← Book details Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 199 OF 337

Sashe 199

Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ina tuki ina sharan hawaywn daya cika min idona da bakomai yasani yun shi ba a lokacin sai ganin yadda taron yan uwa basu san mu ba alhalin muna jinin su. Wanan wani irin zaluncine haka dan uwa uba daya ku rabashi da duniya ku wofintar da iyalan daya bari a cikin duniya cikin rashin damuwa ku kuna zaune daz naku cikin jindadi da kulawa duniya ina zaki damune haka ? Muniya datayi shiru a gefena take fadin kiyi hakkuri nasan abinda ya sakaki kuka ganin yan uwa haka a wuri daya dole kaji ranka ya sosu sosai . To amma kuna da yan uwa haka ashe Sahiba meyasa baku ziyaran su alhalin naga suna son ku sosai ji yadda yarinyar nan data ganki ta rude gaba daya wallahi don jin dadin ganin ki. Amma daga ke har umma har Ammar kamar baku damu dasu ba why kuke nuna kamar baku da gata hakane sai wanan dan uwan naku kadai naga yana zuwa wurin ku shima baku ke zuwa ba ? Murmushin dole na kakaro a fuskana lokacin na kara kai hannuna ina share hawayen dake fuskana bandaiyi magana ba itama nisawa naji tayi kawai lokacin. Haka muka isa gida umma dake zaune tare da yaran suna zaman jiran dawowan mu ta fito tana muna sannu da zuwa na amsa a cikin rai kawai na shige ciki zuwa dakina. Gado na fada na sake wani kuka mai ban tausayi rashin Abban mune ya dawo min sabo a zuciya sai nake ganin gaba daya ahalin namu basu kaunan mu ne wanda ya mutu ya mutu ke nan dai. Nakai wani lokaci kwance a wurin kafin naji muryan maryam tana fadin tare da dan bubuga min jiki in tashi in tashi kawai take fadi ganin ban tashiba ta hawo gadon ta kwanta a jikina. Sai lokacin ne na sauke wani irun ajiyan zuciya naji kamar yarinyar ta lalasheni a lokacin ina jin wani natsuwa na sauka min a zuciyana lokaci guda. Nakai wani lokaci a hakan ban motsa ba kuma ba barci nayi ba a lokacin jin nauyin yarinyae yai min yawa a jikina yasa na dan juyo naga halin da take ciki ashe barci yarinyar tayi lokacib a jikina na gyara mata kwanciya nima na juya rigingine ina kallon darking din dakin. Sai can na tuna banga umma ta biyoni daki ba hakan ya sana mike da sauri nafito daga dakin na nufi dakin umma ganin bata falo a lokacin yasa na nufi dakin nata. Zaune take a inda ta idar da sallah a cikin wani yanayi na ban tausayi jin na shigo dakin ne yasa ta dago idanunta daya sha kuka ta sauke a kaina lokacin. Zaune nakai bakin gado kafin ince komai da ita ta dago tana tambaya maryam na wurin kine na gyada kai tare da fadin tayi barci. Nan take tana damuna tun fitan ku shine na turata wuri ki ta fada a kasalance nasan zaki take son sha zakin nan kuwa ba zai basu lafiya ba idan ya tashi tambayan su. Sun saba da shan sa ne tun gida tunda kikaga shi kadaine a bincin su tace bata ko koyawa diyan ta alheri ba ai duk uwar da tasan kanta zata nisanta danta da wanan kayan kwalaman na turawa saidai uwayen yanzu suna ganin kamar hakan wayewa ne amma da illan da yakewa yaro a jiki sosai kuwa. Ai kinga yarbawa da sauran kabilu basu yarda sun yar da gargajiya ba kodama sugar zasu sha saidai mai kololo kuma bai wuce kwara biyu a wuni don sun san illan hakan ga jikin dan Adam abin ba manya kawai yake shafaba har da yara kanana a wanan zamanin. Shiru nayi ina nazarin abinda umma ke nufi kafin inji tana fadin ashe kun samu taro sosai a airin yan uwa da kukaje ? Na nisa tare da dago kai na dan kalleta nace eh umma gaskiya sun nuna muna jin dadin su sosai da ganin mu a wurin saidai mun barsu da mamakin mu sosai a zukatan su. Nan dai na fara bata labarin abinda ya faru a wirin damu har dawowan mu din tayi shiru tana tunane mai zurfi. Zaune suke a falon su sun tasa kayan a gaban su suna kallo a cikin mamaki kowa yayi shiru sai hauwace tace nifa wanan kafiran motar da kuma irin shiganta shine ya tsaya min a rai wallahi. Jiki don Allah da wani zancen banza ace maki mutum ya fito lagos don me zaki tsaya mamakin arzikin ta lokaci guda sai dai idan kinso. Shi dan lagos meye bai iya aikatawa don kawai ya tara kudi nikan banyi mamakin hakan ba tunda dai kinsa Sahiba kyakyawace ta karshe dama . Wai kina nufin ta kallo Nabila din bata karasa ba tace kwarai kuwa ke nifa ban wani mamaki ko maza sukaje neman kudi acan ai kinga yadda suke dawowa nan Amma ai barikin ta dai baisa ta canza ba yanzu ko tunda tarbiyan nan nata naga yana nan ji yadda taje gaban su mommy ta gaidasu a cikin taron