau dukiyan da sukai haka don kanshi idan an nema babu ko rabin shi a hannun wasun su don ba dukiyan Allah da Annabi bane don haka Allah ba zai barshi a hannun su ba . Da ace na tsaya na saurari wanan mutumin da na karbi lambashi a lokacin nasan zai mun amfani a yanzu zan kirashi in fada mai abar zancen haka ya bar duk mai hannu a ciki da Allah. Saidai ko umma ina jin bata karbi layin shi ba har ya tafi ranan au yazo wurin ku ke nan ma ashe nace yazo ranan da dare na dawo na sameshi a gidan mu tare da umma. Indan hakane zan tsanata binciken nomban shi ko zamu samu zan turo maki ki gwada yi mashi magana aji ko zai yarda ya janye zancen a yanzu. Duk da ya kamata ace na dauka don mahaifin modibbo yana cikin zancen ya kara ban wanan shawaran sai sam ban dauki hakan a zuciyana ba. Illa kawai yadda naga iyalan su suna cikin wani hali a lokacin yasa wani imani da tausayin hakan nasu ya kama zuciyana don nasan zafin irin hakan tun ina karamata. Kawai nasan wanda ya mutu ya mutu ne wanan sharian tsakanin su da Abban mune gobe kiyama don ko ance su dawo da wanan dukiyan a yanzu ba samun shi za ayi duka a hannun su ba. Haka dai mukayi sallama da ya Abubakar din da yake faman ban hakkuri kamar kullun yana kara tausan zuciyana kan abinda akai muna din. Mun gama na kashe wayana saidai maimakon in kwanta in huta sai barcin ya gagareni na fada tunanen duniya kuma. Wata zuciya tana izani kan me zance abar zancen a yanzu bayan su da farko basu tausaya muna ba sunyi son ranau sun rabamu da mahaifin mu. Su suna tare da nasu a cikin jin dadin rayuwa wanda mu sam bamu samu hakan ba don bamu san dadin mahaifi ba a yanzu. Iya abinda Allah ya debowa Abban mu ke nan a lokacin wata zuciya nawa ya fada min don mutum bai wuce lokacin shi ai. Washegari na fadawa umma kaf yadda mukayi da ya Abubakar din tayi dan shiru kafin tace yana da wuya yanzu mukhatar ya janye wanan zancen yadda ya dauke shi da zafi haka. Saidai a gwada yi mai maganan amma abune mai wuya yanzu ya yarda don irin amanan dake tsakanin shi da mahaifin ku a baya don marigayin ya daukeshi tankar wani dan uwa da suka fito ciki daya dashine. Amma mu munfi kusa da Abba din a yanzu hukuncin Allah muke so a kansu bana mutum ba tun farko ma da ansan wanan abu zai shafi har inda ba a zata ba da anbar zancen dukiya iyaka su dai san muna raye a duniya bamu mutu ba. Yanzu ko gashi Ana dara ga dare yayi don shi ma modibbo dayasan da hannun mahaifin shi cikin case din nan da bai yarda tun farko ya tazzara zancen haka ba ko don rufin asirin mahaifin shi din. Umma kike ganin bai sani ba yayi hakan yasan komai shidai mutum ne mai tsayawa yayi aikin shi da gaskiya kawai don ko yanzu bawai ya damu da abinda zai faru kan mahaifin nasa bane ai tunda yayi ba daidai ba ai kinji abinda ya fada ranan kan daddy. Yace yana ganin daddy yasan komai shine dalilin da baison a daga zancen nan a yanzu to kowa keda hannu a cikin case din nan dolene ya fuskanci hukunci daidai abinda yayi don haka a bari ayi sharian daya dace. Har na shirya na fita zuwa wurin aiki muna zancen da umma nan muka barta gida ita kadai kowa ya fita zuwa nasa tsabgan. Saidai ina isa zan shiga office dina idona yayi arba da oga sha,aban tsaye suna magana su ukku haka yasa nagane ashe yana kasan ke nan. Office dina na shiga direct ganin hankalin su ya dauku ga maganan da sukeyi a lokacin na shiga na zauna na fara aikin daya dace a lokacin Banfi minti biyar da zama ba oga Jimo ya shigo office din da wasu takardu yana min bayani akansu wanda ya kasa gano shigewan kudin. Bayani komai yadda yake har zuwa karuwan da aka samu akan yadda abin ya gudana nayi mai sai gashi yana washe bakin shi don jin dadin hakan. Don dama ya rikece shi a zaton shi kudi ya shige wani hanya da bai fahinta ba sai gashi na walwale mashi komai a saukake. Ya juya zai fita a lokacin oga sha,aban ya shigo office din idanuwan shi tarr a kaina har ya karaso inda muke nan oga jimoh ya fara rawan jiki don ganin shi. Mikewa nayi na gaidashi da zuwa ya amsa min tare da jan kujera ya samu wuri yakai zaune a cikin office din nawa. Fita jimo din yayi da sauri daga office din ya barmu mu biyu a lokacin shiru nayi bayan na koma na zauna ina dan kallon fuskan laptop dina. Sai jikina ya bani cewa kallona yakeyi a lokacin haka kawai naji in dago kai don jin shirun wurin yayi yawa a lokacin. Ina dago kai zargina ya zama gaskiya don ni din yake kallo a lokacin da sauri nayi kasa da idona cikin jin nauyin shi don idon daya tsura min din. Muryan shi naji a lokaci guda saida gabana ya fadi yana fadin idan ba mutum ya kira layin ki ba Sahiba ke baki taba kiran mutum kiji lafiyan shi. Abinda ya fito bakina lokaci daya da dago kaina shine iam sorry sir na fada cikin wani irin murya mai rauni a lokacin. Sorry for what ya tambayeni ya tsureni da idanuwan shi nima nayi kasa da kaina don bazan juri irin kallon da yake min ba a lokaci. Mikewa naga yayi ba tare da yai magana ba ya juya zai fita a office din saida yakai kofa ya juyo ya dan kalleni nima kallon nasa nakeyi lokacin. Ya fara fadin i will call you letter don ina son muyi magana dake mai muhinmanci sosai kafin na tafi yanzu naga akwai aiki a gaban ki yana gama fadin hakan ya juya ya fice daga office din. Tun bayan fitan shi wanan wunin aikin ma dai tunane yaso ya rinjayeni lokacin don ina tunanen me yake son muyi magana akai dashi kuma ? Shin a kan aikine ko akan sharian mu zaiso yasan wani abu kai ko kuma wani zance ne na daban ya taso kuma ? Sai dai kuma lokaci guda na share komai na shiga yin harkan gabana a lokacin don tunanen ba zai fitar dani ba a wanan lokacin. Kamar kullun lokacin tashin mu wurin aikin yayi don haka kowa yana rahaman zuwa gida na hada dan abinda na shigo dashi office na fito don zuwa gida. Sama sama nake amsa gaisuwan da ake jefo min ina sauri in fita don ina son in watsa ruwa a jikina don yadda nake jin jikin nawa a lokacin yana son yi min nauyi. A kofan fita muka kara hadewa dashi cikin tawaga saidai wanan karon akwai bakin fuska da ban
Chapter 262 · 0% Book details