Sashe 112
Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
shiga. Rana ya danyi don haka ban samu mota daga cikin unguwa ba sai nayi shawaran takawa da kafa nabi hanya jiki ba kwari don nasan zuwan banza kawai zanyi. Wata Jeep ce fara lafiyayya mai kyau ta wuce ni a hanya duk da basarwa irin nawa saida na yaba da kyau motar na dan bita da kallon basarwa . A kofan shagon na samu motan tsaye da alama maishi shagon yazo sayayya ke nan na dan kara kallon motar ina addu,a raina ina fadin Allah ka bamu wanda yafi wanan mai ita kuma Allah ka kara mar arziki. Dakata nan akace min na dago kai manajan mune tsaye a kofan ya fadi haka dama nasan hakan zai faru tun kan nazo din. Na dago kai tare da fadin sorry sir ban sona kai time din nan ba kayi hakkuri ka barni in shiga don Allah inyi wanan aikin for d sake of my brother . I want to paid his school fees tomorrow na dan hanna hannu wuri daya ina rokon shi yace dani. I beg de go before i call d security for u. U wan pai ur broda school fees, why u no come in time, u tink we de stay here for play or what ? De go jere , u tink say we be yeye here ? Banyi zuciya ba na dan tsaya na kalleshi da idona da suka ciko da dan hawaye don takaicin irin cin fuskan da yake kokarin yi min a wurin. Na dan fara ja da baya baya ina rayawa a raina gaskiya yau idan na bar wurin nan shine karshen zuwana wanan shagon na raya a zuciyana don na filanin yazo a makogorona lokaci guda (zuciya). Wani kallo nayi mai kafin in juya ina kokarin fara tafiya naji wayan shi yayi kara ya dauka yana yes sir ok sir sory sir. U girl ya fada da dan karfi tare da dan takowa har haraban wajen yana kwala min kira duk da nasan dani yake hakan baisa na tsaya ba ko in juyo. I am talking to u ya kara fada da karfi yana shan gabana na dago jajayen idona na sauke a kanshi cikin mamaki yake kallona yace. I dey talk to u , u no look ur back , wen u de warker , oya go inter, u be luck today ya fada . Da ace ni wata maishice ba zan kalli wanan shagon ba a yau koshi shigan da nayi don in cikawa Amar burin shine don tun ranan thursday yana gida zaune bai fita school ba gashi zasu fara exam. Ban ko tsaya gaisuwa ba na kwabe abayan dana sako a sama nakai inda muke ajewa tare da jakkana na nufi wurin aikina sai ga mai raba aikin yazo yace na koma wurin da ake kirga kudi na zauna saka ido shine aikina ranan a kusa da wani office din su da suke meeting manyan dake kula da wurin. Aikine ko a wurin sosai kasancewar wurin babban shagon kaya mutane tun dai yan kasan waje da masu kudi da manyan ma,aikata sai shagon yasamu karbuwa a wurin su . Ban saba da aikin ba duk da ba wani abu bane mai wahala amma yau sai najini daban da sauran ranakun aikin danake masu. Sam ban san akwai mutane a kusa damu suna meeting ba sai lokacin dana fara dan jin hayaniya na tashi a wurin a daidai lokacin kuma kaina ya fara sara min abinda ya dan dade bai mun ba . Har yakai an kai ga kiran wanda muke aiki dashi ya tashi saini na zauna wurin ina karban kudin abinda aka saya din kafin ya dawo . Hayaniyane sosai wa karedw wirin wanda kuma ni kadai ne ke jin hakan don wace muke tare tana saka kaya a leda bata ji komai ba a lokacin. Table din gabana na dan buga na mike sai wanan dakin na murna jin an shigo yasa duk suka dan juyo suna kallona a lokacin don ba wanda ya isa ya shiga wanan wirin. Kudine suka bata har miliyan hamsi da wasu abu akai ya kawo wanan muhawaran a tsakanin su, ina shiga sai kallona sukeyi suna mamakin abinda ya kawoni cikin su karamar ma,aikaciya dani haka. Don ban kai mataki na biyu ba a cikin ma,aikatan wurin sai kuma gani na shigo masu suna tsakiyan da tataunawa akan matsalan dasu manyan wurin kawai ya shafa a lokaci. Good day sir na fada kafin in juya ina fadin d money u are talking now, is with mrs Olanike nd mr Andrus house . Kaika sata ka bata ajiya a gidan ta on 27 karfe sha biyu na dare idan ba a dauki wani mataki ba sai ta fito dashi ku raba kaida ita ko karya na fada ? Ina fadi ina nuna Andy din dake zaune lafin na sake kallon su ina fadin tell him d man he is lookin for who battery him yesterday, is now in idi,eroko try to run away to oversea that,s mr Akani. Da sauri ya dago kai ya kalleni ina