Sashe 196
Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ina bara adduan ku da bakunan ku masu albarka ga wanda Allah yaba ikon tunawa yayi min nagode. Muniya naba kudi ta sayowa yaran abin bukata daga tufafi permppers da alawa da biscuit har magani don yaro baka rabashi da ciwo. Kwana biyu kawai nasan mun samu matsala da yaran bayan shi mun zauna lafiya dasu babu wani matsala gaskiya ganin haka sai na daina damuwa akan yaran Don muma yayi muna shine silar mayar damu cikkakun mutane a yanzu har na tsaya nayi karatu da taimakon Allah ga har Amar shima yana karatun don da karatun lagos natsaya nayi sai yanzune zan shiga jami,a a lokacin. Amma gani a mataayin dako makiyina baiyi tunanen hakan ba gareni koda a mafalkine cikin kuduran ubangiji . Wanan yasa nakeji da diyan ya Abubakar din na kawar da tsanan uwarsu a zuciyana tunda basu sukai min laifi ba uwarsune da kakan su. Ina jin yaran har cikin zuciyana sosai dan zaman mu dasu dama kuma in baki manta ba haka nake da yarani har yaran Abdul sun saba idan na dawo su tareni bazan shiga gida ba sai na raba masu dan abinda na tsaya hanya na sawo masu ranan da ban sayo ba kuma kudine zan basu ince suje school dashi da safe. Yauma shiryawa nayi zamu fita kasancewan weekend ne ranan zamu fita sayayya don washe gari sunday ne yawancin shaguna basu budewa a ranan. Nida muniyace a gaba ta dauki yar ya Abubakar karaman a jikinta babban kuma rabin jikinta yana akan jikina ina tuka motar . Wani babban shagon sayar da kaya na tsaya muniya ta kalloni tana mamaki na sake mata murmushi kafin ince zan dan duba abune na juya wurin samarin dake baya su hudu ina fadin banda garaje sun san nan ba wasa yanzu a yankewa mutum hannuwa idan ya taba masu kaya. Daga cikin motanshi ya kura muna ido sosai har muka fito muka shiga shagon shima fitowa yayi yabi bayan mu zuwa cikin shagon. Yar banci mukeyi a lokacin yana tsaye yana mamakin ina na samu diya saidai abinda ya tsayar mai da mamakin nasa shine gabnin yarinya tana son zuwa wurin . Ajiyan zuciya ya sauke ganin uwar yarinyar ta karbi abinta daga hannuna sunyi gaba sai lokacin ya iya motsawa daga inda yake tsaye din. Kayan yaran nake zabe mata kaina a duke naga hannu ya tabo wani daga bayana yana fadin ki zabi wanan yana da kyau sosai. Ya sallam na fada a raina ina lumshe idanuna duk da ban juyo ba nasan muryan dake min magana a lokacin don muryan Almustaphane a bayana yake maganan. Gane hakan baisa na juyo na fuskance shiba naci gaba da abinda nakeyi wurin dubawa karamin yaron muniya kayan sakawan shi. Sahiba dake nake don nasan kin sheda ko waye a bayan ki ke nan wanan kin juyowan naki da kikayi a yanzu ya nuna min hakan. Kwarai na shedaka kokai waye saidai bai zama dole gareni ba in nuna nasanka a ko ina na ganka kona ji muryan ka din. Murmushi mai sauti naji ya sake tare da gyara tsayuwar shi da kyau yana fadin har yanzu zancen haka na cikin zuciyar ki ashe ? Magana daya zanyi da mutum na rikeshi har mutuwa ta bana mance Alheri hakama bana mance gargadin ko wani zancen danayi da wani. Ina munyi wanan zancen dake a baya na dauka komai ya wuce a yanzu ai na dago kai na watsa mashi wani irin kallo da dukkan idona. Murmushi ya sake yana saka hannayen shi cikim aljihun wanson shi dukka biyu yace ba wanan ba me kika zoyi a kaduna yanzu ? Kwanaki na ganki a by pass sai na dauka bake bace don ban taba zaton cewa kedin bace a kaduna a wanan lokaci daga baya kuma sai banyi mamakin hakan ba don tunawan da nayi cewa kedin dama kin taba zama a nan din. Me ya kawoki nan ina kuma mama da Ammar suke ban rufe baki ba saiga yaran sun dawo hannayen su dauke da alawan da nace kowa ya zabo a lokacin. Amar yana ganin shi ya dan so zuwa wurin shi sai kuma ya tsaya yana kallona a cikin dan shakkan hakan a fili. Zo mana abokina ya fada yana kallon Amar din da murmushi a fuskan shi ya sake mikawa amar din hannu nayi mai alaman ya tafi inda yaken. Da sauri ya karasa wurin shi banda wani dar din komai akan Amar din don mun riga da mun koyar dashi abinda duk wani zai tabayeshi game da zuwan mu din. Gaba daya yaran suka bishi a baya yake tambayan shi yaushe kukazo garin nan yace this week muka zo muna zuwa ganin likitane mu koma lagos. Har a ranshi ya gamsu da hakan da yaron yace don ba wani shaku a fuskan yaron na fadin hakan ya sake tambayan shi wani unguwa kuke yace a hotel a can muka hadu da wa yan nan suma sunzo