← Book details Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 206 OF 337

Sashe 206

Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

zaria a lokacin boko ya gama ratsashi ko sosai shi yasan abinda yakeyi sosai. Maganan shi sam baiyi wa wasun su dadi ba amma kuma manyan sun tsaya ga maganan shi hakan yasa Alh nuhu rufe kowa da fada har yana fadin shine dai babba a nasu zauren don haka ko anki anso dole abi anbinda ya fada don haka bai yarda da zancen wai mairo ta dawo da iyalin ta ba ai dama ba wanda ya koreta don kawai tana zargin kanta ai tagudu ta shiga duniya. Jin hakan matasan daga cikin su suka mike suna fadin maganan shi zancen banza ne shima ai ina ya taba jin haka idan diyan cikan kane zakace mu wofintar dasu a cikin duniya ne ? Ranan dai an fara kaiwa inda ba a son akai don dama matasan hudu sun dade suna jin zafin irin cin zarafin da yakeyi a cikin Family. Ranan kan gaskiya an tashi wanan taron ana kaiwa kaiwa abinda bai taba faru dashi ba ya fadi har wasu tsageran kanansa suna mayar mashi da amsa bako manyansu ba a cikin su. Haka sukayi wanan satin a cikin rigima sai kus kus sukeyi a tsakanin ba wanda ya isa ya fito fili ya fadi don basu samu kan daddy da iyalan shi ba balle suji wani abu a wurin su suna fama da sallaman bakin su da sukazo buki lokacin. Safiyan litini kuma a wurin aiki tun safe bello yana get din ma, aikatan dake shigowa yana sane dasu idan zaka shiga sai kayi signed idan sunan ka na cikin wa yan da aka dakatar ya baka takardan dakatarwa ba bayanin komai sai idan kaje ka karantane zakaga abinda aka rubuta ma a ciki. Karfe tara saiga Oga Bala ya shigotun daga nisa yake mamakin ganin an rufe get din ma,aikatan yau haka ya karaso har get din zai hau maigadin da fada yaga bakon fuskane a ranan don bai sanshi bama kwata kwata a cikin ma,aikatan nasu. Malam ka fito ka duba can indan an yarda ka shiga sai a bude ma ka shiga mutumin ya fada cikin rashin ko inkula da abinda ya fada. Fitowa yayi daga motan yazo yana kokarin bude get din a cikin fada sai ga wasu majiya karfi sun mike mutum biyar dole yaja da baya yana fadin meye hakan wai ? Meke faruwane a cikin nan yau ne ni zaku hana shiga ciki ubanwa yasamu wanan aikin duk garin nan ? Yallabai barka da zuwa aka fada daga gefen shi Bello ya kuma shedashi wurin barka da kwana rankai dade bai tsaya amsawa bellon ba yake fadin kai me ke faruwane wirin nan har banzan mutanen can suna min barazana da shiga ciki. Rankaidade ba laifin su bane umurnin hakan aka bayar daga sama cewa duk wanda sunan shi bai fito a wanan takardan ba kada yashiga ma,aikatan . Me ake nufi da hakan ya tambayi bello din a wani irin yanayi na bacin rai rankai dade gadai takardan ka karanta zaifi kyau nake gani. Zuwan chairman ne ya hana su karasa zancen shima basu yarda ya shiga ciki ba don sunayen su bai fito a ciki ba. Kafin wani lokaci kofan wurin ya koma kamar kasuwa da jama,a wasu su shiga wasu kuma a dakatar dasu daga aikin. Manyan da abin ya shafa sunyi kiran layin duk wani wanda ya kamata ace sun kira a lokacin sai dai basu samu layukan su ba a lokacin. Alh Nuhu yana zaune a falon shi suna waya da kanin sa gyade akan matsalan daya shafesu suna zagin daddy har gyade din na fadin da yau lafiyan kalau ba abinda zai hanashi zuwa gidan Ali dcp yaci masa mutunci sosai wallahi. Yaron shine ya shigo yana fadin Abba wasu mutane suna maka sallama a waje harda yan sanda a tare dasu. Yan sanda ya tambayi yaron yace kwarai don da matan yan sandan me zasu shigo gidan sai gani na iso suka turo ni. Fada ya tashi yanayi akan me zasu zo min har gida idan ma wani abu aisai su kirani inzo in samesu ya fada a cikin gadara. Yana fita a fusace hango taron da yayi ne ya bashi mamaki lokaci guda