nan ni shine ya burgeni da ita a wurin wallahi ko duk ko yadda ido yake a kanta ba. Sahiba ta koma ubanta sak a yanzu muryan mommy datayi tagumi ta fada cikin nisawa da nauyi kafin ta fadi hakan duk suka kallota. Wallahi yau ganin yarinyar nan ya daga min hankali sosai bani ba son duk wanda ke wurin nasan abinda ke zuciyar shi ke nan idan ya tuna. Muryan yayansune yayi sallama duk suka kalli kofan shigowa falon nasu lokacin guda ya shigo suna mashi sannu da zuwa. Saida yagaida mommy a cikin mutunci ya samu wuri ya zauna ya fara amsa gaisuwan kannen nasa a lokacin. Yana ce masu ya bukin ashe har an fara ke nan ko hauwa ta amsa mai da kai kafin tace tun jiya yaya muna ganin bukin yan gayu ai. Faiza ta fito daga dakin cikin murna take mai sannu da zuwa ta zauna a kusa dashi ta fara fadin yaya mu Sahiba fa tazo garin nan wallahi. Sahiba ya fada a cikin mamaki yace ina kika ganta tace cikin fara,a wallahi wai bukin ne ya kawo su tace amma bata sauka gidan nan ba kuma ta karasa fadi cikin bacin rai a fuskan ta. Ita dawa tazo da mama da Amar kanin ta ya tambaya yana boye razanan shi a fuskan shi lokacin. Kai ina kakai yara nan ka tayarwa mutane da hankali haka anya kana son ganin farin cikina kuwa yanzu modibbo ? Yara mommy wasu yaran ke nan ta watsa mai harara kafin tace ai sainace yaran ka zaka gane ko ? Ya dan shafo fuskan shi kadan zuwa kasa yace suna Abuja gidan abokin aikina na kaisu tunda ita bata damu dasu ba. Baka da hankali ina gani yanzu modibbo da har ka tsaya biyewa matarka mara tarbiya ka aikata hakan bayan kasan hakan zai jefamu a wani hali na tashin hankali. Kuyi hakkuri mommy nasan a lokacin idan na kawo maki sunan zakice ne a mayar dasu wurin ta a lokacin ni kuma ina son nuna mata ita ba kowa bace yasa na dauki matakin hakan. Yanzu kai wani irin yardane tsakanin ka da wanda kakaiwa yaran har ka yarda zai rikama yaran tsakani da Allah ku dinga yin tunane kafin aiwatar da abu wallahi. Abinda za aje a dawo ana da ansani a kansa bayan lokaci ya kure baida dadi duk da dai itama din Nazifan halinta sai Allah ne amma wanan matakin baiyi ba wallahi ta karasa cikin bacin rai sosai ta mike ta shige dakin ta. Suka bita da kallo kafin hauwa tace dashi kayi hakkuri yaya har daddy saida suka samu matsala da mommy kan wanan zancen don shi daddy wai laifin mommy yake gani yanzu . Amma dai ita mommy ai bata kula mashi ba tunda neman abinda zai tunzurata ta cikin taron nan yanzu yakeyi . Wani kallo yayi wa yarinyar yai shiru bai kara cewa komai ba yashiga dogon tunane mai zurfi kafin ya furzo da iska daga bakin shi yana fadin. Naso a ginawa mommy gida ta bar su nan amma kuma hakan ba abinda zai yuyu bane don shi kanshi daddy ba zai yarda da hakan ba sam. Kaima yayan mu kasan ba zai yarda da hakan ba ai don yasan duniya zata zageshi kawai dai mommy tayi hakkuri da sabon sauyin data samu a wurin shi yanzu don anty da kuke gani ba karamar shu,uma bace. Kai ku daina irin wanan zancen zargine da camfi irin na mutane sai mutum ya daukarwa kanshi zunubi a banza irin haka. Yaya kai namiji ne baka ganewa wallahi amma muda muke zaune a cikin gida mun san abinda ke gudana ai Nabila ta fada cikin bacin rai da damu kan irin cusgunawan da mahaifiyar nasu ke gani yanzu a gidan. Bai kara magana a kan zancen ba sai tambayan daya jefowa Faiza data zauna a gefen shi itama cikin damuwa don irin rayuwan cin fuskan da mahaifiyar tasu take gani a gidan yanzu abin yana damun kowan su a rai. Yace Sahiba din tace zata kara dawowa nan ne ko sun tafi ke nan tace zata gobe da yardan Allah don bamu ko zauna da ita ba a gidan gwaggo hari inda akai event din muka hadu da ita tazo da Alheri sosai yaya taba kowa mamami bakaga irin kayan rabo da takawo a wurin bane yaya . Na fada maki sahiba ta canza a yanzu don babba ma,aikaciyace Sha,aban comoany ga baki daya inda yake da reshe cikin kasan nan itace mai kula da shige da ficen komai a kasa. Sahiba din kwarai kuwa ita din ba karamar mace bace a yanzu gaskiya duk abinda kukaga tayi kada kuyi mamakin hakan tanada oppotuniy din yin hakan gaskiya don ta wuce sanin ku a yanzu. Kinji ina fada maki kina cewa wai maza takebi kila in bashi ba ina zata samu kudi irin haka take wanan abin yanzu kinji ke nan da kunnuwan ki hauwa ta fadawa Nabila din. Kallon mamaki yayi mata kafin yace ke yanzu ashe ba mai tsayawa kiyi fada bane idan wani ya fadi haka akan yar uwarki ashe ? Kai yaya wai idan an tashi
Chapter 199 · 0% Book details