fadin haka ban tsaya jiran komai ba na juya na sakai na fita daga dakin taron duk suka bini da idanuwan su lokaci daya mamakin ya hana kowan su magana . Me yarinyar nan take magana a kai ne mai wurin ya kira waya yana tambaya sai wani Abdulhamid yake kara masa bayani abinda na fada. Sam ba wanda yayi zaton jin hakan don har ana batun kiran security daga waje su wuce da wayanda ake zargin sune da alhakin hakan lokacin. Gaskiya ta fada ko kuwa daku da ita duk mu mika ku wurin yan sanda yanzu kuyi bayani a can manager ya fada a fusace. Namijin yace shi sam bai san wanan maganan ba, bai ma san inda wanan zance ya fito haka ba ai. It look like wanan yarinyar tana da wani baiwa akan hakan don haka kawai ba a kirata ba a nan ta shigo ta fadi abinda ya faru haka . Har kuma tayi magana a kan mr Akani da suke rikicin kudi da oga a daren jiya sai gashi ta fada yanzu a nan yaya akayi duk ta san wanan din yanzu ? Dole maganan ta abin dubawa ne don ya akayi har ta san da zancen Akani da jiyan nan sukayi shi da dare oga ya kirani yana fada min abinda ya faru. Ya zama dole mu mikaku duka wurin hukuma idan kunje can kuyi bayanin abinda ke faruwa in yaso ta kara yi masu bayani a can ya fada yana kokarin daga wayan shi. Jin hakan da mrs Olanike tayi yasa da sauri tace zan fadi gaskiya bana son abu daya dangata da station ko wani abin juju ko kadan a rayuwana. Me, i no wan wahala woo, come collet d money wan you bring to me dat day abi, d same day, dat dis gurl talk about it? No be dat day, u bring d money they talking about it now? i no wan wahala wooo atoh! I ask u whare u getterm ? u say make i no ask u now. Ta mike tsaye tana fadin ita fa bata ciki shiri ajiya kawai ya kawo mata ta ajiye mai na dan wani lokaci kuma ta aje mai su. Manyan sukai kasa da kai na dan lokaci duk basuyi zaton wanan mailaifin shiyayi rub da ciki da wanan kudin daya shige ba haka masu yawa. Sun fi kai zargin su gun kananan ma aikatan su dake tura masu kudi sune suka kwashe kudin haka gashi kuma wanda ake zargin yana da alaka da mai wajen ke nan su din yan uwa ne najini yai masa wanan aikin. Ina barin dakin jakkana da abayana na dauka da zuman fita daga wurin don gaba daya hankalina baya a jikina a lokacin. Karo nayi da mutum haka baisa na tsaya ba don in bashi hakkuri yana tsaye ya zura hannayen shi a cikin aljihun wandon dake jikin shi duka biyu. Ido na dago kawai na kalleshi na ci gaba da tafiyana banyi magana dashi ba na nufi hkudin fita daga wajen ga baki daya naji an rikoni. Kaina kai nake fadi ga maishi ina fadin mu head wooo my wooo har nakai kasa durkushe a wurin rike da kaina dake min ciwo sosai. Ayoyin Allah daga cikin Al,Qur,an mai girma ya fara ja min lokaci hankalin mutane ya fara dawowa gare mu hakan yasa ya dan kara jana zuwa bayan wani kanta. Har dai ya kai karshe ya kira sunana na amsa mai yace masha Allah dan juyawa yayi yajana fadin dis is notin serious woo . We usualy have dis problem in our people so don't take is serious matter ya kuma juyo kaina yana fadin go home nd have a rest. Tafiya na fara yi kafin daga inda yake yayi mai magana sai Abdulhamid din ya dakatar dani da in jirashi yazo bayan na jirashi ne sai gashi da mota yazo ya kaini har gida. Umma ya sama yayi mata bayanin abinda ya faru dani tayi maigodiya tare da dan bayani nan yayi mata alkwarin akwai wurin wani alpha da zai kaini yana bada maganin irin matsalan nan tayi mai godiya kafin ta shiga gida ta sameni kwance har barci ya daukeni a lokacin. Ban falka ba sai dare na dan samu sauki naci abinci bisa tursasawan umma din na kuma watsa ruwa a jikina na sake kwantawa. Kwana biyu ina kwance ban fita ko ina abin duniya yayiwa umma yawa ana haka ranan da abin ya faru da kwana hudu sai ga yan shagon mu maza mutum ukku sun sallamawa umma tafito suka gaisa . Suke fadin sunzone kan abinda yafaru dani a dalilin su don haka mai shagon yace su kawo min alherin don jin dadin da yayi na fitowan kudin shi daya gane wasu kudin shima da suka fi wanan yawa a hannun Akani dana fada mai inda yake ya bishi. Manaja yasa hannu ya ciro key daga Aljihun shi tare da envelop ya aje a gaban ta yana fadin wanan key din motace sai kuma kudin mai a cikin wanan takardan