bukine sukace. Daukan yaran yayi yaci gaba da yi masu sayyayya har na fitan arziki mu dai muna jiran su a madakata muka fito tare dashi. A bakin motan mu ya tsaya nayi dabaran ba muniya makulin motar tun kan mu fito akan itace zata ja motar kada ya gane hakan don tun wurin biyan kudun Amar yai min signal da cewa ya fadamai hakan. Duk sun shiga motar sun zauna saini naji yyace gaskiya sahiba baki da kirki kin shigo garin nan keda Amar amma baki nemi yan gida sun san kina nan ba. Ba wani abu nazo nan nema wurin wani ba asibiti mukazo kawai kuma jirgin safe zamubi gobe din wanan makwabciyar tamuce ta matsa mu shigo ko zamu dan saki jiki dama Amar ya fada min yace. Ka gaida gwaggo na fada ina kokarin shiga motar dana bude tako kije da kanki idan kin damu da ita ya fada. Nashige mota bance dashi komai ba a lokacin mukaja muka tafi muka dauki wani hanya don batar mai da sawu saida naga bai biyo mu bane na sauke ajiyan zuciya. Mun koma gida nake ba umma bayanin haduwan mu dashi lokacin muka bude abinda ya sayo ma yaran muna mamakin hakan. Ammar kuma ya bamu bayanin duk yadda sukayi dashi lokacin dayaja su yana masu sayayya. Wai yar nan kinyi dubara tun farko kamar kin san hakan zai faru din nace na sani tunda munzo garin su man ai dole mu hadu da wanin su gashi ko duk mun hadu dasu din. Kayan da nayi oda lagos don halattan bukin baby suka iso gareni a daidai lokacin da kuma nake wasi wasin zuwa bukin yanzu don ni kadai nasan shirin da nakeyi a bangarena yanzu boyo dai ya isa hakanan kuma garemu na fada a raina. Shiri nayi sosai da ba tare da kowa yasan da hakan ba sai wa yanda na shirya hakan dasu da zamu tafi tare. Shiru dakin yayi lokaci guda ba wanda ya iya magana a cikin su bayan mahaifiyar nasu tagama wayan da hjy Addah. Tasiu ne ya kawar da shirun falon yana fadin ba shike nan ba tunda wurin kakansu suke yanzu meye na damuwa kuma ? Kai dan Allah rufa min baki in yaran na wurin Addah ita fa me yake nufi da ita ko a nan kake son ta zauna muna a samu abun fada kan mu. Ban fita wani ba yanzun kuma wani na shirin tunkara duk a kan yaya wanan abin dame yai kamane wai ? Ni Abba ma nakejiwa wallahi don idan yasan da zacen nan komawan ki yanzu sai Allah gidan nan. Wa zai fadawa Abba ina gidan nan ta fada tana dauko wayanta tana neman layin mijin nata lokaci guda. Ai dole Alh ya san kina gidan nan ke kin dauka zancen wasane wai kinyi wauta babba da kibar yaran nan a gidanshi koda baizo donke ba dole yazo don yayan shi ai. Dolene mana Nura ya fada yana mikewa tsaye yace ita anty ma duk mata suna son dangin mijin su amma ke kullun kina cikin fada da naki ko banza ai gwaggo Addah kanwar mahaifin mune kuma muna jin dadin ta duk wanda yaje daga gidan nan. Ya fada yana gunguni ya fita daga dakin rai bace uwar nasu ta kwala mashi kira don kada ya fita ya fadawa wani. Da kyat yaron ya dawo dakin ya zauna yana cicika yana batsewa har lokacin yana jin zafin yar uwan nasu sosai a zuciyar shi. Ya kara fadin ke baki tausayin mamace ki duba dan iskan nan idan baida hankaline ai suna da yan mata a part din meyasa baije can ba sai nan don suna jin haushin mu mana su barna muna suna ga banza. Kan uwar na suke abin duniya ya dameta lokaci guda kafin tayi magana uwargidan su tayi sallama ta shigo da sunan gaida Aina,u da jiki. Amma tana ganin Nazifa sai kuma ta buge da fadin kina nan ne ashe ta juya ta kalli mai aikin nata tana fadin ina yaran suke ? Suna gida tare da baban su ta fada Allah sarki sai basu biyo kuba kuma ashe sun saba da uban nasune har haka. Aina ya karfin jikin naki tace naji sauki a wani irin yanayi na nuna rashin jin dadi a lokacin. Ta juya tana fadin idan kun tafi a gaida muna su ta fice a cikin tsarguwa ganin yadda suke zaune zugun zugun a falon kamar an masu mutuwa. Dole dai yadda ba a son din hakan akayi don an nemi wayan Abubakar din ba, a samuba don baya shiga yana fadin a kashe wayan yake. Dole uwargidan nasu tafadawa halinda ake ciki ta samu mijin nasu da zancen bayan ta gama yiwa nazifan fada sosai na irin rashin jankalin da takeyi. Har tana fadin idan baki hankali ba sai iyayyen shi ko shi sun saka ya kara aure mace da zatazo ta mamaye mKi gida kina ji kin gani kuwa. Shi kuma Alh ya gama jin tana gida modibbo y kwashe yaran ya rufe gida ba a san inda yaje da yaran ba yanzu haka ko an kira wayan nasa baya shiga sam. Dago kan Alh din sai cewa yayi to shine me ke nifa sam