yana isa suke fada mai sunzo tafiya dashine don anyi karan shi a sha,anban company. SHA,ABAN ya maimaita sunan a cikin mamaki sunan manager din na chairman ya kira yana fadin sune sukai karana kowa ? Alh idan kaje can zakaji yanzu mu wanan ba case din mu bane case yana hannun Oganin mune can wanan ai wullakancine da rainin wayau zasuce sunyi karan mutun haka. Alfarma daya sukai mai don kasamcewar shi babban mutum yasa suka kyaleshi ya shiga motarshi zuwa headquater din su inda ake neman shi a can. Saidai yana zuwa yaga ashw bashi kadai bane mutane da dama ne a wurin case din ya shafa yaso ya nuna masu halin shi amma basu bashi daman hakan ba don sun fada mai umurni suka samu daga sama. Muna zaune kiran ya Abubakar ya shigo yake tambaya muna nan gida na amsa mashi da eh ba a dauki wani lokaci ba mai tsawo sai gashi gidan namu. Yaran nasa na ganin sa suka shiga murna saidai ya mika hannu karamar ta lafe a jikin umma tana mashi dariya babban ma tazo ta kwanta min a jiki tana boye fuskan ta. Gaidashi mukayi kafin ya fara magana yana fadin umma nasan duk kinsan abinda ke faruwa a yanzu kan gabatar dasu da Sahiba tayi ta hanyar da kowa bai tsamanin ta haka zata fitowa kowa ba lokaci guda haka ta girgiza kowa na ahalin lokaci guda. Da wanda ya dace ya sani wanda bai dace ba duk sun sani a lokaci guda abin kamar an fasa kwaine a gari don kowa zancen da yakeyi ke nan a yanzu. Saidai a gaskiya umma ba zance hakan baiyi daidai ba ko yayi daidai duba ga sanin waye Uncle Nuhu a cikin garin nan dama kasa baki daya. Uncle dai basai na fada maku ba shu,umine na gaske wallahi naso ace ta bari sai zuwa lokacin da muka shirya tunkaransa mu tunkareshi alokacin da muke da shirin mu. Amma yanzu aikin gama ya gama ko don yasan kuna raye an fada mashi kuma hankalin su a yanzu duk a tashe yake don wanan abin ya jawo rabuwan hankali da baraka a tsakaninsu sun kashi gida biyu. Nan dai yaiwa umma data sansu bayan duk abubuwan dake gudana a tsakanin yan,uwa na tashin hankali kan zancen cewa mu din diyan marigayi ne dan uwansu. Ikon Allah wanan hakikancewar haka umma ta fada a cikin mamaki yace eh saboda sun san basu shuka gaskiya bane ya jawo hakan ba komai ba. Idan ba wani abinku a hannun su ai duk wanan tayar da jijiyoyin wuyan ba za ayi shi ba ayanzu asalima ba zasu damu daku ba ai sam don kun baiyana din yanzu. Dago yarinyar dake jikina a kwance nayi don gyara zama da nake son yi inyi magana a lokacin sai naga yarinyar ashe tayi barci ne a hakan data lafe a jikina wai. Abinda ya jawo hankalin shi garemu ke nan yake fadawa umma mommy ta dameni kan indawo da yaran nan hakana don ma bukin nan ne ta daga min kafa da zancen nace dasu Abuja nakaisu gidan abokina. Uwar tasu ta dawo ke nan umma ta tambaya yace ta dawo don mommy kawai na dawo da ita saboda naga mommy tana shakun mahaifinta sosai a rayuwan tane. Dolene aji shakan wanan shu,imin mara imani don kawar da rayuwan kiyashi yafi girma dana mutum a wurin shi sam bashi da imani ko kadan. Amma umma banda ya Abubakar na fada ina jawo yar ina gyara mata kwanciya a kujera wayan shi ya dauki kara ya ciro yana dubawa sunan Nazifa ya gani ya dauka cikin basarwa yana amsawa. Hankali tashe take fada mai wai yan sanda sunzo har gida sun tafi da Abban su yace akan wani dalili tace yasir yace wai akan wani company ne na SHA,ABAN sukai karan su daddy din shine ake neman ka a yanzu gida. Daga inda yake zaune ya dago kai ya tsureni da idanun shi shanyayu masu kamada yana jin barci ko wani shauki yace kunyi karan wasune yau din nan yana mai kura min idon nashi har lokacin ? Kai kawai na iya gyada mai a lokacin don yadda yake kallona a cikin mamaki ba zan iya yunkurin fadan komai ba a lokacin.
Chapter 206 · 0% Book details